irin murmushi ya saki yace,"yanzu ni har sai an bani izinin kallon Beauty? kallonki fa shine abincin idanuna". na ɗago ina kallonsa, nayi shiru bance komai ba saboda wata magana da ta haska acikin kaina, wannan furucin nasa yayi salo dana Yayana da ya taɓa cewa Kallon Cutie nah abincin idanuwana. kamar yanda Proff yay ƙuri yana kallona haka nima na ƙura masa ido, don so nake na ga aina yake a zaune, idan har naga wani abu mai kama da gidan nan to tabbas zargin Yaya da nake na shine Proff to ya tabbata, sai dai banga wani alamu na shaidan hakan ba. yace da ni, "Beauty please ki bani aron hankalinki yau muyi magana kinji". "ina jinka". nace ina daɗa haɗe fuska. "ki fito gani a ƙofar gidanku". nai saurin ɗagowa ina dubansa da mamaki,"gidanmu kuma?". yace,"kar ki ɗauka wasa, am serious". ina daɗa dubansa nace,"taya akai ka san gidanmu, ni fa ban yarda da kai ba". Yay murmushi mai sauti kamin yace,"Beauty me nayi kuma na rashin yarda, kin kalla nan". ya faɗa yana nuna min wata ƙatuwar waya dake ɗaya hannunsa. map naga yana aiki, lallaima mutumin nan wato wayo yay min kenan ya kirani ya biyo sahun kiran, kamar ya san tunanin da nake yace,"nayi miki wayo ko. kiyi haƙuri nazo ba tare da izininki ba, yanzu dai ki fito waje muyi maganan da ya kamata". nace,"ai bani nace kazo ba, don haka sai ka koma". "aikuwa to yanzu zan shigo da kaina, dama yau weekend nasan Baba na gida kinga saina sanar masa da abinda ke tafe dani". nayi zumbur na miƙe ina faɗin, "ni ban saka ba, gani nan". ƙaramin gyalena na ɗauka na yafa na fita, na ce da Gwaggo nayi baƙo ina zuwa, ta bina da kallo baki a sake wato abin ya bata mamaki, ina buɗe ƙofan parlo naji tana cewa,"wayyo ni Hannatu daɗi barni da raina, yau Sabina taga zaɓin ranta, yau zanyi kwanan farinciki, dama zuwan wannan rana nake ta jira, Allah yasa dai ku daidaita, fargabata Allah yasa kar jami'an tsaron kanki su sauya miki ra'ayi, domin nima a yanzu banda burin da ya wuce naga na kaiki gida mafi girma da daraja a wurin ƴa mace". tana ta murna take faɗin haka don harda ƴar rawarta, ni dai ban kulata ba nayi ficewata. gaban gate ɗin gidanmu kaɗan yay parking motan nasa, na ƙarasa wurin da sallama, da jikin motar na jingina sai haɗe rai nake, ni har ga Allah banso wannan zuwan nasa ba, wayana yay ringing, ina kallo naga sunansa ne, na ɗaga ina cewa,"to mene kuma na kirana bayan gani nazo, ai nasan ka ganni ka fito mana". na faɗa cike da tsiwa a lokacin dana ɗaga, da murya mai ban tausayi yace,"Beauty da ace ina da ƙafafun da zan taka, da kamin fitowanki zan iso tarbanki, ki tayani da adu'a na samu lafiya naci gaba da takawa kamar yanda nake lokacin da ina ɗan shekara uku, na rantse miki Beauty daga wannan lokacin za ki zama sarauniya ta gaske, domin ni zan zame miki bafadanki a duk wani taku na tafiya naki". gaba ɗaya sai naji wani nauyi ya kamani tare da yin da nasanin furucina, dan sosai ya bani tausayi har naji dama ban faɗa masa hakan ba, driver ne ya zagayo ya buɗe min murfin motar, na leƙa kaina ciki nace da shi, "ba zan iya shigowa ba saboda Gwaggo ta hanani shiga motan kowa, ka faɗi ko mine daga nan ina jinka". yace da driver ya fito masa da wheel chair nasa, jin hakan nace. "a'a barshi kawai, bari na shigo ɗin amma sai dai ka hanzarta". kuma nima dama na faɗa masa ne don na gwada shi, saboda in har ya damu da maganar da ta kawo shi to zai fito da ƙafafunsa, ashe dai da gaske bayada ƙafan ba wasan kwaikwayo ne yake ba, tabbas shi ɗin ba Yayana bane. bayan na zauna na ɗan dube shi kaɗan naga mood na fuskansa ya sauya, raina naji babu dadi domin nasan magana ne silar hakan, nayi ƙasa da kaina ina wasa da yatsuna nace," kayi haƙuri don Allah, nasan baka ji daɗin furucina ba". kwantar da kansa yayi a jikin kujera, hakama idonsa a lumshe suke, da raunin murya ya fara magana yana cewa. "wannan shine rashin yarda da kika yi da ni? Beauty miye ribana idan na ɗorawa kaina cutar ƙarya, don kawai na samu shiga a wurin mutane? to me na rasa? ban rasa komai ba na jin daɗin rayuwar ba, ki yarda dani Beauty wallahi babu yaudara a tare dani, dukkan abinda kike gani tare dani gaskiya ne, wannan ƙafafun da ki ke gani shekaru 27 kenan rabon da su taka, anyi maganin amma shiru, kullu yaumin a zaune suke basa iya sarrafa kansu sai da taimakon wani". yay shiru tare sauke wani nauyayyan numfashi, na goge ƙwallar dake neman sauko min nace,"Allah ya baka lafiya". har lokacin idonsa a rufe ya amsa min da amin kamin ya ɗora da cewa,"tun da nake a rayuwata ban taɓa jin wata mace ta shiga raina ba sai dana fara ganinki Beauty, duk da nasan ke ɗin kinfi ƙarfina amma ina da yaƙinin za ki iya kasancewa tare dani a cikin kowanne irin hali, domin ke din kina da zuciya mai kyau, halinki mai kyau, ko mai naki me kyau... ko da nace miki kin min sata ba satar komai nake nufi ba fa ce zuciyata da kika sace, Beauty na rantse miki labarinki yasa mahaifiyata acikin farinciki, yasa ƴan'uwana a farinciki, Daddyna kaɗai ya rage ya sanki kuma shima ina jiran