mukai muna abu guda har sai dana iya. to kuma yanzu kasan idon sai a hankali ni ba kallon komai nake daga nesa ba, ita kuma waccen ƴar bata tashi sai azahar". Baba ya saita mata alerm ɗin landline ɗinta, yace duk sanda taji ya buga to lokaci ne yayi. idan kuma da daddare ne ya buga asuba ce tayi. sallama yay mata akan zai fita aiki, ya ɗauko kuɗi ya bata, ta amsa tana tasa masa albarka tana masa adu'a. ta fito masa rakiya ta kalla Yayana daya shigo babu jimawa, ta dakatar da Baba da cewan. "yauwa Auwalu ni namanta inata so na maka magana. kaga dai magana ta gaskiya bana jin daɗin abinda wannan yaron yake min, wai ba zai tashi cin abincin safe ba sai rana ta take zaka gansa ya shigo zagalo-zagalo ya wuce kitchen, kuma idan ya tashi du-du ɗan abinda zaici bai wuce cokali biyar ba zai ambatar min baƙar kalmar da bana so a gare shi yace wai ya ƙoshi, kuma daga wannan ƙoshin in Allah ya yarda ba zai kuma cin komi ba sai dare. to dan Allah irin haka ba sai yaja min zagi da tsinuwa ba ace bana bashi abinci, ina zaluntar maraya bayan ba halina bane. idan ciwon yunwa ya kama shi fa tsakani da Allah, idan shi baya son lafiyarsa aini ina so, haka kawai yaja min tashin hankali ya hanani natsuwa, na koma zaman jinya. to gaskiya kayi masa magana tun kamin ya kassara kansa". Baba yace,"wa kike magana akai ne?". tana cuna Yaya da baki tace,"gashi nan wannan yaron da Sabina ta kawo. ni fa ka ganni duka su ukun ba jin daɗin zama nake yi dasu ba, ina haƙuri ne kawai da halin kowa acikinsu. kuma duk maraicinsu nake tausayawa, bare shi wannan zagalon da babu uwa babu uba, duk cikinsu yafi ɗagan hankali, amma shi baya tausayin kansa, ni kuma abin yana ci min tuwo a ƙwarya. to gaskiya idan ba zaka yi musu faɗa su sauya hali ba ni zan cewa tsohon bazawarina ya fito muyi aure kawai na huta, banda Sahibina ma ya rasu ai da basu ganni a gabansu in tattalinsu haka ba, har suji daɗin min iya shege. dan haka ni dai don Allah kaja masa kunne ya bar zama da yunwa kar yaja min tashin hankali, na kasa tsaye na kasa zaune na ƙare a zaryar neman magani". Baba yay ƴar ƙaramar dariyar rikicin Gwaggo, yana duban Yayana yace,"to kai Yaya me yasa baka son cin abinci? ya kamata ka dinga ci kaji ko, kaga ulcer dai yanzu ta zama ciwon zamani Allah ya rabamu da ita. a dinga yin abinda Gwaggo take so kunji ni gaba ɗayanku, idan ba haka ba mu daina shiri da mutum". gaba ɗayansu suka ce "to". kamin nan Yayana yace, "Baba nifa ina son cin abinci, itace sai tace dole da safe shayi ne za'a sha, ni kuma ba sha nake ba. shi yasa nake haƙura sai da rana". caraf Gwaggo tace, "to nufinka zama zan dinga yi ina dafa maka abinda kake so, to wannan sai ka bari sai kayi aure shine kake da iko akan matarka". tace da Baba, "kaga Auwalu tafiyarka Allah ya bada sa'a. ni zanma tufkar hanci". Baba na murmushi ya fita, yana fita tace da Yayana,"to yanzu daka zo min wuri ƙarfe tara mene ya kawoka?". bai bata amsa ba saboda idonsa na kaina yana kallona, haushi ya isheta ta daki cinya tace. "kanka ka walaƙanta ba ni ba". ta faɗa tana wucewarta ɗaki.
*5hours letter.*
da Yayana da Yaya Haidar na zaune kan kujera kowa da abinda yakeyi, Yaya Abba ma ya shigo daga baya, gaba ɗaya basa iya zama a ɓangarensu. ni ina zaune an saka min lallai duk na gaji da shi, gashi ko 1hr ma bai yi ba, na kishingiɗe a wurin ina bacci, muryan Gwaggo ce ta farkar da ni. "har yanzu wannan lallan bai yi bane?". tace dani tana zama a kujera. "umm baiyi ba, kuma ni walla duk na gaji". tace, "ke daɗina dake kenan kin cika raki, to kuwa karki cire shi har sai naje na dawo, dan ba za ki sani asarar kuɗi ba. ina kuɗin dana ba ki ki ajiye min ɗazu?"."yana ɗakinki cikin ƙaramar drower". "nawa ne dama da kika ƙirga?". nace, "sha biyar ne". tace,"kai Allah dai ya yiwa Auwalu albarka ya ƙara masa arziƙi...ke Iklima". ta ƙwala mata kira, tazo cikin gaggawa ta durƙusa tana cewa gata,"kije inda nace ki ɗaukon goro ranan, za ki ga kuɗi ki ɗauko min". ta tashi ta tafi ta kawo mata, ta karɓa tana dubansu, sabbin ƴan dubu-dubu ne wanda aka cira a rapa. Yaya Abba na gani ya taso ya dawo kusa da ita yana yin ƴar murya akan ta bashi nasa kason. kamar ba zata bashi ba sai kuma ta cira dubu biyu ta bashi, ta bawa Yaya Haidar ma biyu, sannan tace da Yayana kai Zagalo kaima ga naka, ya taso ya amsa yana cewa,"na gode Matar". "uhmm kaji da shi dai, ai ka kusa bani takarda ta matsawar ba zaka sauya halin cin abinci ba. haka kawai ciwon yunwa ya kamaka ka mutu ka barni da zawarci ina budurwata ɗanya shagab". ta faɗa tana miƙewa, kamin kuma tace da shi yazo ya kaita unguwa zata dubo mijin ƙawarta babu lafiya, tunda yazo dama ta daina yarda Yaya Abba ko Yaya Haidar wani ya kaita anguwa, acewarta su tuƙin sai da rai sukeyi, ita kam bata shirya tafiya yanzu bata kaini ɗaki ba. na shagwaɓe fuska nace,"to Gwaggo nifa ba ki bani nawa kuɗin ba". ta waigo daga tafiyar da take tana cewa,"ayyah ke fa muna tare, waɗan nan da kika gani asu zan cira na saya kayan dubiya, sauran kuma ne