NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 77 of 98

mawa Yayanki maganin cin abinci zanyi, akwai wata Mata ƙawata Hajiya Me Riga zata min kwatace, ko yaye yaro za'ayi can ake kaishi a bashi maganin cin abinci. ki bari idan aka kuma bani wasu gaba ɗaya ma naki ne, aike ƴar lele ce". nayi murmushi ina jin daɗi, nayi mata adu'ar a dawo lafiya, tana amsawa da amin, tana kuma cewa su Yaya Abba duk wanda ya kuma taɓani bata yafe ba, tunda ita sai bata nan su dinƙa sani aiki kamar jaka, to yau ko banzan kallo akayi min ta bar mutum da Allah, gani nan amana ce, wanda yaci amana kuma ya san sauran a lahira. Yayana yazo ya wuce ta kusa da ƙafata har yana tankwaɓe min lalle, wanda nasan kuma yana sane, ni ban san me nayi masa ba yake jin haushina kwana biyu, ko magana nayi masa sai yaga damar amsa min.[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(24)* nabi bayansa da kallo ina hararsa kamar zanyi kuka, banda ina tausayinsa da saina faɗawa Gwaggo yanzun nan ta rama min. ***Ƙwiiiiii kake ji a sanda Alhussain yay wani mugun take burkin motar, Allah ya rufa asiri baibi ta kan matar da ta ɗauke yaronta ba daya fito daga cikin shop, Alhussain ya kifa kansa akan sitiyarin motar idanuwansa a rumtse. a wannan lokacin da wasu hawayen da bai san sanda suke saukowa ba, a wannan lokacin Gwaggo dake gaban motar ta sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciyar data amsa gaba ɗaya acikin motar. ta buɗe baki tana ta fitar da numfashi, gefe ɗaya ƙirjinta sai lugude yake kamar allon ƙirjinta zai faso waje. a yanda take ji inda za'ace zuciyarta ce ta fito tayoyin motar tasu tabi ta kan zuciyar ta mitstsike ba zata musa ba, tsawon wucewar wasu daƙiƙu kamin ta dawo hayyacinta, sannan ta dubi gefenta inda Alhussain yake wanda har sannan goshinsa ke akan sitiyarin. sautin muryarta ya fito da wannan fargabar da bata gama barinta ba. "Yaya kasheni zaka yi?, saura kaɗan fa kabi ta kan ɗan mutane ina hankalinka ya tafi?". magana take tayi amma sam bai ɗago ba kuma babu alamar zai ɗago ɗin. hakanne ya ɗarsa tsoro a ranta ta miƙa hannu ta ɗago shi, sai ta ganshi ruwan hawaye duk ya wanke masa fuska, yayinda da idonsa dake buɗe ke kallon waje, inda wannan matar da ɗanta ke tsaye tana rungume da shi tsam ajikinta. "kai lafiya? menene? kai ka juyo ka faɗamin halin da ake ciki, kukan namiji ko tashin hankali". yasa hannu ya goge hawayensa, sannan muryarsa ta fito cikin wani irin rauni me tsinka zuciya yace,"Gwaggo wasu iyayen Mata suna tsananin son ƴaƴansu, irin soyayyar da zasu iya jefa kansu a kowanne irin hatsari". sai yay shiru wani hawayen na ƙara sauko masa, kuma har wannan lokacin ƙwayar idonsa bata ɗauke daga kan wannan matar ba da yake jin wani abu akanta na tsarga masa ba. Gwaggo da tai kasaƙe tana dubansa tace,"hakane. amma maganar daga ina haka?". a wannan lokacin da ya shiga magana muryarsa na fita ne da karyewar kowanne harafi, kuma a yanzu kuka yake sosai. "Gwaggo me yasa tawa mahaifiyar bata kasance irin sauran ba? me yasa tata zuciyar babu wannan ƙaunar dake tsakanin ɗa da uwa?...Gwaggo ni ba ƙaramin yaro bane, na girma, na zama cikakken namiji, amma me yasa kullum nake jin ina buƙatar mahaifiyata a kusa da ni? ina tsananin buƙatar na jita a kusa dani...in da tasan ba zata so ni ba me yasa ta zaɓi ta samar dani ta hanyar da bata dace ba?, ta samar dani ta gurɓatacciyar hanya, dalilin da yasa ta jefar dani kenan a bola...ina sonta, duk da haka ina sonta Gwaggo, kuma na yafe mata ba, kuma zanso tazo gareni ko da na second ɗaya ne, nima na samu naji wannan ɗumin jikin na uwa da kowanne ɗan sunnah yake samu, wallahi ina sonta Gwaggo, ko kaɗan bana fushi da ita". ya ƙarasa furucin da wani irin murmushi me ciwo dake fita a saman fuskarsa, yana mai saka hannu ya goge hawayen fuskarsa sannan yaywa motar key suci gaba da tafi. "ka tuna me likita yace maka?". Gwaggo ke cewa da shi, kuma ba tare da ta jira cewarsa taci gaba da faɗin,"yace damuwar dake danƙare a zuciyarsa zata iya haifar maka da matsala nan da lokaci kaɗan...ka daina damuwar haka, ajikina ina jin akwai wani ɓoyayyan lamari tare da kai". tai shiru tana saka yatsa ta dungure masa kai. "kaje dan kanka tunda ni baka ƙaunar kasancewa tare da ni". sai kawai fuskarsa ta washe da wani murmushi, yasa hannu a kafaɗar Gwaggo, haka yaci gaba da driving ɗin har ya kaita inda take son zuwa. basu dawo ba sai bayan la'asar, tana shigowa ko zama batayi ba Zainab tazo tace mata Umma babu lafiya, ta zabari ƙafa ta fice a kiɗime sai salati ta ke zabgawa kamar ance mata ta mutu ne. yanzu ma da Yayana zai wuce da gayya ya kuma sa ƙafa ya shafe min tafin ƙafata, ya kuma yi wucewarsa kamar bai san abinda ya aikata ba, baƙinciki ya isheni kawai na fashe da kuka, Yaya Abba dake bacci ya farka ya doka min tsawa akan nai musu shiru, ni dai ban kula shi ba naci gaba da kukana ina kiran Gwaggo. "wai ke me yasa kuka baya miki wahala?". Yayana dake durƙusawa kusa dani ya faɗa. na ɗago na kalle shi na ɗauke kaina, na maida kaina ƙasa naci gaba da kukana. ina kallonsa ta gefen i
🏠