NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 8 of 98

la min kira, kaman ba zan amsa ba sai kuma na buɗe ba ki nace da ita ina zuwa, na miƙe jiki babu ƙwari kamar mara lafiya na fito. na rakuɓe gefe guda ina jiran abinda zai fito daga bakin Gwaggo, abunda naji tana faɗi ne yasa na ɗaga ido ina dubanta. “wanne Mahaukaci ne wannnan har da zai ɗaga maki hankali haka?, Sabina kin san halina fa sarai, ina da sauƙin kai amma bana son shashanci, waye shi?”. sai naji zuciyata tayi min nauyi saboda kalmar mahaukaci da Gwaggo tayi amfani da ita wurin kiran Yaya da shi, na turo baki gaba ina daɗa dubanta ta cikin glasses nawa nace. “don Allah ku daina kiran shi da mahaukaci, baku san yadda zuciyata ta ke duka ba, kalmar mahaukaci ai bata danganci mutum musulmi ba, mahaukaci ai sai dabba, shi kuma mutum ne mai kamala, don a maganar shi bata yi min kama da mai taɓin hankali ba, kawai halin rayuwa ne ya mayar da shi haka”. Zuru Gwaggo tayi tana dubana, maganganuna sun bata mamaki matuƙa gaya, cikin faɗa-faɗa ta kama cewa, “yo wai ke shin kin yi hauka ne, a ina ma kika gan shi ne tukun har kike faɗin haka, kin san dai Farhana ba zata maki ƙarya ba ko?”. “Gwaggo Allah ba mahaukaci bane, kawai dan ta gan shi a cikin kango kan bola shikenan sai ta kira shi da mahaukaci, idan ita aka faɗawa ɗan uwanta haka ai ba zata ji daɗi ba, ni idan bata yi wasa ba ma sai na daina kulata akansa wallah”. Gwaggo ta wurgo min daƙuwa tana faɗin,"ungo wannan, nace ungo, yau naji Mace, ke anya ma kuwa da kike je wurin shi bai shafa maki haukan ba, wannan wace irin macece ke, wai ke baki san duniya ta lalace haka ba, waye ke yadda da irin su musamman ma masu zama cikin kango, wannan waya san adadin yaran daya lalata daya fake a cikin nan, kar na sa ke jin wannan maganar a bakinki, kar in kuma jin kin amabace shi da sunan Yaya’n ki balle damuwa akansa...ince ko kin jini da kunnen fahimta?”. na muskuta gefe guda, ji nake kamar nayi kuka da kalaman Gwaggo, ƙasan zuciyata tuni yayi baƙi tana bugawa da sauri da sauri kamar zata fito waje. Bance da Gwaggo komai ba na Miƙe haɗe da buga ƙafa a ƙasa na bar wurin, ta biyo ni da faɗin, “ai ba ki buga ƙafar da kyau ba, da kinyi yanda zan shaida kin zama mara kunya, sai na san ta inda zan karɓeta". da faɗin hakan ta miƙe ta nufi inda wutar gawayi take ta zuba kuɓewar, kana ta shiga toilet dake tsakar gidan don ɗora alwalar magriba. ni kam shigewa ɗaki nayi na faɗa kan gado ina kukan irin cin zarafin da Gwaggo tayiwa Yaya, yau da ace ba Gwaggo bace ta faɗa haka da ko waye mun rabu da shi kenan. Washe gari da Safe kuwa ina gama ayyukan gida nace da Gwaggo zanje gidan su Farhana, bata yi yunƙurin hanani ba, sai ma ɗumamen tuwo data zuba a plask tace na kaiwa Hajiyar Farhana saboda ta san tana son ɗumamen tuwo. fitowana na tari mai napep, tunda na hau ko passenger bai ɗauka ba har muka isa ƙofar gidansu Farhana, na fito na ba shi kuɗin shi na shiga gidan. A parlon gidan na iske su duk, suna ta hira gwanin burgewa, gaishe da su nayi har yayunta Maza suka amsa suna min tsiya. na miƙa plask ɗin hannuna gaban Mamansu ina cewa,“Hajiya gashi inji Gwaggo tace na kawo maki”. Hajiya ta amsa tana murmushi ta buɗe, ƙamshin ɗumamen ya daki hancin Hajiya har da lumshe ido tana faɗin, “kaii Masha Allah, kuma kamar kin san yanzu nake cema Farhana ta kiraki ko Gwaggo tuwo tayi yau ashe kuwa shi ɗinne, kaii madalla nagode ƙwarai Allah yayi albarka”. na amsa da Amin sannan muka haura sama nida Farhana inda ɗakinta yake. kamar bani nai fushi da ita ba jiya, itanma kaman ba itane ta shareni ba, tunda muka zauna hira kawai muke zubawa ba ƙaƙƙautawa, sai ma can da ta lura ne kaman hankalina ya rabu gida biyu ta ke faɗin, "wai wani abunne kuma?”. na girgiza mata kai, ta ƙara cewa,"to sai ki bani complete attention ɗinki dan ban iya ta magana alhalin ba sanin me nake cewa kike ba". sai na ɗan yamutsa fuska nace,"ke ni yanzu ma zan wuce, amma tukunnama me kuka dafa yanzu?”. tana hararata tace,"ban sa ni ba. wannan wanne irin kuturun wulaƙanci ne, muna hirarmu me daɗi kawai kice za ki tafi. hala fushin da kike da ni ne har yanzu bai baki daina ba?". "dilla ni ba haka bane, kawai dai ina so zan tafi ne. idan ban bar fushi dake ba ai ba za ki kalla ma nazo ba". "to amma daga zuwa sai tafiya abinda ba ki taɓa ba, to ina ma zaki je wai wanda ban sani ba?, dan dai ba za ki zo ki wuce gida da wuri haka sanin cewar za kisha tambaya gun Gwaggo". naja tsaki cikin ƙosawa nace,"ke dilla Malama ni ina tambayanki me kuka dafa kina wani tsareni da tambayoyinki kamar kin kama me laifi, na faɗa maki bana son irin haka, idan kuma abincinne ba za ki banba ki faɗa min na sa ni, daɗin abun gidanmu ma akwai". duba da yanda raina ya ɓaci kuma nake magana a hasale yasa tace,"ahh ba rami me ya kawo zancen rami?, kinga ni ba baƙuwar zafi bace Allah ba ki haƙuri. indai abinci ne irish potato ne da ƙwai, kawo maki zanyi ko da kanki zaki zubo tunda Allah yasa kin san inda yake?". na kuma jifanta da harara, ban saki
🏠