do yana murmusa fuska saboda walaƙanci, na ɗago ina miƙa masa hannuna nace,"ni dai kunce min na cire shi haka nan kamin ka ƙarasa dagule minshi ya koma dungulmi". na faɗi hakan bana kallonsa saboda ina jin haushinsa. murmushin mungunta yayi, yay ƙwafa kaɗan kamin yasa hannunsa ya kuma dame min na hannun gaba ɗaya, ai ban san lokacin da na kuma fashewa da kuka ba ina dire diren ƙafa, cikin tsawa Yaya Haidar yace. "dilla Malama wannan wane irin rashin hankali ne?". ina sheƙar kuka nace, "don Allah Yaya Haidar kazo ka kunce min na hannu ɗaya na cire sauran, duk an dagule min shi karya zama na tsofaffi". harara ya zabga min yace,"uban wani ya sa ki yin ƙunshin? idan ba ki shiga hankalinki kin cire shi kin tashi kin wuce ciki ba sai na tashi na ɓarar dake anan wurin. kuma karki rufe mana baki ki kalla yanda zanyi dake". ina kallon yanda ya kafeni da ido yana min wani mugun kallo. ni kam ina zumɓura baki nace,"to ni ya kake so nayi, ba zan iya cirewa da kaina ba, kuma Iklima ta tafi islamiya. kawai dan anga Gwaggo bata nan sai a dinga cin zalina, da ace ma ina da Yaya mace babu me min irin hakan". can shima Yaya Abba ya hauni da masifa,"na rantse da Allah kika katse min bacci gaba ɗaya saina taso nazo nan na faffale ki da mari, shashasha kawai, har yanzu ke ba za ki girma da kuka ba". ba shiri naja bakina na gimtse, saboda ko kowa ba zai iya aikata abinda yace ba shi zai iya, dan ya tashi yasa waya ya tafasan jiki ba komai bane a wurinsa, ganina yake kamar ƴar shekara biyar. ni ban san me nayi musu ba suka tsaneni haka, babu mai tattalina acikinsu matsayina na ƙanwarsu, abu kaɗan zanyi su hayayyaƙo min, dama ga abinda ke ƙara basu haushi shagwaɓa ni da Gwaggo ke yi, ina sheƙar kuka naketa ƙunƙuni, Yaya Haidar ya taso a harzuƙe zai bige ni. Yayana ya riga shi isowa, ya tankwashe ƙafarsa tare da kamo hannuna yana kunce min lallan. "Malami kai kuma miye hakan?". Yaya Haidar ya faɗa yana mai jifansa da harara cike da jin haushinsa. Yayana yayi masa shiru, yana sa cokali ya kankare min lallen, dama tunda yazo sam basa shiri da juna, ko magana basa yi, idan kuwa ta kama dole to a rigima za'ayita. sai can ne kuma yay maganar a fizge yace,"kai yanzu idan aka barka sai ka daketa?, Haidar kana abu kamar ba wayayye ba". Yaya Haidar ya mayar masa da cewar,"to kai abinda kayi a wurinka wayewa ne? ka kama hannun yarinyar da ba muharramarka ba da sunan kai mai ilimi". na kalla Yayana naga yana murmushi, a tunanina hannu ɗaya zai cire min sai naga ya kamo ɗayan ma ya shiga cire min, yana gamawa da hannaye ya shiga cire min na ƙafata ma. Haka Yaya Haidar ya gama kwasar haushinsa anan tsaye ya fice ya bar parlon a fusace. ni kuwa yana gama cire min na miƙe ina cewa,"kuma ban gode ba". na faɗa ina murguɗa masa baki. kamin na bar wurin ya damƙo hannuna, shima ya miƙe tsaye, dab dani ya tsaya yana cewa,"ina jin haushinki shine za ki ƙara ɓata min rai ko". ashe lallen daya cire min ya kwaso a hannunsa, ban sani ba naji ya mulke min shi a fuska, sannan ya cika ni yay ficewarsa. cike da takaici na ɗauka wayana dake ringing nayi ɗaki, ina tunanin abinda zan masa na huce, haka kawai ni ban san me nayi masa ba yana cewa yana jin haushina, na shiga toilet na wanko fuskana inata jera ƙwafa. ina karkaɗa kai na ɗaga kiran wayar daya kuma shigowa, sallamar muryar dana jine yasa ni rufe ido ina jin faɗuwar gaba, ban san me yasa ba a duk lokacin da naji muryan Proff sai gabana ya faɗi, kuma duk da cewan muryansa iri guda ne dana Yayana amma shi akan Yayana bana jin hakan, sai dai kaina yana ɗaurewa akan wasu al'amuransu. "Beauty nah". ya katse min tunanin dana tafi. "na'am sir". ko taya akai ya gane, sai ji nayi ya jefo min tambayar,"lalala wa ya taɓa min Beauty, wa ya ɓata miki rai umm Beauty nah?". cikin sanyin shagwaɓata nace,"Yaya ne, kuma ba abinda na masa". na faɗi hakan ina turo baki kamar ina gabansa. "Ya Salam shi Yayan da kansa, gaskiya bai kyauta min ba. amma kiyi haƙuri kinji, Yaya ne babu yanda na iya da shi da na ɗau mataki yanzun nan. yanzu kiyi haƙuri kinji, oya yi dariya naji". ya faɗa kamar yana magana da wata ƴar yarinya, ban kuwa san lokacin da dariyar ta subce min ba nace,"ai ka rabu da shi zan rama ne". Yay siririyar dariyar da sai dana furgita da jinta da kuma sautinta, na rantse da Allah irin dariyar Yayana sak, kalle-kalle na farayi a ɗakin naga ko dai shine ya shigo, sai naga babu kowa, na buɗe baki nace, "Proff...". ban ƙarasa ba naji an fizge wayata an jefar a ƙasa, ina ɗaga kai naga Yaya Haidar a kaina. da muryar ɓacin rai yake nuna ni da yatsa yana cewa. "ke ba ki da mutunci ba ki da hankali ba ki da tunani ba kya aiki da iliminki ko. kin maida kanki ballagaza kowane kare ɗora idonsa yake ajikinki, ki kalla a yanda kike fita parlo bayan duk kin san maza ne a wajen, amma saboda shashanci yay miki yawa an gama sangartaki ke ba ki san abinda ya kamata ba. to ki jini da kyau, duk randa kika kuma bari wancan ɗan tsintuwar ya kuma kusanto inda kike ma sai ranki