yayi mummunan ɓaci, bare ki bari ya taɓa miki hannu, za ki kalla yanda zan dake". na buɗi baki zanyi magana naga har ya fice ya barni da takaici, ni yau kam gaba ɗaya sun gama ƙona min rai duk su ukun, shi ko meye ruwansa dani oho. Gwaggo kuwa tunda ta isa ɓangaren Umma taga yanayin da take ciki hankalinta ya tashi, ta fashe da kuka tana cewa,"Allah sarki Hajara sannu kinji. Allah ya ba ki lafiya ya yaye miki. wai dama shi ciwon tun yaushe ne?". ta ke tambayar Yaran. Amina tace,"tunfa jiya ne, ɗazu ma Baba ya turo Dr yazo yasa mata drip da allura. harta samu tayi bacci sai yanzu kuma da ta tashi jikin ya kuma dawowa". Gwaggo ta matsi ƙwalla tana ƙoƙarin kamo Umma ta sanyota jikinta tana cewa,"Allah sarki Sannu Hajara insha'Allahu yanzu za ki samu sauƙi, ba wai-wai za kiyi ba adu'a za ki dinga yi". tana gyara yafen mayafinta kuma take cewa,"yanzu ke gaki aba rusheshiya da na miƙar dake zaune ko kya ɗanji daɗi, jiki sai kace buhun masara. ke Amina zo ki taimakan mu ɗagata zaune, wannan kwanciyar ita zata ƙara kashe mata jiki". haka Gwaggo ta zauna a wurin Umma, sai nan da nan take da ita, bata baro wajenta ba sai da ta ga jikinta yayi sauƙi tukunna.
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(26)*
shigarmu parlo muka zube kan kujera tare da fashewa da dariya. Gwaggo ce zaune kan carpet tasa Yayana a gaba tana barbaɗa magani a abinci, gefenta kuma wasu ɗaurin magunguna ne na daban suma iri-iri. faɗi take tana cewa,"yanzu kaga idan Allah ya taimaka sai kaga cikin kwanaki kaɗan kayi kuɓulɓul da kai, saboda maganin matar nan akwai kyau sosai, so nake na gama da kai saina koma kan Abba". Yaya Abba yace,"to ni kuma Maganin me za'a samo min?". "shegen cinka da yake damuna shi zan shiga fafutukar neman maganinsa, domin wannan babbar lalura ce kake fama da ita, yawan cinka har tsoro yake bani Abba". ta faɗa tana kuma kunce wani ɗaurin ta ɗibi garin maganin ta barbaɗa acikin abincin. sai da ta gama tas tukunna tasa cokali ta juya, sannan ta tura ma Yaya plate ɗin abincin gabansa tana cewa,"gashi nan maza kaci, kaga sau uku a rana akace, kuma kai da ba ƙaunar abinci kake ba gashi har yamma tayi ko ci ɗaya baka yi ba. gaba ɗaya ni na rasa wanna irin ciki ne da kai wallahi, naso ace ma an haɗa maka da ɗurar ƙwai yanda za ka dinƙa ci babu ƙaƙƙautawa, to matsalar ba bina za ka yi ba Yaya, tunda kai ba sanin ciwon kanka kayi ba". shirun da taji ya mata ne yasa ta tsaya tana masa wani duba tace,"wai ba da mutum nake magana bane?". gaba ɗaya hankalinsa na kan waya, ba wai jinta ne baiyi ba, sarai yana jinta ya shareta, kofi ta raruma ta wurga masa ya sauka a goshinsa, ya ɗago cikin sauri yana sosa wurin yana kallonta. "Gwaggo me nayi miki? da kin fasan goshi fa". harara ta zabga mishi tace,"kai dama baka da mutunci, yanzu duk maganar nan da nake ashe ba saurarena kake ba, ka barni sai zuba nake kamar tsohuwar kanya, su kuma waɗancan mahaukatan suna min dariya. to ni duk wanda yay min dariya kansa ya cuta saboda rage imani ta ke. yanzu da ka ɗago aika fahimci ina magana da kai ko, zaka ɗauka abincin kaci ko ƙaƙa?". yace,"kai Gwaggo, wai fisabilillahi taya za'ayi da girmana na kama cin abinci da wani maganin ƴan yaye, nifa ba yaro bane. gaskiya ni bazan sha wannan magungunan ba da ban san daga ina aka samo su ba". tayi galala tana kallonsa cikin jin haushi tace,"to kana so kace min kasheka zanyi kenan, to ka sani ni ba azzaluma bace, dan ko kishiyoyina ban cutar dasu ba bare kai da kake jikana. kuma dan ubanka Auwalu banda ma ina ƙaunarka kai har kaga na damu da kaci ne, amma saboda baka yo gadon arziƙi irin na Sahibina ba shine kake faɗa min son ranka. kasan irin wahalar da nasha wajen neman gidan mai maganin nan kuwa? da ace kana da imani wallahi sai ka tausaya min, ka duba ƙafafuna tun yammacin jiya da na dawo suke min ciwo har yanzu kuma, amma sam bai dame ni ba saboda nafi so na ganku kullum acikin ƙoshin lafiya". Ya tankwashe ƙafa ya matso kusa da ita, sai daya rungumeta yace,"Hajiya Gwaggo tah ina so ki fahimci su kansu masu maganin hausan nan ba lallai sun san abinda suke badawa ba. da maganin bature ne zan sha, amma wannan da babu Nafdac taya zan aikawa cikina shi, garin neman gira a rasa ido". ta juyo ta kalle ni tace,"ke meye Nauduk ɗin daya faɗa?". irin kallon da take min yasa na gimtse dariyata nace,"kai Gwaggo ba Nauduk ba Nafdac, hukuma ce ta tace magunguna da kayan abinci, duk wani magani ko abinci ko nasha idan babu nafdac ajiki ba'a so ayi amfani da shi". "hmm". tace tana taɓe baki, ta ture Yaya daga jikinta, ta yunƙura tana tattara magungunan tana cewa,"naudok mata shegiyo dan uwar ubanta, da ma'aikatar, da masu aikinta da masu bin umarninta na haɗasu na kankantsa musu mari. shegen tsirfar banza da wofi, kai wannan bature anyi ɗan jaraba billahillazi. daga yau ɗin nan indai ni ɗin masoyiyar Sahibina ce, babu ɗan banzan da zan kuma cewa yasha magani acikinku, ku rayu ko karku rayu ba damuwata bace, ana tausaya muku amma