NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 85 of 98

he ƙafafunsa. "Gwaggo kamar yanda na faɗa miki a baya yanzu ma haka zan maimaita miki, na rantse da Allah bani da niyyar cutar da kowa a rayuwata, bare ku da kuka gama yimin gatan komai. ni kaina da Sabina tai yunƙurin taimakona nayi mamaki saboda babu wanda zai so haɗa alaƙa da mutumin da baya da asali, mutumin da baka san shi ba, ki yafe min Gwaggo, ban cuce ku ba kuma ban yaudareku ba, ina matuƙar godiya da kyautatawar da kuka yi min a rayuwa". ya faɗin hakan yana miƙewa, jikina yay sanyi nai saurin kamo hannunsa na miƙe tsaye, nauyinsa ya kamani sai dai wani gefe na zuciyata na rasa me nake ji, wani abune ya tokare wurin. shi kuma ya ɗauke kai daga kallona yay kauda fuska, yana kuma kiciniyar ƙwace hannunsa dana damƙe, murya a hankali nace,"to amma Yaya idan ba kai bane to shi ɗin daya zo wane?. kayi haƙuri na maka bahaguwar fahimta, Yaya ko kaina ka tsinci kanka a irin yanayin dana tsinci kaina za kayi mamaki." "waike maganar me kike ne?". Gwaggo tace dani, ina riƙe da hannunsa na juyo gareta ina cewa,"na rantse da Allah Gwaggo su biyu ne. surarsu iri guda ce, maganar iri guda ce, yanzu haka dana fita wajensa irin kalar kayan nan dake jikin Yaya shima sune a jikinsa, kuma shima ɗin baƙin glass ya saka saɓanin fari daya saba sanyawa, kamar yanda na dawo na tarar da Yaya zaune shima haka na tarar da shi a mota. Gwaggo dole na tsorata nayi tunanin shi ɗin ba mutum bane". na kama hannunsa ina ja nace," idan baku gasgata ni ba kazo muje na nuna maka shi nasan har yanzu yana nan domin na barshi da abinda ba zai iya tafiya lokaci ɗaya ba". ko da muka je gate babu motarsa bare ƙyallinsa, kaina ya kuma ɗaurewa, abin ya kuma ɗaure min kai da kuma tsoro, anya kuwa?. dariyar Yaya tasa ni juyowa ina dubansa, sosai yake dariya wadda har haƙonsa suka bayyana gaba ɗaya,"yarinya ta gama sa ni a ranta tazo wurin saurayinta tana masa kallon ni ne". shine abinda yake faɗa yana kuma dariya har da tafawa. "Yaya kana ɗaukan maganata wasa ko". naji haushi na bar masa wurin. abinda ya ƙunsa min shi na dawo Gwaggo ma ta kuma ƙunsa min, takaici ya isheni na shige ɗaki. cikin kwana biyu gaba ɗaya sai suka koma cewa wai aljanun kaina ne ke buɗe min ido, haka ina ji ina gani da lafiyata amma kullum a cikin yimin hayaƙi ake. na rasa ta yanda zanyi su gasgata ni amma ni dai yanzu ina da yaƙinin Yaya na da alaƙa mai ƙarfi da Proff idan har da gaske ba mutum ɗaya bane kamar yanda na fi zargi, a yanzu jira kawai nake a koma makaranta kamar yanda Farhana ta bani shawara. [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(25)* "oak see u letter". na faɗa cikin wayar dake maƙale a kunnena, kuma daidai lokacin da nayi perking motana a parking lot. Hidaya tace,"yauwa karki manta in zaki shigo ki taho min da Arable crop handout ɗin nan". na amsa mata,"ba zan mata ba insha'Allah, bye". na kashe wayan ina jefawa cikin jaka, yayin da Aisha wacce muka fita tare ta buɗe murfin motar ta fita. tana tsaye daga bakin ƙofar tana cewa,"na tafi zaki shigo da kayan ko na ɗauka?". nace da ita a sanda nake fitowa,"ɗauki ki tafi da su, ba zan shiga part ɗinku ba zanyi karatu ne". "oak". ta faɗa tana buɗe bayan motar ta ɗauki kayan da muka amso a office ɗin Baba. ko sanda na shiga ma Gwaggo bata san na dawo ba, ɗakina kawai na shiga nai wanka na sanyo english wears na fito, naci alelen da na tabbatar Gwaggo ce tayi shi saboda yanda yay daɗi. ina gamawa kuma na suri maltina a fridge nayo waje. cikin rumfar bunun dake garden ɗin gidanmu na nufa, na zauna kan deck chair ɗin dake wurin. hannuna riƙe da waya wanda na gaza ɗauke ƙwayar idona akanta tun ɗazu, abar ta batun littafin dana ɗauko zan karanta, dan tuni nayi watsi da shi gefe. kallon screen ɗin wayar nake fuskata sai fitar da yalwataccen murmushi take me cike da annashuwar jin daɗi, hoton Yayana ne na shagala a kallonsa wanda yayi matuƙar kyau, gaskiya shi ɗin kyakykyawa ne, a duk wani kallo biyu da zanma hoton sai na lumshe ido. kuma ban sani ba kawai ta bayana naji an rufe min ido, ban tsorota ba saboda ƙamshin turaren daya daki hancina kaɗai ya riga ya bayyanar min da kowa ne. na ɗora hannuna saman nasa ina ƙoƙarin cirewa, sai ya zuro kansa ta gefen wuyana yana leƙen abinda nake kallo, ina jin hakan nayi saurin kifa fuskar wayan saman cinyata don karya gani. "ni bazan gani ba?". Ya tambayeni cikin zazzaƙar muryarsa me sanyaya ilahirin jiki. ban buɗe baki na ba shi amsa ba, sai ɗaga masa kai da nayi alamar ehh, kuma har zuwa yanzu idona a rufe yake da hannunsa, ni kuwa sai aikin murmushi nake ina jin wani abu me sanyi na tsarga min. "ƙanwar Yaya ki barni na kalla abinda ya ɗauke miki hankali har na jima tsaye anan ba ki san da zuwana ba". gabana ya faɗi, wato ma ya daɗe da zuwa ban sa ni ba. _wayyo Allah yasa bai san abinda nake kallo ba._ na faɗi hakan a zuciyata ina rumtse idona dake cikin hannunsa. ajikina naji ya ƙura min ido yana kallona, duk na jin wani iri a tare dani saboda rigar jikina mara
🏠