NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 87 of 98

tafa hannu yana kifawa, sai ya ɗago ya nuna ni da yatsa ya kuma kifawa ya tuntsire da wata dariyar. kamar na fashe da kuka don haushi, na juya zan tafiyata ya biyoni yana dakatar dani da cewar,"Malama dakata mana. kin manta da kyautata fa. ki tsaya ki bani sai kiyi tafiyar kije kici gaba da aikin zane na tunda na zama celebriry". "sai ka faɗi abinda kake so ai". ina faɗa ina murguda masa baki don duk haushinsa nake ji, na rufe ido ina ƙara tamke fuska ina hura hanci, kawai kuma sai kuka ya taho min lokaci ɗaya hawaye ya shiga sauko min. jinsa nayi ya kama haɓata yana ja yana haɗa ƴar waƙarsa wai nayi shiru sai kace yaga wata ƙaramar yarinya. "ki taimake ni ki bar kukan nan, ki rufan asiri a wurin Gwaggo kar na shigesu yau a wurinta". na bige hannunsa ina cewa,"ai duk saina faɗa mata ka sa ni kuka, dama tace zata rama min kwaɓe min lallan da kayi. ni ka faɗi abinda zan baka nayi tafiyata, kuma daga yau na bar kulaka". hannuna ya kamo ya jawoni kusa da shi sosai, wanda tazaran dake tsakaninmu ko 1inch bai kai ba. tukunna ya juyar dani ya ɗora haɓarsa bisa kafaɗa yana kewaye cikina da duka hannayensa, ban nuna masa haramcin hakan ba saboda ni kallon matsayi guda da Yaya Abba nake masa, ga kuma wani yanayi da na shiga wanda nasan dole ba zan iya hana shi ba. "Cutie". a hankali ya faɗi sunan daya ke kirana da shi yanzu, yana kuma manne gefen fuskarsa da tawa. na daɗa lumshe ido ina haɗiyar wani yawu kamin na amsa. "ummm". a kasalance sakamakon iskar numfashinsa dake sauka cikin ƙirjina. hannunsa ya ɗago ya nuna ƙirjina saitin ɓangaren zuciyata da manuniyar yatsansa, da wata iriyar murya ya furta, "Cutie nah, Cutien Yayanta, abinda ke cikin nan, abunda ke cikin nan nake so, shi nake so ki mani kyautarsa...kinji dan Allah". da rashin fahimtar abinda yake nufi nace,"ban gane ba. miye ne dama acikin nan ɗin banda ƙashi, indai ba kaina zan baka gaba ɗaya ba ka kaiwa Gwaggo ta dafa maka ka cinye". yay wani murmushi, yana kuma yin ƙasa da murya yake cewa. "nima nafi so ki mallaka min kan naki gaba ɗaya amma bazan cinyeki ba saboda ina buƙatarki". yana juyo dani na fuskance shi yake ƙarasa cewa,"sai dai na tsaga ƙirjina na adanaki a ciki ta yanda babu wanda zai ke kalle min wannan cute face ɗin sai idan ni naso". yana faɗin hakan yana shafa kumatuna da babban yatsansa. tsintar kaina nayi sakin murmushi, iskar bakinsa daya hura min a ido ita ta dawo dani daga duniyar tunanin dana tafi cikin ƙanƙanen lokaci, nai saurin sanya tafukan hannuna ina rufe fuskata. hannunsa yasa ya ɗauke hannun nawa, shima murmushin yake amma mai ɗauke da wata ma'ana, tun daga tsintsiyar hannuna ya kama har zuwa yatsuna yana mai tsugunawa agabana ya dire gwiwansa ɗaya a ƙasa, ya kamo yatsana na kusa dana tsakiya yana cewa dani,"please close your eyes". na rufe idona, zuwa wani lokaci naji ya saki hannuna yana cewa na buɗe idona, ina buɗewa na gansa ya miƙe tsaye, ya kalleni ya lumshe ido, sannan yay min nuni dana kalla yatsuna. ina duba hannuna na furta,"wow". da ƙarfi tare da yin tsalle, ina matuƙar nuna jin daɗina. kallon zoben nake ina jin wani farinciki a raina don ba ƙaramin kyau yayi ba, tsanin jin daɗi yasa na faɗa jikinsa tare na rungume shi. "thanku so Much Yayana, gaskiya naji daɗin ring ɗin nan ya mani kyau kamar ni. na gode, na gode Allah ya ƙara maka kuɗi da yawa". na sake shi ina cewa, "Yayana taya kasan ina son zobe matuƙa". kallona kawai yake da numsassun idanunsa ba tare daya furta komai ba, ina kallonsa na ɗaga masa kai alaman mene, duba da yanda mood nasa ya sauya zuwa damuwa saɓanin ɗazu da yake cikin nishaɗi. kai ya girgiza min alaman babu komai, na zunɓuro baki ina cewa,"to kai kurma ne, kayi magana mana". ya rumfe ido ya buɗe, har yanzu kuma bai ce min komai ba, ina wasa da zoben daya samin nayi ƙasa da kaina ina cewa,"Yayana to ka faɗa min kyautan dana maka alƙawari, ɗazun ban gane me kake cewa ba". murmushi naga yayi, ya lakuce min hanci yana cewa,"zama ki gane ne yarinya mai wayo". yana faɗin hakan ya kamo fuskata yay min kiss a goshi, tukunna ya zuba hannayensa a aljihu ya juya ya tafi, ya barni tsaye ina aikin juya zoben dake hannuna wanda har yanzu jin daɗi ya hanani rufe bakina. dukkan abinda ke faruwa tsakanin Sabina da Alhussain akan idon Haidar dake window a tsaye, be saki labule ba sai daya ga barin Alhussain a wurin, samun zuciyarsa yayi da babu daɗi, ya jingina kansa da bango tare da rumtse idanuwansa. lokaci ɗaya kansa ya hau ciwo, ya dafe ɓari ɗaya daya fi masa azaba, idanuwansa suka fara tara zafin baƙin ciki, zuciyarsa kuwa ta canza takun bugunta, gaba ɗaya duk wasu sassa da gaɓoɓin dake jikinsa sun fara shiga wani yanayi na azaba. jiri ne ke ɗibarsa sosai dan haka ya faɗa kan gado yana fuskantar sama, yana sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya. idonsa na rufe yake hasko abubuwan da suka wakana tsakaninsu, mai kama da zallar soyayya, abunda yafi tsaya masa arai yanda Alhussain yasa hannunsa acikinta da kuma haɗa fuskarsu, gashi har yana
🏠