awace. sakinta tayi ta kama ƙugu tana faman cika tana batsewa sai hure huren hanci ta ke. shi kuma yaci gaba da magana a zafafe,"wai ke Na'ima me yasa a rayuwarki sam ba ki son zaman lafiya ne. yanzu abu da kika aikata a tunaninki dacewa ne?...". ai bat bari ya ƙarasa ba cikin hargowa yace,"to me nayi kuma ni ƴar gidan laifi, ni da aka tsana ake ɗora min laifi ko da yaushe". yay ƙaramin tsaki yace, "kinji matsalar taki ai, babu wanda ya tsaneki a gidan nan sai dai kowa ya tsani halinki, wannan ban zan halin naki shine ba'a so...yanzu kawai ki kama sakin tsaki a gaban babbar mace, fisabillahi wannan ɗabi'a ce mai kyau?". ta taɓe baki ta juya masa baya tana harare harare. "to ita ɗin uwa tace da ba zanyi tsaki a gabanta ba. kaga ni fa Alhaji na gaji da wannan takurawarka akan waccan baƙar matar taka, akan abinda bai kai ya kawo ba bini-bini sai kazo ka kama sauke min buhun masifa, to ni na gaji, na gaji gaskiya". ido kawai ya bita da shi yana kallonta kamin yace, "to ita kuma Khaleesat da kika hanata kula Mom ɗin nasu mene dalili?". "saboda ba ita ta haifeta ba, ba kuma ta tayani naƙudarta ba". "amma aini ubanta ne ko, kuma na isa da ƴata ko". ya kalla Khaleesat yace, "ke kije ki tattaro duk kayanki ki koma wurin Fa'iƙa da zama har sai randa na ba ki umarnin barin wajenta kinji ko". Ta ke kuwa Mami ta lailayo wata ashar ta yarfa sannan tace, "wallahi ba zai yiwu ba. ba'a isa an maida ni ɓora ba acikin wannan gida. a rasa inda za'a kai min ƴa sai wurin kishiya saboda ba'a sona ba'a ƙaunata. tun wuri Alhaji ka sauya shawara ko kuma wallahi na ɗaga hankalin kowa a cikin gidan nan". yay guntun murmushi da takaici sannan yace,"kije gidanku sai ki ɗaga hankalin kowa acan...ai tunda har yanzu kika gagara hankali to tabbas baki da ranar da hankali, kin girma amma sam baki san abunda ya dace ba. to ki bar min gida na ba ki hutu". "mtswww". taja tsaki da ƙarfin daya doki kunnuwansu. "to sai me da hutunka dama. ko baka faɗa ba dama zan tafi, abunda kawai nake so ka sa ni shine baka isa ka kaimin ƴata wurin kishiya ba, ehh wallahi kayi kaɗan". Daddy yay mata wani kallon banza kamin yace,"ba ina nufin na ba ki hutu bane. kije na sake ki saki guda". ya kalla Khaleesat yace, "wuce muje". ya bar Mami anan da ife-ife tana zage-zage kamar mahaukaciya sabuwar kamu.
_😅Masu cewa maganar Gwaggo yayi yawa hakana zakuyi haƙuri, dan Kakata nake tunawa in akazo babin Gwaggo, mu ma tamu Kakar idan ta fara sababi sai mun matseta Babban Yaya ya juye mata coflin a maƙoshi tukunna muke samun salama😅, so ku barni nake tunawa da Marigayiyata._
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(23)*
cikin ɗagin murya yace da ni. "ba za ki bani ba?". nima na cukule ina kauda fuska nace, "ehh ai kaima ga taka can kaje ka ɗauka ka ƙarasa sha, idan kuma ka ƙoshi da itane sai ka ɗauka wani sabo a kwali ai akwai da yawa". Na faɗi hakan ina fito da ita zan kuma kaiwa bakina, cikin amon muryarsa nan mai dadi ya dakatar dani. "don girman Allah karda kiyi gangancin sha, wallahi Allah bata dace dake ba, babu abinda takeyi fa ce ƙara damuwa amma bata maganin komai...". na saki wani yalwataccen murmushi da sautinsa ya amsa acikin ɗakin. sai ya ɗago yana kallona da kallo irin na mamaki. na ɗaga masa gira nace,"Yayana wai ni zaka ma wayo ko, saboda karna sha zaka ce min haka, to naƙi wayon sai nasha nima naji irin daɗin da kake ji acikinta har yasa kake min rowa". Kasaƙe yay yana dubana yayinda yake jin wani abu ga me dani na ƙara ɗarsuwa a zuciyarsa. sai ya kulle idonsa ya wani fizgi numfashi. "na rantse ba wayo ne nake miki ba. Da gaske nake miki bata maganin komai kuma wallahi bata dace...". Bai ƙarasa ba nayi saurin sanya yatsana a leɓensa alaman yay shiru. "Yayana". Na kira sunansa kiran daya ji har ƙwaƙwalwarsa, ya zuba min ido kamar yanda na zuba masa idanuna da suka taru da ruwa. "Yayana idan har wannan abar bata dace da ni ba to na rantse da Allah kaima bata dace da kai ba, saboda mutumin kirki baya shanta, mutumin da yake jin tsoron Allah baya shanta. idan har kana son lafiyarka ba zaka shata ba, idan har kana so damuwarka ta yaye ba zaka sha ba sai dai ka ɗauka maganin damuwa kankat Al-qur'ani me girma ka karanta, wannan shine hanyar da ma'aiki ya koyar damu, ba wai mu ɗauka abinda mun san zai cutar damu ba don magance damuwarmu, ita ɗin fa haramun ce na faɗa maka haramunce mene yasa ba zaka haƙura da ita ba?". Bayan na numfasa naci gaba da cewa,"haƙiƙa ba zan hanaka damuwa ba amma ba zan bar damuwa ta dameka ba Yayana, amma ina so ka fahimci cewar ƙaddararka ce a haka domin tuni Allah ya rubuta hakan zai faru da kai, dole ne kayi imani da ƙaddararka muddin kana son cika mumini na ƙwarai. A baya na faɗa maka bayan imani da ƙaddara akwai haƙuri, Yayana kayi haƙuri da yanda ka sami rayuwa, Allah da kansa yake cewa ana cikawa masu haƙuri ladansu ba tare da ƙididdiga ba. Yayana shaye-shaye babban zunubi ne mai girma ya kamata ka nisance shi, musamman abin