ba kwa gani. to ni daga yau babu ruwana na fita a sha'anin kowa. masu shegen ci idan sun mutu ta dalilin haka Allah ya jiƙan rai, suma marasa ci idan ciwon yunwa ya kwantar dasu a asibiti iyakata nabi su da Allah ya kyauta amma babu mai sa ni zaman jinya, nima kunga tattalin arziƙina ya ƙaru, dama wannan ma jiya dubu uku haka nasa na karɓo maganin nan, to ajiye shi zanyi idan Hajara ta haihu na bata in ta tashi yaye, an huta da kuma ɓarnatar da kuɗi". har ta nufa hanyar ɗakinta ta juyo a ƙufule, tana cuna Yaya da baki tace masa,"kai Zagalo daga yau idan kaga dama abincin ma ka daina ci gaba ɗaya, shine zaka burgeni. kuma ka sa ni na bar saka kwano da kai, kaje wurin Hajara ko Zara'u wani ya dinga baka, in kuwa har na kuma ganin ƙafarka tazo karɓar abinci saina bika da muciya". ta kalla Yaya Abba dake dariya tace,"kaje kai da Allah, tunda na faɗa maka bana son dariya, kuma kaima karka kuma zuwar min karɓar kwanon abinci dan ba zaka dinga sa ni almubazzaranci ba, ci sama da sau biyar a rana, ɗan ƙaramin buhun shinkafata ya dinga ƙarewa a kwana uku yo ina dalili haka kawai. amma in kuka daina zuwa nima na huta, kaga ubanka Auwalu sai ya gane ba ni nake cinye masa kayan abinci ba". tayi shigewarta ɗaki ta barmu da dariya, muka haɗa ido da Yayana munawa juna wani irin kallo muna murmushi, yanda kallon ya fara shiga jikina ne yasa nai saurin ɗauke idona. Kaina a ƙasa ina ƴar dariya nace,"ni dai gaskiya ba'a kyautawa Gwaggota, kullum a cikin tattalinmu take amma har ta taƙarƙare taje ta karɓowa mutum maganin ƴan yaye yace bazai sha ba". yace da ni,"to ke me ya hana ki karɓa ki sha?". nace,"aini na tsaya a yanda take so, bana shegen ci kuma bana ƙin ci". Yaya Abba ya haɗe rai yace,"tashi ki bar wurin nan tunda babu sa'anki". na ɓata fuska na tashi na bar wurin, aikinsa kenan idan ana zaune yace na tashi na bar cikin manya. da Magriba Uncle Sulaiman yazo Babansu Yaya Haidar, wanda shine Babba a ƴaƴan Gwaggo sai Baba da yake auta, dama su bakwai ne kuma duk sun rasu sai su biyu yanzu. tunda yazo Gwaggo ke masa faɗa akan rashin sada zumuncinsa, shi kuma yana bata haƙuri. ta dubeni tace,"ke je ki kirawo masa ɗansa yazo, dan nasan dai shi yazo gani ba ni ba". Uncle yace, "Gwaggo wallahi ba haka bane, kin san namu aikin sai a hankali ba ko da yaushe muke samun lokaci ba, amma don Allah kiyi haƙuri zan dinga yakicewa duk weekend na dinga zuwa". tayi dariyar manyace tace,"haba ɗan nan, karka damu wayarma da muke kullum ta isa, ai nasan yanayin aikin naku shi yasa ma nake maka uzuri nake kuma tausaya maka. ni dai fatana yace ko baka karɓar cin hanci? dan ƴan sanda halinku ɗaya ne". Uncle ya murmusa yace,"a'a Mama, ai a kullum ina tunawa da nasiharki da kuma faɗanki. kuma na tabbata hakan shi yasa nake samun ci gaba". taji daɗi ta kuma ƙara yi masa adu'a. ta kuma ɗora masa compalin da cewar,"ka ɗau matakin hana Junaidu zuwa gidan nan, sam bashi da kirki baiyi halin ƙwarai ba, yaran nan daga nayi masa tsiyar idan zai zo gaisheni bai iya kawo abin arziƙi ba kamar Haidar, sai dai yazo ya sa ni gaba da surutun banza, shine shekaranjiya daya tashi zuwa ya ɗuro ruwa da gishiri a kwalbar lemu ya kawo min. wallahi Sulaimanu na zaci lemun gaske ne nayita masa godiya nace yasa min a freezer sai ansha ruwa, ana shan ruwa na hau kwankwaɗa harshena ya ɗaure, ai ɗan nan ya shiga da hakkina. ni dai inaga a duniya ni kaɗai ce banyi sa'ar jikoki na arziƙi ba, Sabina ce kaɗai ƴar albarka, dama-dama ma Aliya da Husnah sai Muklas, duk da shima bai cika halin ƙwarai ba wataran, amma dai yafi su Abba a haka, dama su Aisha ba'a magana. saboda haka ni dai ka hana Junaid zuwa dan gaba zai iya jiƙa min barkono ya karni. kaga yanzu shi Haidar yau kwata-kwata ma ban sa shi a idona ba, ko gaisuwar safe wannan babu, dama sa'anni yake ganina da shi, to ban damu ba tunda gaisuwarsa ba zata ƙare ni da komai ba haka kuma ba zata rageni da komai. ni dama gaba ɗayansu maraicinsu nake tausayawa to amma sun maidani abar banza. ina faɗa maka fa Haidar har gaba ya ɗora dani a gidan nan, daga nacewa Auwalu yana shigowa da sassafe yay min sata a kitchen, shikenan ya daina zuwa inda nake sai dai yaje waje ya siyo abinci yaci". sai kuma ta fara matsar ƙwalla tana cewa,"hakan da yayi ya kyauta min kenan Sulaimanu, idan na tuna basu da uwa hankalina tashi yake, wallahi duk sanda ban saka yaran nan uku a raina ba bana samun kwanciyar hankali. to shi gaba ɗaya ya ɗauke ƙafa da shigo min, Abba da Yaya ne kawai masu zuwa na gansu naji daɗi, shi kuwa sai dai ya barni da tunanin halin da yake ci, tsakani da Allah idan na kamu da ciwon zuciya fa". Uncle ransa ya ɓaci, ya hau bata haƙuri ni kuma yace, "Sabina je ki kirawo min Haidar". ko da naje na ɗau 2minutes ina buga ƙofan ɗakinsa amma shiru, ina murɗa handle ya buɗe, nayi tsakin ɓata lokacin da nayi ina aikin bugu, ina shiga na ganshi kwance kan gado yana kallon sama, ko vest babu jikinsa sai towel dake ɗaure a ƙugunsa, na ɗauke kai da sauri ina ka