llon gefe guda yace,"abubuwan da yawa...na farko anyiwa wata yarinya fyaɗe hr ta mutu shine aka ɗora alhakin hakan akaina, na jima kamin gaskiya ta bayyana, ashe Baban Yarinyar yana harkar ƙwayoyi sai suka sami matsala da yaransa shine suka ɗau fansar abunda yay musu akan yarinyar. bayan na fito da ƴan kwanaki aka sace yara anan anguwar, mutane suka ɗora min laifin da banji ba ban gani ba akan cewan ni na sacesu, bisa wannan zargin nasu yasa ƴan sanda suka kamani, nasha wuya sosai a wurinsu har naji inama na mutu na bar wannan rayuwar ƙuncin, a ranar da zamu wuce kotu ranar akaga yaran, sati ɗaya kenan da aka sakeni, na dawo duk inda naje na zauna domin samun mafaka sai an koreni, babu wanda ya tsauyawa halin buƙatar taimakon da nake ciki sai limamin wannan masallacin, shine ya kaini chemist aka bani kulawa". Tunda ya fara maganar nake kuka sosai, har ta kai ga na daina sauraron abinda yake cewa, hannu yasa ya dafa goshina ya ɗago fuskata da tayi shaɓe-shaɓe da ruwan hawaye. Ina kallo ya yagi ƙasan rigarsa yay min tsumman goge hawayena "kina so a kuma kamani ne?". Ya faɗa a yayin da yake gogen gefen idona wanda nake tunanin kwalli ne ya zazzago. Na shiga girgiza masa kai da sauri alamar a'a. "to ki bar kuka, kar mutane su ganki ace nayi miki wani abun, a ƙara kamani ayi min ɗaurin rai da rai". Babu shiri na tsayar da kukana, ina faɗin,"wallahi ba zan taɓa yafewa wanda yay maka wannan sharrin ba, wallahi ba zan taɓa yafewa wanda ya wahalar da kai ba, Allah ya bi maka hakkinka. Me yasa daka dawo baka kirani ba?". "ta ina zan kiraki?". "nafa aje maka letter da zan tafi, na san kuma har zuwa lokacin yana nan tunda babu wanda ke shiga sai kai, kuma nayi yanda ko da iska ba zai iya figansa ba bare ruwa ya lalata shi". Yay wani murmushi mai ciwo, damuwa na daɗa bayyana a tare da shi. "tunda na sanyo ƙafata cikin anguwar nan ake min ruwan duwatsu akan saina koma, da ƙyar wasu bayin Allah suka taimakeni. Ba daban ina da yaƙinin idanuwana zasu ƙara ganinki ba, da ba ki zo kin kuma samuna anan ba". Hannunsa dake cikin nawa ya daɗa matsewa ya damƙe, idanunsa a runtse ya shiga juyi da kansa yana faɗin. "tunda suka kamani, tunda suka sanya ƙafafuna a sasari, tunda suka jefani a ɗakin duhu, a kowanne bugun azabtarwa, a kowanne nau'in horo mai wahala, a duk wani bugu na zuciyata kece a raina, bana jin daɗin duniyar, har saina rufe idona na hasko ki aciki sannan nake samun sassauci. Don Allah kice min kina da alaƙa da ni, ki ce ke ɗin jinina ce, ki ce kin shigo rayuwata ne domin ki share min hawayena". Ya gama faɗin hakan yana mai jinginar da kansa jikin bishiya, ya kuma ƙara damƙe hannuna wanda har sai da jikina ya amsa, yana ƙara rumtse idonsa sosai. Nace da shi,"Yayana ba zan iya barinka a wannan halin ba, yau ɗin nazo tafiya da kai ne. Ba zan kuma barinka a cikin ƙangin rayuwa ba...daga yau insha'Allahu ka bar wannan gararin, dan zanyi maka gata a yayin da zan sanyaka cikin ahalina, zan tabbata ƙanwa a gareka a yayin da zaka tabbata Yaya a gareni ka kuma tabbata ɗa a wurin Babana, a inda zaka tabbata jika a wurin Gwaggona. Insha'Allahu lokacin yayewar baƙin cikinka yayi, haka kuma lokacin dawwamarka a farinciki yayi, ba zan kuma bari ka shiga damuwa ba har abada". Sai yanzu ne ya buɗe kyawawan idanunsa ya zuba su a cikin nawa. Ido cikin ido muke kallon juna, har sai da kwarjininsa ya kashe min ido tukunna nayi saurin kawar da idanuwana daga kallonsa. Na miƙe ina jan hannunsa akan ya tashi mu tafi. murya a ƙasan maƙoshi yace,"nan shi yafi dacewa da ni, idan kika tafi da ni ina za ki kaini?". "nan ba shine ya dace da kai ba. Kyakykyawan mazauni shi ya dace da kai, kaifa mutumin kirki ne, don girman Allah Yaya ka tashi mu tafi gidanmu, na rantse maka idan bamu tafi tare ba, ba zan bar cikin layin nan ba zakaji saƙon mutuwata, na tafi inda ba zaka kuma ganina ba sai a aljannah". Zumbur naga ya miƙe, ina riƙe da hannunsa muke tafiya kaman wani yarona, wanda nayi hakanne gudun kar ya tsere min, har sai da muka fito bakin layi na tari me napep kana na sake shi lokacin da muka shiga ciki. Muna tafe ina tunanin yanda zanyi da Yayana, Hajiya ba zata taɓa fuskantar wani zance da zan mata ba, don haka ya zame min dole na koma gida a yau. Na ɗauko waya na kira Baba yana ɗagawa nace,"Baba kana so na?". "Sabina babu sallama babu gaisuwa sai tambayar dake kin san amsarta". Na lumshe ido ina ƙara narke fuska nace,"Baba ni dai ka amsa min". Murmushi mai sauti yayi yace, "ina sonki sosai Sabina, duk cikin ƴaƴana bayan Abba nafi sonki na kuma fi ji dake". Maganan Babana yay min daɗi, na ƙara ce masa,"to Baba indai da gaske kana sona kayi min buking jirgi yanzu, zuwa anjima zan dawo gida". "ki dawo kuma? Wani abu ya faru ne?". Nace da shi,"a'a Baba babu abinda ya faru, kawai zan dawo ne na gaji da zaman". "a'a ban yarda dake ba ki dai faɗa min gaskiya, ko Hajiya tayi miki wani abu ne?". "ko ɗaya Baba, mun gama gaisawa da Hajiya kuma dama ai ita nazo gani, don Allah Baba ni dai a biy