dawowansa ne, Beauty shin za ki iya yimin alfarma? ki aminta dani ki zama matar aurena?". na wani ɗago a zabure ina kallonsa, da gaske ne dama sona yake? me yasa na bashi fuskar da har ya iya furtamin wannan maganar? cikin tsiwata nace,"dama wannan maganar ce ta kawo ka wurina?, dana san ita ce da ban fito na ɓata lokacina ba anan, idan kai kana sona to ni bana sonka domin ina da mijin aure". mtswwww naja tsaki na fito daga motan na wuce gida raina a ɓace, ba tare dana tsaya sauraron me yake cewa ba. abinda na gani a parlo ne ya razani, har ban san lokacin dana jefar da wayana a ƙasa ba na ruƙunƙume Gwaggo, sosai ganin Yaya ya furgita ni, idan nace muku shine Proff karku musa min, abinda ya bani mamaki taya akai ya rigani shigowa cikin gidan nan? na rumtse ido sosai jikina ya hau mazari, idan Yayana ba aljani bane to shi wane? adu'oi na shiga karantowa cikin raina ina ƙara damƙe hannun Gwaggo wadda ta zubawa sarautar Allah ido, har ina neman tasar hankalinta. gaba ɗaya su ma kuma saina basu tsoro saboda yanda nake yi, ina buɗe idona naga yana kusanto inda nake wanda shima ya cika da mamaki gami da tsoron abinda ya sameni, na shiga nuna shi da hannu ina karkaɗawa nake cewa,"karka zo inda nake, karka kusanto ni tunda kai ɗin mayaudari ne". yanda nake kamar wata wadda ta tada iska, ni kuwa tsabar baƙin cikin yaudararmu da yay shi ya tsayan a rai, lallai yayi wasa da hankalina, naji Gwaggo ta doka wani uban tsaki ta yarfar da hannuna. domin itama ta fahimci abinda ke tsakanina da Yaya, sai dai tunda ta gane soyayya muke ta nuna min bata so domin ba abune da zai ɗore ba. ta wuce tana faɗin,"aikin wofi, to da yake sonki sai akace miki da ke kaɗai zai zauna? to ko ni da kike ganina duk wannan uban kyan nawa Sahibina bai zauna dani ɗaya ba, haka ya ringizani da ɗai ɗai har ɓiyu, atoh tun wuri ma ki bar damun kanki akan ɗa namiji". wani takaicinta ya kamani, ni ga abinda ke damuna ita kuma tana wani zance na daban. Yayana yana zuwa ya damƙi kafaɗuna yana girgiza ni da tambayar mene, nayi watsi da hannayensa, kallonsa nake da takaici ina zubda hawaye, sam bama zan iya kwatanta haushinsa da nake ji ba a raina. cikin muryar da ta jiƙu da ɓacin rai nace. "a tunaninka mu kayiwa,? to ka yi babban kuskuren tunani domin kuwa kanka ka cuta, Allah ma ba zai barka ba domin kaci amanarmu, musamman ma ni kaci amanata kuma bazan yafe maka ba, mayaudari munafuki kawai". ai ban kai ga rufe baki ba tass naji an ɗauke ni da mari, ina kallonsa yake nuna kansa yana cewa,"me nayi miki da har za ki dinga dangantani da waɗanan maganganun?". cikin ƙunar rai nake kallonsa, cikin baƙin ciki da takaici na ɗaga hannu nima na yarfa masa maruka har guda biyu, domin nima a hasale nake kamar yanda yake.
na ɗaga muryar da ta karaɗe duka parlon nace,"an gaya maka ɗin, idan da kalaman da suka fi wannan you deserve them, me kake nema a rayuwarmu da ka biyo mana ta wannan siga? who are you?". wani irin kallo yake min na rashin fahimtar inda maganarki ta dosa, na cakumi kwalar rigarsa ina daɗa ɗaga siririyan muryana nake cewa,"Ka faɗa min waye kai? kuma mene dalilinka na shigowa rayuwata?". yay watsi da hannayena, shima ransa a ɓace kuma murya a ɗage yace,"na shigo rayuwarki ko kuma kika shigo da ni rayuwarki? idan ke zan miki ƙarya tunaninki zan zauna nayiwa manyan mutane ƙarya ne, wallahi inda na san nufinki wulaƙantani ne da cin zarafi ne da ban jinginu dake ba...me tasa za ki saka min da hakan a lokacin da na riga na gama sakankanewa?". na juya na kalla Gwaggo nace,"Gwaggo shi ɗin azzalumi ne kuma mayaudari, kice ya faɗa miki gaskiyar shi wane, ni ban yarda da shi ba, wallahi idan ba mugun mutum bane to aljani ne, ki tambaye shi Gwaggo kiji". kamar bada ita nayi magana ba tayi min shiru, Ya juya zai fice ransa a dagule. nac,"idan kana da gaskiya ka tsaya mana". tsayawa yay ba tare daya juyo ba, naje gaban Gwaggo ina daɗa ce mata,"Gwaggo ki tambayeshi shi ɗin wane? waya aiko shi? kuma me yazo yi mana?". tana sauya channel tace,"yo dama ki tsinci mutum a bola kiyi tunanin bil'adama ne, a wannan yafi kama da aljan". na turo baki ina mata wani duba saboda gaba ɗaya ita ɗaukan abin wasa take, na kuma ce mata,"Gwaggo ki bar batun wasa Alah shi ɗin dama na jima ina zarginsa, yau kuma na ƙara tabbatar da zargina akansa, yaudararmu kawai yake da sunan shi ɗin ba kowa bane, yana wasa da hankalinmu, Gwaggo ki kore shi kice ya bar mana gida kar ya cutar min daku". sai yanzu dai taga da gaske ne nake maganar, babu batun wasa, ta dube shi dake tsaye hannayensa zube cikin wandon aljihu kamar yanda ya saba, sai idonsa dake rumtse gam. a hankali yake magana. "Dama bada niyyar taimakona kika shigo rayuwata ba?, me kike zargi akaina da har kike min kallon macuci?". "na shiga uku". na faɗa ina ɗora hannu akaina. "Gwaggo ke faɗin ni dai daka zo gidan nan tsakani da Allah na ɗauke ka, ina jinka kuma tamkar jikina, bana taɓa banbantaka dasu Abba ba, shin Yaya maganganun da take gaskiya ne?". gabanta yazo ya durƙus