a min kuɗin jirgi yanzu kujeran mutum biyu, yau nake son dawowa". "tom shikenan, Allah ya dawo min dake lapia". Kai tsaye wani private hospital muka wuce, ƙwararren likita na nema, aka ƙara treating ciwukan Yayana sosai, dan sai da aka sauya masa bandage, aka kuma lodo mana magunguna kamar me, banda allurorin daya sha. Bayan fitowanmu muka nufi resturant, ordering lafiyayyan abinci na sa aka mani wanda nasan Yayana zai san ehh yaci abincin daya amsa sunansa abinci. Gaba ya saka abinci ya kasa ci sai ido daya ƙura min, dana kalla baida niyyan ci na ɗauka spoon na kai bakinsa ina cewa, "oya haaa". Bai buɗe bakin ba sai neman sauke hannuna da yayi. Na ɗan tsuke fuska nace, "Yayana zafa kasha magani naka ne, ko baka so ciwonka ya warke da wuri?, to idan kai baka so ni ina so, plsss kaci abinci idan ba so kake nasa maka kuka ba ka rasa yanda zaka yi da ni, yanzu mutane suzo su tafi da kai a kuma sanyaka a cell". Na faɗi hakan ina kuma kai abincin bakinsa, ya dafa hannuna yana tayani kai cokalin bakinsa, haka naita bashi abincin har sai dana tabbata ya ƙoshi kana na ƙyale shi, na sauke kaina ƙasa ina ɓallo magani cike da jin nauyin kallon da yake min, na bashi magungunan duk daya dace yasha yanzu, sannan muka bar wurin muka wuce wani boutique na kayan maza. Kayan maza nake ta ɗauka sama da kala nawa, duka ƴan kanti ne kowanne haɗe da takalminsa, duk wanda na ɗauka saina kara ajikinsa don tabbatar da cewan zai masa, kuma duk wanda zan gwada mashi sai ya dace da shi, hakan yasa na ƙara jin ƙananan kaya sun kuma shiga raina, domin ni ina son naga namiji nasa ƙanan kaya amma na mutumci. Shi dai bina da ido kawai yake har na kammala na kuma riƙo hannunsa muka fito, kansa na kalla wanda gashinsa ke buƙatar aski, amma saboda ciwon dake goshinsa babu damar yi. Ina kallon Hajiya nata kirana naƙi ɗagawa, na kuma taran mota muka wuce kasuwan kwari, nan ma manyan shaddojiji na saya, yadi da boyel da huluna. Muna fitowa daga kasuwan naga kiran Baba, ina ɗagawa yace da ni yasa abokinsa ya kammala komai, bakwai na dare jirgi zai tashi, ina murna nayi masa godiya, dama cikin tunanin inda zamu wuce yanzu nake. Ko rabin awa bamu yi ba a airpot jirginmu ya tashi, cikin ƙanƙanen lokaci sai gamu mun sauka a abuja, minti biyu da isowanmu Yaya Abba yazo ɗaukana. Sai yanzu ƙirjina ya hau bugu, to waima mene zance idan na kai masu shi? ta ina zan fara bayani? lallai fa nayi wawta da yawa, ko Gwaggo da nake sa ran zata fahimce ni to zan sha gwagwarmaya kamin ta aminta da buƙatar da zani da ita. Tsaye nayi na kasa ƙarasawa gaban motar, na ɗago na kalla Yayana, hannunsa da nake riƙe da shi na saki, maganganun bakina na neman rasasu nake. "Karfa naja maki matsala a gida". Nace, "babu wani matsala ka jirani anan bari na dawo". ko dana isa wurin Yaya Abba da ƙyar nasha kansa ya fahimceni, shima don yana da tausayi ne kuma mutum ne mai son yin taimako, ba komai na faɗa masa ba, hasalima ce masa nayi a yaune na fara ganinsa. Baya Yayana ya shiga ni kuma na shiga gaba, su kaima juna musabaha, naji daɗin hakan, muna shiga gida muka tarar da Yaya Haidar shima ya dawo, kallo kawai ya bimu da shi ya amsa key ɗin part nasu wurin Yaya Abba ya wuce. Na kalla Yaya Abba nace masa, "ga wannan kayan na saya masa, ka ajiye a wurinka kamin Allah yasa muji amincewan su Baba". Ya amsa ya wuce ciki bayan yacewa Yayana yaji tsoron Allah ya faɗi asalin tarihin rayuwarsa karya ɓoye komai. A parlo nayi masa masauki, na wuce ɗakin Gwaggo domin kiranta, sai na tarar bata nan, na fito zan duba kitchen saina kalleta tsaye tayi turus tana kallon Yayana dake zaune kan kujera kansa na ƙasa baima san da zuwan nata ba. Zuwa nayi na rungumeta tare da fashewa da kuka, nan ta ke hankalinta ya tashi maganar dake bakinta ta mutu. A ruɗe ta hau tambayana mene ya faru, ni dai shiru na mata ina ci gaba da kukana, sai da ta tsawatar min kana na ɗago ina kama hannayenta na shiga roƙonta. "Gwaggo nah kene kika ce min duk wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimake shi, kika ce mana mu taimakin mutumin da yake cikin tsaka mai wuya domin Allah yana son masu taimako...". "ke ni naji duk, ban son kuma wani bayanin, idan har ba za ki mani shiru da wannan kukan naki ba, kukan zan saurara ko kuma bayanin". Nai shiru ina goge fuskana. Tace, "to mene dama?". Na kama hannunta zuwa kujera ta zauna ni kuma na durƙusa a gabanta nace. "Gwaggo baya da gatan kowa sai na Allah, ko iyayensa bai taɓa sa ni ba, shine wanda na ba ki labari kika ce na fita sha'aninsa ko ki saɓa min, wallahi wallahi Gwaggo ki yarda dani shi ɗin mutumin kirki ne, jarrabar rayuwa ce ta jefa shi cikin wannan mummunar rayuwar ta shaye-shaye, Sai dai nasan ba za ki taɓa yarda dani ba sai idan kinji daga bakinsa, don Allah Gwaggo kiji tausayinsa ki taimaka masa kamar yanda muma Allah ya taimakemu ya daɗa rufa mana asiri, ina so naga ya fita daga wannan halin kuma kema nasan za ki so hakan". ta sauke ajiyar zuciya, ta kalle shi wanda tuni ya sauko daga kan kujera ya durƙusa a ƙa