NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 82 of 98

Allah ka daina wallahi bana jin daɗi kuma bana so a rubuta maka laifin zunubi". na faɗa hawaye na gangaro min, shi kuma fuska a tamke yace. "naji, ba zan kuma ba. amma kema k...". sai kuma yayi shiru ya kama hannuna muka fita yana cewa nai masa shiru na goge hawayena. muna shiga parlo Gwaggo ta taso hankalinta a tashe ta shiga tambayata lafiya duba da yanayin da ta ganni, ya saki hannuna yana faɗin. "aljanu ta tayar, ki daina barinta fita da daddare". ya faɗi hakan yana kama hannunta ya damƙa mata magani a kwalba, na kalleshi naga ya haɗe rai kuma yana maganar kamar da gaske, muna haɗa ido na murguɗa masa baki nace,"Allah ya isa". na faɗa a yanda kowa ba zai jini ba sai shi daya ganni. Gwaggo kuwa kuka ta saka sosai, tana faɗawa Uncle lalurar dake damuna, yace insha'Allahu za'ai min maganin da zasu rabu dani. "ita fa ɗaya tilo nake da ita Sulaimanu. baka ga yanda suke takura mata". ta kuma faɗa tana kuka. irin yanda take zuzuta abin kamar kullu yaumin nake tayar da su, ni harta bani haushi ma na miƙe na bar wurin, shi kuwa Uncle cewa yake. "ki bar kuka Mama, adu'a za'ayi Allah ya yaye mata, sai kuma magani da zamu durfafa wajen nemansa". tace,"to Sulaimanu dan Allah kayi taimakon daka za'a dace saboda shi ubanta ba damuwa yay da wannan ciwon nata ba, sam ko a jikinsa, don da na gaya masa ma ko razana bai yi ba. yanzu ka duba banda Aliyu yana gidan nan yanda suka tashi da wannan daren ya zanyi?, ai ni dai wannan yaro babu abinda zance da shi sai dai Allah yayi masa albarka yasa ya gama da duniya lafiya, ya kuma haɗa shi da matar ƙwarai. walla a kaf jikokina babu mai ƙaunata kamar Aliyu". ta ƙarasa maganar tana sa gefen zanenta ta goge hawaye. tace,"Aliyu Haidar". suna gaisawa da Mahaifinsa ya ɗago ya kalleta baiyi magana ba tace,"na gode maka ƙwarai kaji". "ki godewa Allah". ta miƙe zuwa ɗakin Sabina inda ta shiga ta sameta tana aikin kuka. duk yanda tayi dani akan nayi shiru ƙememe naƙi sauraronta, har saida tace zata kira Yaya Haidar yazo ayi min turare ko sune basu tafi. nai saurin cewa da ita,"a'a dan Allah Gwaggo, wallah naji sauƙi". muna haka Yayana ya shigo, kallo ɗaya zaka yiwa fuskarsa ka hangi damuwa acikinta. yazo ya zauna gefen gado yana min sannu, na tsaya ina kallonsa, kenan shima ya yarda da maganarsu aljanu na tayar, jikinsa na faɗa na kuma sakin kuka ina cewa. "Allah ni Yaya ban tada aljanuna ba, ni bani ma dasu wallahi Sharrin Gwaggo da Yaya Haidar ne kawai". yasa hannu yana shafa gashin kaina, muryansa mai sanyin daɗi yace, "na san Cutie nah bata da wani aljanu, ki rabu dasu kinji. idan ma sune Allah zai rabaki dasu, amma ki share hawayen bana son jin kukanki". ya ɗagoni a jikinsa ya kama haɓata yana goge min hawayena da hanky ɗinsa mai ƙamshin daɗi, ni kuma ina ta sheƙar kukana ina kuma ɓata fuska cike da shagwaɓa. ya haɗe goshina da nasa, ya kashe min ido guda tare da raɗa min wata magana a kunne, muka haɗa ido na ƙyalƙyale da dariya wanda tuni hakan ya wanke ɓacin ran da nake ciki. Gwaggo dake jiƙa magunguna zata bani ta juyo tana kallonmu, tana kallon Yaya da suka yi faɗa tayi ƙwafa tace,"Allah yasa su ƙara tashi suyi maka ɗan banzan dukan da zaka kasa motsawa, tunda ka zama mai ɗaurewa ƙarya gindi, wato rikicin tsufana ne yasa nace tana da aljanu ko?, saboda an faɗa maka bana ƙaunarta, to Allah yasa su bayyana yanzu su gwada maka ko ta hanyar shaƙe maka wuyana sai ka ƙaryatamu da kyau". [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(27)* Gaban mirrow nake ina drying gashina, wayana maƙale a kafaɗana muna waya da Farhana, har yau bata bar fushi dani ba akan zuwan da nayi naje na dawo banje gidansu ba, bayan nace mata a gidansu zan sauka. ina dariyar masifar da take aikin yi nake bata haƙuri ina cewa ita dai ta cika mita, nace mata inan zuwa ai, taja tsaki ta kashe wayan. ban kai ga kammalawa ba wayana ya kuma ƙara, na miƙa hannu na ɗauka, sunan Proff na gani a jikin screen na yawo ta hanyar vedio calling, na cuno baki haɗe da yin ƙaramin tsaki na ajiye, na rasa me yasa kwana biyu yake takura min da kira, shima kiran dole sai yace vedio call, idan ban ɗaga ba kuma ya addabeni da message, har saina fusata na ɗaga zan masa tsiwa sai karsashin muryarsa ya hanani aiwatar da komai, ta hakan zargina akan Yayana ya ƙara yawaita, na kuma ɗora ayar tambaya akansa akan abinda zuciyata ke saƙa min a game da shi. inata mita a zuciyata kiran ya kuma shigowa a karo na kusan biyar, dai-dai da lokacin da nake ɗaure jelar gashina, garin kai hannu na katse kiran saina danna answer ba tare dana sa ni ba naci gaba da abinda nake. sai bayan dana kammala na ɗau wayan zan fita kawai naga mutum ya tallabi fuskarsa yana aikin kallona, kallonsa nayi ya sakar min murmushi yana faɗin,"gyaran gashin yayi kyau, sai ya ƙara fito da beauty nah, kin kalla kanki a madubi kuwa ko kuma kin bar min gari na faɗa?". na samu bakin gado na zauna ina zumɓura baki, nayi ƙasa da kaina ina cewa,"to wa yace ka kalle ni?". wani sir
🏠