NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 72 of 98

na masa wani duba, baima san da zuwan nawa ba, zuciyata naji tayi zafi. plastic chair na ɗauka naje gabansa na ajiye, sannan na ɗauko kwalin sigarin daya ajiye saman table na ɗauka guda biyu, tukunna na dawo kan kujeran na zauna, ƙafa na ɗora ɗaya kan ɗaya ina girgizawa, ashana na kunnawa sigarin, duk wannan abin da nake ina kallonsa ta gefen ido yana kallona, irin kallon kissima abubuwa da dama a rai. Zuciyata na lugude na rufe idona na kai sigarin bakina ina ƙoƙarin zuƙa, da mugun hanzari ya miƙe daga zaunen da yake ya warceta a hannuna. tsawa ya doka min wadda tasa ni firgita, yana huci yake cewa, "ke ba ki da hankali ne, kinsan me kike ƙoƙarin aikatawa kuwa?". Ya faɗi hakan ransa a ɓace yana kafe ni da jajayen idanunsa da suka yi jawur. tuni idona ya ciko da ruwan hawaye har yay nasarar gangarowa saman fuskata, na zube gwiwoyina gabansa hawayena na ƙara tsananta gudu. "don Allah Yayana ka bani nasha ko nima na samu sauƙin abinda nake ji a zuciyata. Please ka bani abata nasha damuwata ta yaye, wallahi ina jin zuciyata na min zafi ne". "tashi ki bar ɗakin nan bana son rigima". Ba tare dana miƙe ba nace,"ba zan fita har sai ka bani maganin damuwata nasha, please ka bani a bata, ko kai dana zo na sameka kana sha na hanaka ne? to kuma sai kaine zaka min baƙincikin maganin matsalata".Na faɗi hakan ina ɗaga sanyayyiyar muryata. Shima gwiwoyinsa ya zube a gabana, ya runtse ido yana ajiyar zuciya, sannan ya miƙo min sigarin still idonsa a rufe kansa kuma a ƙasa a sunkuye. nasa hannu na amsa, ina karɓa ne ya buɗe idonsa, ganin da gaske shan zanyi yay saurin miƙo hannu zai kuma ƙwacewa, da sauri na ɓoyeta a bayana ina turo baki gaba. *Gwarimpa, Abuja.* ƙarfe tara da rabi na safe, kamar yanda tsarin gidan yake gaba ɗayansu ake haɗuwa a parlo idan za'aci abinci, amma idan Daddy na gari kenan. yanzu ma hakan ta ke, ba ki ɗayansu a dining, Mami da iyalanta, haka ma Mom da nata iyalin sai Anie dake zaune itama, Muhsin ne kawai babu. Daddy yay gyaran murya kamin yace, "lafiya Muhsin bai fito ba har yanzu? ko bai tashi bane?". "ya tashi, na barshi yana wanka ne, ban sa ni ba ko ya fito yanzu". cewar Muhsina. Daddy ya tashi ya wuce zuwa ɗakinsa, yana shiga ya gansa yana kokawan ciro riga a wadrobe, ya ƙarasa da sauri ya riƙe shi dan yana gab da faɗowa daga kekensa, rigar ya ciro masa ya saka masa, yana shafa fuskarsa yace,"me yasa baka kira wani ba?". da damuwa fal tare da shi yace,"Daddy ina so na fara sabarwa kaina da irin wannan ɗawainiyar, Muhsina zata yi aure soon idan Allah ya bata miji...". sai kuma yay shiru bai kuma cewa komai ba. Daddy ya sauke ajiyar zuciya cike da tausayin ɗan nasa, shima bai ce komai ba ya tura shi suka fita a ɗakin. kowa abincinsa yake ci baka jin ƙaran komi saina spoons, ana cikin ci ne Mami taja tsaki ta miƙe ta bar wurin, Abid ya mara ma ta baya, babu wanda yay magana bayan bin bayansu da kallo sai kuma girgirza kai. Khaleesat gaba ɗaya ta fara rikicewa domin wannan tashin da Mami tayi idan har bata bisu ba tasan sauran, ga shi jazaman ta miƙe sai Daddy yay ma ta magana, kuma zaice itama ta fara ɗaukan mugun halinsu ne. abincin ta dakata da ci, sai juya spoon ɗin ta ke, duk abinda ta ke Mom na lura da ita, bayan ta sauke numfashi tace, "Khaleesat". _innalillahi wa'inna ilaihi waji'un._ shine abinda Khaleesat ta ambata a ranta tare da jin faɗuwar gaba. tun ɗazu ta ke adu'ar Allah yasa kar Mom tayi ma ta magana, Mom ta kuma kiran sunanta amma bata amsa ba sai sunkuyar da kanta da tayi, ta rasa wannan wacce iriyar rayuwa ce da mahaifiyarsu ta ɗaukar ma kanta, ita kam wannan dokar da ta kafa ma ta tayi mata tsauri, Mom ta wuce gban komai, saboda macece mai mutunci. doka tsawar Daddy yay dai-dai da kiran sunanta da Mom ta kuma yi a karo na uku. cikin faɗa Daddy ke cewa, "ke dan ubaki ba ki ji Mom ɗinku na maki magana bane kika ma ta banza, ko kema kin fara bin sahun uwar ta ki ne. to ni ba zan ɗauki wannan shirmen acikin gidana ba kinjini ko. idan kina so mu shirya kiyi abunda nake so idan kuma ba haka ba babu ruwana dake". muryarta a sarƙe tace, "kayi haƙuri Daddy". shine abinda tace da shi hawaye na sakko ma ta. "ba ni za ki bawa haƙuri ba". jin abinda yace sai ta juya saitin Mom sai dai ta kasa yi ma ta magana haka kuma ta kasa kallonta sai hawaye da take saukarwa. hakan yasa Mom ta fara fahimtar wani abu, dan haka ta dafata tana faɗin, "Maminki ta hanaki yimin magana ko?". ta ƙara yin ƙasa da kanta, duk tabi ta dabarbarce ta rasa abin cewa. "kar ki damu Khaleesat kinji, ki taiwa mahaifiyarki adu'a domin abunda ta ke buƙata kenan". kai kawai ta iya jijjigawa ba tare da tace komai ba. Anie na gefe tace, "Allah dai ya kyauta halin wannan Mata, ni na rasa randa zata yi hankali wallahi". ran Daddy a ɓace ya miƙe ya bar wurin yana cewa Khaleesat ta biyo shi. Khaleesat na gaba yana biye da ita a bayansa, tana kuwa yin sallama parlo Mami ta damƙo wuyanta ta fara sauke ma ta ruwan bala'i. "saketa". Daddy daya shigo ya ce da ita a ts
🏠