NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 75 of 98

goge-goge ta durƙusa ta gaisheta. "lafiya lau Iklima, sannu da aiki kinji". "yauwa Gwaggo, ga abincin naki can bari na kai miki ɗaki". tace da ita, "a'a barshi tukunna ba yanzu ba. tun yaushe waɗancan Ƴaƴan suka shigo nan?". tace, "ehh sun ɗan jima". tsaki Gwaggo taja ta hau sababi,"wannan ai shine nayi banyi ba rufe ƙofa da ɓarayi, sam na rasa irin wannan abu, sai a kama zuwar maka wuri tun sassafe ko tashi baka yi ba, a shigar maka kitchen babu izininka, banda uban ci babu abinda aka saka a gaba, sai shegen kashi kamar ɓerayen daji, ina jin Auwalu rannan yana maganar sokawai ɗin gidan nan na neman cika, na rufa muku asiri nace matansa ne. to tsakani da Allah haka akeyi, gaskiya ku rage ci, ni ba zai yiwu ayita zuwar min waje ana aikin turawa ciki ba kuma babu taimakon da za'ai min, ko shara wannan ba'a iya min ba sai dai a ɓatan wuri a zunguri ƙatunan kai kamar randa a ƙara gaba. to gaskiya ni nama gaji da dafawa ƙarti abinci, Auwalu yazo ya shiga tsakanina daku, duba fa don Allah inata magana amma kun min shiru kun cika min kunne da ƙaran cokali kamar ba daku nake magana ba, saboda ni bakwa ganin girmana...to daɗin abin dai ni na haifi iyayenku, idan ku ba ku yimin biyayya ba su sa yi min ai". duk cikinsu babu wanda ya saurareta, sai abincinsu da suka ci gaba da ci, Abba yana kai cokali bakinsa ya ɗago ido ya kalleta, kamar jira take ta zabga mishi harara. Haidar na gamawa ya tashi daga dining ɗin, ta gabanta yazo ya wuce yana rataya earpiece a kunne yaje ya kunna tv, da ido ta bishi, sai daya koma kan kujera ya zauna tukunna tace da Iklima. "ke kashe min kayan kallona kinji, idan kin kammala aikinki na kunna idan zan kalla tunda kayan nawa ne ba na wani ba, kuma Auwalu ya saya min ba uban wani ba da za'a dinga yimin gadara da su, duk sanda aka tashi sai azo a kunna min ɗan iskan yaren da ni ba fuskantarsa nake ba". sai kuma ta juya kan Abba da har yanzu yake kan cin abinci, tayi ƙasa da murya tace,"yanzu kai Abba wannan dacewa ne fisabilillahi, abinda kuka yimin kun kyauta kenan?, inata magana kun min shiru kamar da dutse nake magana kun barni sai zuba nake babu mai tarar numfashi na, a haka na raineka? tarbiyar da na baka kenan? idan shi bai san dai-dai ba ai kai ka sani, kuma ni dai ban koya maka rashin kyautawa ba, duk da kaima halinka sai kai amma tunda ka ƙara ɗinkewa da wancan yaron iskancinka ya ƙara hawa sama, shi yasa na ƙagu ya gama abinda ya kawo shi ya koma gidan ubansa, tun kamin ya ruguza min tarbiyar dana shekara 27 ina baka ita". Yaya Abba yace, "amma dai Gwaggo kin san ba kyau ana cin abinci ana magana, kuma ma meye ne kike so muce miki?". tace, "au ku baku da hankalin sanin abinda ya kamata kuce min, idan babu haƙuri ai akwai lallashi. amma babu komai kowa yay na gari kansa, ni dai daga yau na bar ciyar daku. yazo yay min katangar ƙarfe daku, idan ba zai haɗaku da matansa ba to kuma yay muku ɗakin girki idan yaso kuyi ta kwaɓarku kuna ci. amma ni dai na bar girki da gardawa, atou magana ta gaskiya kenan ina dalili, Ƴaƴana basu saka min hawan jini ba Ƴaƴan wasu su saka min". tana gama faɗin hakan ta shigo ɗakin Sabina. har lokacin bata tashi ba, tana zuwa ta kashe ac, zafin da naji shi ya tashe ni, ina buɗe ido naji tana cewa da Iklima. "ki fito da kayan wankinta gaba ɗaya kamin ta tashi, naji tana batun wankesu kuma ni ba ƙaunar wankin injin nan nake ba sai naga kamar yana yaga kaya, ita kuma ba ganewa take ba saboda ba kuɗinta ne ke ciwo ba wajen saya". na miƙe zaune ina ɓata fuska nace, "Gwaggo ke kika kashe min Ac?". a hasale tace, "ban sa ni ba, mutum sai shegen lalacin banza da wofi, kiyita bacci kamar kasa ko gajiya ba kya yi, to ki tashi haka". "ni fa ban gama baccin ba, kuma ma yaushe ne rabon da nayi bacci irin haka. don Allah Gwaggo ki barni da zaran an koma makaranta fa shikenan". tace, "sai ki koma ai kiyi tayi kar ki tashi har a busa ƙaho, kuma ita dai wannan na'urar sanyi da baki da aiki sai warewa jikinki ita, to billahillazi kibi a hankali don ba gata ne kike wa kanki ba, mijinki za ki cuta, atou gaskiya nake faɗa miki ni babu ruwana". ƙunshe dariyata nayi har sai da ta fita na sa ki, na miƙe naje na kashe AC'n saboda Gwaggo gaskiya take faɗa min, na shiga toilet domin yin wanka. sai dana shirya na fito yin break, Yaya Abba da Yaya Haidar na zaune kan kujera, na gaida su kana na wuce dining, ina zama sai ga Baba ya shigo, gaishe shi muka yi, yake tambayarmu ina Gwaggo bata tashi ba ne?, a tare muka haɗa baki wurin ce masa ta tashi tana ɗaki ne. yana shiga ya tarar tana sallar walha, zama yay ya jira idarwarta, suka gaisa da Baba yace,"Gwaggo tun yanzu kika yi sallar, ai da kin bari sai anjima". tace, "walla kaga Auwalu kwana biyun nan da hadari ke haɗowa sai dai naji kiran azahar kawai, shi yasa nake yinta da wuri na huta". Baba yace, "ina agogon ɗakin ko ya lalace ne?". ya faɗa yana ɗaga kansa ya kalla bango. tace, "a'a yanayi, ai ɗan albarkar yaron nan Haidar shi ya koya min ma yanda ake gane lokacin, ranar yini
🏠