NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 88 of 98

da damar yi mata kiss kuma yasa mata zobe, Wata bahaguwar ajiyar zuciya ya ƙara yi, hannunsa dafe da saitin zuciarsa. tunda yake bai taɓa shiga tashin hankali irin haka ba, sai yanzu ne Yake mamaki ƙwarai matuƙa da yanda yake jin Sabina a ransa, me yasa tun farko ya kasa ɗaukan hakan a matsayin *SO* ?, mai yasa ya kasa barin yarinyar ta saba da shi ko da ace bada sanin yana sonta bane, shi kansa ya san babu kowa a zuciyar Sabina amma yanzu gashi farat ɗaya wani daban yazo ya shige zuciyarta, wani irin ƙullutun baƙin ciki ne ya tsaya masa a maƙogaro. da ƙarfi yasa hannu ya daki goshinsa, jin zuciyarsa yake na neman fitowa, ƙululun abinda daya tokare masa zuciya SO ne ko kuma KISHI? idan duka biyun suka haɗe suka tabbata ya zaiyi? dan ba zai taɓa iya furtawa yarinyar cewar yana sonta ba, kuma gashi ba zai iya jurar ganinta da wani ba. zuwana compound nayi kiciɓis da Umma, na rissina ina cewa,"Umma ina yini, ya sauƙin jiki? Allah ya ƙara lafiya". na haɗe maganta duka don na san ba lallai ta amsa min ba. ina kallo ta taɓe baki bayan ta kalleni, na duƙa ƙasa zan cire abu a takalmina naji tana cewa. "ahaka dai za'a lalace, anƙi ai aure sai aikin jera kafaɗu da manya saboda babu kunya, anje an ɗauko mutum da niyyar taimakonsa an ɓige da iskancin banza a bayan idon mutane, to bari Baban naki ya dawo zan zayyane masa komai saboda baza aci amanata da shi ba, tun wuri yasan irin matakin da zai ɗauka kamin kija mana abin magana". na ɗago na danƙara mata harara kamar idanuwana zasu zazzago nace,"A kaf duniya inda mai yimin mugun baki kece ta farko, Umma ya kamata ki lura ki gane ni ba sa'arki bace, kija girmanki ki kama shi ki riƙe, ni ɗin fa da kike haukar kishinki akaina ba nice kishiyarki ba, amma duk kinbi kin ɗora min karan tsana saboda kawai soyayyar da mahaifina yake min, to hala idan bai so ni ba ke zai so? karki manta kefa matarsa ce da zai iya sauyaki duk sanda yaso, ni kuma ƴarsa ce abadan abadina, so babu yanda kika iya da ganina, da za ki haƙura ma da kin hutawa kanki da cutar hawan jini, idan ba haka ba soon za ki kamu da ciwon zuciya saboda a kullum soyayyata ƙara ninkuwa take a zuciyar Babana, atoh, saboda haka please ki fita a rayuwata. Lalacewa kuma da kike magana ki gani akan Ƴaƴanki, kuma idan Baba ya dawo kika fasa karanta masa komai ke ɗin ba ki amsa sunanki ba". na nufi side ɗinmu zan shige tace,"Sabina" Cak na tsaya na juyo ina kallonta ina kuma jifanta da harara da murguɗa baki. tana nuna kanta take cewa,"Sabina ni kike gayawa waɗannan maganganun saboda ba ki da mutunci ba ki da tarbiyya, ni ɗinfa matar ubanki ce". na taɓe baki nace,"so what, dan kina matar ubana ai ba yana nufin ke ɗin uwata bace, kuma ko mene na gaya miki aike kika jawo tunda ba kya kama girmanki, ke kullum burinki kija tashin hankali acikin gidan nan, to duk wata masifa taki ta ƙare miki ke ɗaya". Yaya Abbane ya iso wurin, ya tambayeni meke faruwa, na zayyane masa komai. ya dubeta cike da jin haushi yace,"wallahi ke dai Umma anyi girman banza, ki zauna ki dinga jan ƴar cikinki da rigima. kuma a haka kike so a dinga yi miki biyayya, to ki fara kama kanki kamin nan aganki da gashin ido, ni dai ina gargaɗinki kar ki ƙara yiwa ƙanwata mugun baki, don gaba abin ba zai mana kyau ba". Umma ta ƙufulu tana huci tace,"to Abba ko dukana zaka yi ne sai nasan da gaske mataki zaka ɗauka". yace,"to wuyar dukan za kiyi ne, ki ƙara taɓa min ƙanwa ki gani".ya faɗi hakan yana cewa da ni,"mu tafi". [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(28)* bakin wani tangamemen gate motar tasu ta tsaya ƙirar lexus, kallo ɗaga zaka yiwa gidan kasan ba ƙanan mutane ke rayuwa cikinsa ba, dan tun daga farkon estate ɗin zaka san its not possible ma talaka ya shigo shi, iyakan tsaruwa gidan ya tsaru kamar a ƙasar turai, ƙaryar baki yace zai fasalta haɗuwar ginin, gaba ɗaya wajensa kewaye yake da wasu irin flowers masu ƙawata kyawun wuri. a yayin da mutanen dake cikin motar fuskokinsu ke cike da annashuwa. driver ya danna horn da sauri gate man yazo ya buɗe, suna shiga kai tsaye wajen entrans shiga main part na gidan driver yay parking motan, ƙasan wajen gaba ɗaya shimfiɗe yake da grass carpet sai hasken fitilu multi colour dake haska wurin sai kace hotel, driver ya fito cikin sauri ya buɗe booth ya ɗauko wheel chair, sannan yazo ya buɗe ma Muhsin murfin motar, sai dai bai fito ba yana zaune ya ɗauko waya a aljihunsa yana dialling number. daga cikin kantamemen parlon gidan irin 100 by 100 ɗin nan, parlon ya gaji da haɗuwa kamar ba za'a mutu ba, kewaye yake da wasu lumtsatstsun cushions na alfarma, a cikin ɗaya daga cikin cushions ɗin mai zaman mutum guda, farar dattijuwar Mata ce kyakykyawa daka ganta kaga shuwa arab, ta dubi agogon gwal ɗin dake hannunta, ta sauke numfashi, damuwa a tattare da ita tace,"Muhsina do you look up the time? your brother is still not yet back, duba ki ga har da additional five minutes on his return time". Muhsina na zaune kan
🏠