sa. "tashi ka koma ka zauna". tace da shi tana dubansa da tausayawa, don jikinta yay sanyi da kallon yanayinsa da tayi. ta kalle ni tace, "Sabina ba wai ina ƙin ta taki bane, a'a ina tsoron yanda halin wannan rayuwar ta koma. za ki kalla mutum abin tausayi har kiyi masa kuka ki taimaka masa amma ƙarshe yazo ya cuceka, yaci amanarka, kuma kinga ke macece ina tsoron abinda zaije ya biyo baya, ba kowa ne kake yarda da shi ba yanzu. Kar muzo mu taimake shi yaci amanarmu daga baya". Sannan ta kalle shi tace, "bawan Allah tsakanin ka da Allah har zuciyarka baka da wata mummunar manufa, baka da wani ƙuduri na cutar da wannan yarinya dake tausayinka?". "Gwaggo zuciyata tsarkakkiya ce, bani da fatan cutar da wani a rayuwata". "to shikenan Allah yasa da gaske kake, ina son dukkan abinda Sabina ke so, dan haka zamu taimaka maka da iya abinda ta buƙata, sai dai bazan fasa ce maka kaji tsoron Allah ba. Bari mahaifinta yazo". "na gode Gwaggo Allah ya saka da alkhairi". Wayyo Allah nah wani sanyin daɗi naji ya baibaye ni. tace da ni, "kinje kin gudo ko. Bamu jima da gama waya da Hajiya ba tace za ki sani karki kuma zuwar mata gida. Kuma kayanki bayar da su zata yi, karta soma ganin koɗaɗɗiyar ƙafarki da sunan ɗaukan kaya". Dariya kawai nayi bance komai ba, tace naje na zubowa Yayana abinci, na miƙe naje na kawo masa abin sanyawa a baki, ina duƙawa zan aje masa yace,"na gode amma ki koma da shi, a ƙoshe nake da wanda kika ciyar dani ɗazu". Zuwan Baba Gwaggo ta zayyane masa komai. Baba ya numfasa yace da shi, "bawan Allah ka duba girman Allah ka faɗa mana wane kai". Ina kallon Yayana yay saurin rufe ido, kuma da alama tambayar ta Baba ta jefasa a wani yanayi na baƙinciki, ya buɗi baki muryar na fita da ainihin damuwar dake ransa yace,"wanene ni? Da ace nasan wanene ni da ban kasance a cikin wannan rayuwar ba, wallahi Baba ban san asalina ba. Abinda kawai na sa ni shine na taso a hannun wasu bayin Allah har na tsawon shekara biyu, suma kuma sun tsince ni ne a bola lokacin ba zan wuce shekaru huɗu ba a duniya a cewarsu. Amma mene asalina? daga ina nake? wanne gari? mene asalin sunana dana iyayena? ina zan bi in neme su? ina zan dosa? duk ban sa ni ba. Wallah summa tallahi bani da masaniyar komai a ga me da tarihin rayuwata". Ya faɗi hakan yana kuka. Baba Yace, "to su ina waɗanda suka tsinceka ɗin?". "sun gaji da riƙona shi yasa suka koreni daga garesu saboda mutane na zargin cewar ƴarsu ce tayi cikin shege. tun ban gama wayo ba nake yawo kwararo², idan na samu abinci naci idan ban samu ba hakan zan kwana da yunwa, banda matsuguni da makwanci sai kanguna, sai dai ina zuwa makarantar almajirai a duk garin dana tsinci kaina a haka har nayi sauka, sai dai duk inda na shiga jama'a ƙyamata suke suna hantarata. sigari na fara shanta ne saboda samun sauƙin abunda ke damuna, amma ni ɗin ba mutumin banza ba ne". Yanzu na ƙara jin tausayinsa ya kamani, su Gwaggo ma hakan take a gare su, Baba yace,"haƙiƙa duk wanda yaji labarinka dole ya taimaka maka in har yana da damar hakan. To ka kwantar da hankalinka, munyi maka alƙawarin zamu taimake ka mu share maka hawaye ka fita daga rayuwar ƙuncin da kake ciki, zan kuma maidaka tamkar ɗan dana haifa da cikina. Ina fatan ba zaka taɓa cin amanarmu ba". Furucin Baba ya sa ni shauƙi a ruhina ba kaɗan ba, ta yanda fuskata ta gaza ɓoye farincikin da nake ciki. "Allah yay miki albarka Sabina, lallai ke ɗin kina zuciya mai kyau tunda har kika yi tunanin taimako irin haka, tabbas nayi dacen ƴa ta gari. Kina da halin kirki da mutunci kamar mahaifiyarki". nayi ƙasa da kaina ina wasa da yatsun ƙafata ina jin daɗin adu'ar Baba da kuma yabona. Yayana na zubar hawaye yake yiwa Baba godiya, nima kuma yake ƙara gode min. Da wannan ya samu kyakykyawan matsuguni a cikin gidanmu, kamar yanda aka bawa Yaya Abba part nasa haka shima aka mallaka masa nasa part ɗin wanda dama shi ɗaya ne ya rage a gidan, da har su Umma na zargin Baba da munafurtarsu yake aure ne zai ƙara, to yanzu da aka bashi sai hankalinsu ya kwanta. Kowa na gidanmu Yaya yake ce masa har Baba da Gwaggo, kuma naci sa'ar ƙannena akansa. Sun zama kamar tagwaye shi da Yaya Abba, kuma duk sanda Baba zai fita office da shi yake fita, haka duk saturday and sunday yana zuwa makaranta mai suna Comprehensive collage, har mota Baba ya bashi, haka ma duk dare su kanyi zaman karatu shi da Yaya Abba don babu girman kai a tare da shi. Bayan kwana biyu na fito ɗauke da flask ɗin abinci zan kaima Yayana ɗakinsa, Ina shiga parlonsa na lumshe idanuwana ina shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren dake tashi aciki, na lura Yayana dai ma'abocin son ƙamshi ne. Kamin na kai ga gama shaƙar ƙamshin tuni wani mugun warin taba ya dakar min hanci, nayi saurin buɗe idona nasa hannu ina toshe hancina dan ƙiris na kwara amai. Raina a ɓace na wuce cikin ɗakinsa, zaune na hangeshi daga can ƙuryan gado yana zuƙar abarsa hankali kwance. idan da abinda ke sa zuciyata ɗaci na tsince shi a irin wannan yanayi, nafi minti biyu tsaye i