NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 86 of 98

hannu ce, ga saman ƙirjina duk a waje kasancewarsa dukiyar fulanina acike take kuma a sama, abinda ma yasa na fito a haka saboda babu mai zuwa wajen idan ba ni ba, saima Aisha dana gani ranar nan tazo tana karatu zasu fara exams. na yunƙura zan miƙe ya maidani na zauna yana me zagayowa ya zauna kusa dani, yana jana da wasa Alallai saina bashi ya kalla. ina samun damar ƙwace hannuna daga nasa na miƙe da sauri ina ja da baya ina dariyar dake daɗa ƙawata kyawun halittar fuskata, haɓa ya riƙe yana kallona, ni kam sai dariya nake masa. na ɗan tsaya ina cewa,"ka gama ƙiyasce ƙiyascenka amma ni kam bazan baka ka gani ba". nace da shi ina yi masa gwalo. tasowa yay ya biyoni muka fara guje-guje, gaba ɗayanmu ƙyalƙyala dariya muke, banyi aune ba caraf naji ya damƙo hannuna ta baya, muka tsaya muna aikin sauke numfarfashi, ina ƙara ƙanƙame wayata saboda bana so yaga hotonsa da nake kallo. dab dani ya matso kamar zai mannu da jikina, yana zuro kansa ta kafaɗata yace,"wa na kama?". ina maida numfashi na lumshe ido, jikina yay sanyi ina jin wani iri a tare dani saboda yanda tsigar jikina ta tashi sakamakon ɗumin iskar bakinsa dake sauka ajikina adalilin numfashin daya ke saukewa shima. na turo ɗan ƙaramin bakina gaba ina cewa,"to wai miye ruwanka da abinda nake kallo, ni Allah ba zan baka wayana ba". na ƙarasa faɗa cike da shagwaɓata mai narkar da zuciya. juyo dani yay muna facing juna, fuskarsa lulluɓe da murmushi mai kyau, ya kafeni da ido ko ƙiftawa babu, nima hakan take agareni domin tunda na fara kallonsa na gaza ɗauke idona ko da na second. sautin murmushinsa ya fito har haƙoransa farare na bayyana, ya ɗan zoro min ido kaɗan yana ɗaga gira duka biyun. da sauri na sauke idona ƙasa cike da wata muguwar kunya, na fizge hannuna zan gudu ya kuma kamoni yana faɗin,"zo nan sai kin faɗa min mene kike yi da hotona?". gabana ya faɗi na ɗago na kallesa, ya sake ɗaga min gira yana cewa,"uhmm tell me, ai ina ganinki tun ɗazu, me yasa kike kalle min hotona? idan ba haka ba yanzu na shigar da ƙararki kotun Gwaggo". na hankaɗo baki gaba ina ɗan tirtirjewa nace,"wane yace maka hotonka nake kalla, to ni mene zanyi da hotonka da zan zauna ina aikin kallonsa bayan gaka a gida. na ma gane wayo ne kake son yi mani kuma naƙi wayon bazan dai nuna maka abinda nake kallo ba". na ƙarasa faɗa ina siririyar dariya me bayyanar da haƙora. shima dariyar waskewar da nake neman yi yayi, ban aune ba kawai naji ya fizgi wayar hannu, nan da nan kuwa na hau dukan ƙafafu kamar zanyi kuka ina cewa ya bani wayata kar ya buɗe min. na murguda baki ina cewa,"to ai dai ma baka san password ɗin ba, ni ka bani kayata bincike babu kyau". na faɗi hakan ina miƙa hannu zan amshe shi kuma yana kaucewa. kallona yay kawai yayi dariya kaɗan kana yace,"ki ƙaddara ban san password ɗin ba, amma idan na buɗe kyautar me za ki bani?". na ɗaga kaina sama ina nazari, tsawon daƙiƙa ɗaya nace,"shikenan naji in har ka buɗe ni kuma duk abinda kake so ka faɗa zan baka ko menene shi". na faɗi hakan saboda ina da tabbacin ba zai iya buɗewa ba, kusa da shi na tsaya ina kallon yanda zai buɗe ina masa dariya ƙasa-ƙasa. gani nayi yana rubuta Yayana, abinda ya matuƙar bani mamaki, taya akayi yasan password ɗina? bayan wayata bata taɓa zuwa hannunsa ba, kuma ban taɓa buɗewa agabansa ba tunda fingerprint nake amfani. muka haɗa ido ina masa kallo mai alamar tambaya da kuma tuhuma. na tsuke fuska na kama ƙugu ina cewa,"taya akayi kasan passowrd ena? wato ka jima kana ɗaukar mani phone kayi min bincike ban sa ni ba ko?". yanayin irin yanda yara ke rantsuwa yayi yace,"ni wallahi Allah ban taɓa ɗaukar maki waya na buɗe ba, kawai fa nayi guessing ne....to ni dai bama wannan ba tunda na buɗe saiki ba ni kyautar da kika ɗau alƙawari". ya faɗa yana sarƙe hannayensa ta baya. zanyi magana ya tari numfashina da cewa,"tsaya tsaya! tukunna ma kika ce mene za kiyi da hotona?, to yanzu mene wannan, gashi nan a wallpeper kuma gashi a screensaver. shikenan ma gano ki yarinya, wato kina kallona kowanne lokaci don ki cinye min kyawuna ya dawo kanki, saboda na fiki kyau, shine ma idan mun fita kike jin haushi idan ƴan mata na bina, to kuwa wannan kyan ƙwalelenki, ba za ki taɓa ƙwace min shi ba ki kashe min kasuwa". na kalleshi ina hararansa, na ɓata fuska na juyar da kai gefe ina cewa,"su ƴan matansu sune basu san kyau ba da har suke maka kallon me kyau, ni kam dana ke wise ai ban taɓa ganin kyan ba bare har ya burgeni...yanzuma Malaminmu ne yace mu zana mutumin da yafi kowa muni a duniya za'a buga shi a kafa hoton a gidan zoo, ni kuma ina shawara da zuciyata tace nayi drowing ɗinka, kaga ma na taimaka maka tunda kana jin daɗi ƴan mata na kallonka, kaga idan ka fita yanzu sai ake biyan naira biyar naira goma ƴan wahala suyita zuwa can suna ganinka". dariyar da ya bushe da itane yasa na juyo ina kallonsa cike da jin wani abu a raina da na kasa tantance menene, ya dage sai sheƙa dariyar yake babu ƙaƙƙautawa harda su
🏠