na har abada kaji Yaya". kawai sai na kalla ya runtse ido yana jijjiga min kansa alaman yaji kuma zaiyi yanda nace. har cikin raina sai naji daɗi, na saki Murmushi kana nace masa, "na gode Yaya nah. Kuma ka sani idan ni bana ganinka Allah yana kallonka, dan haka ka riƙe alƙawarin daka ɗauka...alƙawari yana da girma, kayana ne karka manta da wannan". na juya cikin rashin kuzarin jiki na barshi a tsaye, yayin da nake jin kallonsa da yake bina da shi ajikina, kuma har sanda na shiga mota na zauna idonsa na kaina, zuwa lokacin da Farhana ta yiwa motar key sannan naga ya juya ya koma inda muka fito.
kuma tun bayan zaman Alhussain da kuma bayan tafiyar Sabina, tunaninsa guda ɗaya ne yake yi, _dama akwai ranar da zata zo wani ya kusance shi da nuna kulawa gami da tausayawa irin haka? Dama a cikin Mata akwai masu uzuri da kirki irin haka?_
tambayoyin da yay ma kansa kenan, a yayin da hoton Sabina ke haska mishi a ido da amsar tambayar tasa. ta kasance a tare da shi alhalin bata san shi ba, bata san waye shi ba, ba zagi, babu ƙyama, babu walaƙanci, babu tozarci, sai ƙoƙarin janyo shi a jikinta domin ta nuna masa illar halin daya jefa kansa ciki, halin daya na zaune acikinsa ne ta dole bisa ƙaddara. ayau kuma sanadinta yaji yana bala'in son kasancewa da ahalinsa, ya gansu ko da ace ba zasu kalle shi ba, ko da ba zasu karɓe shi ba, ko da zasu wulaƙanta shi. Wani abu mai zafin gaske yaji ya taɓa zuciyarsa, *SHIN WANENE SHI?*, *SU WAYE IYAYESA?*, *MENE SILAR KASANCEWARSA A WANNAN HALIN*, *YAUSHE ZAI FITA DAGA WANNAN ƘANGIN RAYUWAR?*, *HAR TSAWON WANNE LOKACI ZA'A ƊAUKA KAMIN ƘADDARARSA TA SAUYA FUSKA?*... sai yaji zuciyarsa ta matse sosai, ta yi rauni, ya dafe goshinsa ya kuma runtse idonsa da ƙarfin gaske, ya cije leɓensa na ƙasa hawaye masu zafin gaske suka shiga malala a fuskarsa, sai kuma ya fashe da kuka mai ƙarfi tare da kifa kansa a saman cinyarsa yana riƙe da kansa dake mugun sara mishi tamkar zai bar jikinsa. wannan yanayin, wani yanayi ne da yake tsintar kansa a duk sanda ya rasa amsar waɗan can tambayoyin, ya ɗau tsawon lokaci a haka cikin rera wannan kukan mai ƙaramin sauti tamkar ba matashin saurayi ba, tukunna ya miƙe ya tafi masallaci dalilin kiran sallar daya ji ana yi, bai baro cikin masallaci ba har sai da akayi sallar isha'i kana, nan ma sai da za'a rufe masallacin sannan ya fito. A dawowarsa ya tsaya a dai-dai inda motar su Sabina tayi parking ɗazu, kallon wajen yake da haskawar hoton abunda ya faru a ɗazu, bai san dalili ba, amma haka kawai yaji yana so yarinyar ta ƙara kasancewa da shi. sai yasa hannu ya matse idanunsa dake rufe, ƙasan zuciyarsa na raya masa da cewar _ko zata sake dawowa?._
*Please don't forget to comment, vote and share.*
*AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(3)*
da wannan tunanin ya samu wuri ya zauna, zuciyarsa tana cigaba da tunani iri-iri, tunanin duniya, tunanin rayuwarsa da tunanin yarinyar da ta fara raɓarsa tun bayan sanin kansa da yay. motar Farhana na tsayawa ban ce komai ba na buɗe murfin motar na fita cikin fushi ba tare da ko na dubi inda Farhana ta ke ba, can ƙasan murya na furta,"nagode ki gaida su Hajiya". tace da ni,"zasu ji insha'Allah, amma ba ki ɗauka kayan da muka saya ba”. wani irin kallo na bita da shi ta ƙasan ido, ban ko yunƙurin amsa ma ta ba, dan abunda tayiwa wancan bawan Allah'n ji nake tamkar Yaya Abba da muke ciki guda ta yiwa, shi yasa tun tahowarmu nake fushi da ita, kuma ina ganin kaman ba zamu shirya ba har sai mun koma wajensa ta bashi haƙuri yace ya haƙura tukunna.
ban rufe ma ta ƙofa ba sai dana ja tsaki tukunna na fara tafiya na ɗauka hanyar gida, ganin hakan yasa Farhana fitowa daga motar ta buɗe boot ta ɗauko kayan da muka saya ta biyo bayana da shi. A ɗan ƙaramin tsakar gidanmu wanda yasha shara baka ganin ko da ɗigon datti, na tarar da Gwaggo tana goga kuɓewa, sallama kawai nayi na shige ciki, ban ma san ta amsa ba ko bata amsa ba, kuma ajikina nake jin yanda Gwaggo ke bin bayana da kallo, kuma shirunta ya bani tabbacin tana tunanin yanayin da ta ganni aciki ne. Farhana ta shigo, Gwaggo ko amsa sallamarta ba tai ba tace mata,“yauwa yanzu kuwa zance to ya akayi baki shigo ba, ashe kina bayanta, meye sa me ta ne? naga daga sallama ta shige ciki, Allah yasa lafiya ne". Farhana tace, “lafiyarta lau, ai kin san halinta da ɗan banzan saka damuwa a rai, wai fa wani mahaukaci ta gani a hanyarmu ta dawowa gida shi ne ta ɗaga hankalinta haka". ta duƙa a gaban Gwaggo ta aje ledar hannunta da cewa,"ni dai zan wuce Gwaggo sai wani lokacin, ga shi wannan nata ne”. Gwaggo ta maida hankalinta kan kuɓewar da ta ke gogawa tace, “to madalla, kyace ina gaida Hajiyarku”. Daga haka Farhana ta gyara zaman glass nata ta fice. Maganar Farhana ta tsayawa Gwaggo a rai, don kuwa sarai ta san halin Sabina, zata iya yin komi akan wannan mahaukaci kamar yadda Farhana ta faɗa mata, to amma meye nata na damuwa haka, koma meye dai zata ji. ina kishingiɗe jikin pillow naji Gwaggo na Ƙwa