kake nufi ba?". "ina nufin yana gidan maza, kusan wata shida da kamashi kenan". Nai ƙoƙarin tare kukan dake neman fito min nace, "a bisa wanne laifi aka kama shi?". Yana ƙulla madara a leda yace, "yo Hajiya irin waɗannan ai annoba ne a unguwa, hukuma tayi ram da su shine dai-dai". Ban iya cewa da shi komai ba na juya na fita da ƙafafuna da suka min nauyi, idanuwana na tsananta zubar hawaye, zafin da nake ji a zuciyata ba zai iya misaltuwa ba, ni ɗaya nasan tashin hankalin da nake ciki, saura kaɗan wani mai mashin ya bigeni naji an jawo ni, mutumin ya hauni da masifa ina tafiya ina tunanin banza zan haɗa accident. Sam ban san halin nake ciki ba sai a yanzu da yay maganar, na kalla inda nake tafiyar na kalleni tsakiyar hanya da ababen hawa ke wucewa. "kayi haƙuri don Allah". Ina faɗa ina ƙoƙarin barin wajen. "idan ba damuwa ki tsaya zanyi magana dake. Zan shiga wancan shagon naga kin fito kina kuka, na tambayi mai wurin yake gaya min wanda kike nema". Ni dai bance masa koma ba, sai dafe kaina da nayi wanda naji juwa na neman ɗibata ta zubar a ƙasa. Maganar da yay ne ta dawo dani hayyacina nayi saurin ɗagowa ina dubansa. "ya ce mashayin bakin bola kike nema?. Duk abinda ya faɗa miki gaskiya ne amma bai san da cewar an fito da shi ba. Sai dai ya bar wurin da yake zama, idan kika zaga bayan masallacin nan daga wajen wata bishiya za ki gansa zaune a wurin, yanzu muka fito daga masallaci tare da shi". Ban jira sauran maganarsa ba, haka Ko godiya ban tsaya yi masa ba, tuni na juya ina tafiya cikin sauri har na isa inda yay min kwatancen. Ina zuwa kuwa na hangi mutum zaune akan dutse ya juya baya, ban san lokacin da murmushin jin daɗi ya subce min ba, na ƙarasa wurinsa ƙafafuna na rawa, na tsaya a bayansa ina jin kamar na rungume shi saboda yanda nake jin wani farincikin a raina. "Yayana". Na kira sunansa ina mai jan harufan ta wani irin siga ba tare da nasan nayi hakan ba. shi da yake zaune yaji muryar da har mutuwarsa ba zai taɓa mantawa da ita ba, yay shiru yana jiran ƙara sauraron zaƙin muryar, ganin bai juyo ba hakan yasa na zaga gabansa cike da zumuɗin son ganin fuskarsa. Annashuwar farinciki na ƙara bayyana a saman fuskata na zube a gabansa, haƙorana duk a waje saboda na kasa ɓoye jin daɗina, sai dai yanayin da idona ya hau kansa komai nawa ya tsaya cak, hankalina yay ƙololuwar tashi, a jere na jefa masa tambayoyi baki na karkarwa a yayinda da ruwan hawaye ya cika min ido suna zuba. "Yayana mene haka nake gani a jikinka? Wannan bandage ɗin na mene? Aina ka sami ciwuka masu yawa haka? garin ya ya hakan ya faru da kai? wane yay maka hakan?". Nayi maganar gefen zuciyata na harbawa da tsananin zafi, a yayinda tsananin tausayinsa ya kanainaye ilahirin jinin jikina, na miƙa hannuna dake rawa zan kamo fuskarsa ya janye kansa. a hankali laɓensa na sama dana ƙasa suka tale suka buɗe wajen faɗin. "ina kika tafi watanni da yawa? me yasa kika daina zuwa inda nake? me yasa na daina ganinki? a haka kika fito da fuskarki waje jama'ar duniya suna kallonki? Ina niƙab ɗinki? Me yasa ba ki saka ba?". A wani irin yanayi tambayoyin nasa suka jefani, yanayin dana kasa gane mishi, na kasa jurewa kallon da yake min na sadda kaina ƙasa, nafi buƙatar daya amsa min nawa, ina ɗagowa naga ya kauda fuskarsa gefe, idonsa a lumshe, yana ƙoƙarin tashi ya bar wurin nayi saurin kamo hannunsa na maido shi ya zauna.
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(22)*
harufan bakina na fita a kakkarye nace da shi,"Don Allah Yayana". kalaman bakin suka fito acikin siga ta roƙo ina mai ƙare damƙe hannunsa. Cak ya tsaya ya dawo ya zauna, yana ta so ya ƙwace hannunsa daga riƙon dana masa amma na hana, kansa na kallon ƙasa yay shiru bai magana ba, damuwa na ƙara bijiro min na datsi shirun da cewan,"Yaya zuciyata matsewa takeyi, dan Allah ka faɗa min wannan ciwon fa?". ya ɗago ya sareni da ido, sannan ya buɗi baki yace,"ni me yasa ba za ki amsa min nawa ba?". "to aini na fara tambayanka". Yace, "idan har aka ɗora duka tambayoyin a bisa mizanin ma'auni, nawa ita tafi muhimmanci da cancantar amsawa sama da taki, duk da cewan tambayanki yafi yawa amma girman tawa zata rinjayeta. Na rantse miki idan har ba ki bani amsar dalilin da yasa kika fito babu niƙab ba, zan tashi na tafi, tafiyar da har abada ba za ki kuma ganina ba". Ban san lokacin dana haɗa yatsuna da nashi wuri ɗaya ba ina wasa da su, na fara magana ina cewa,"kamin mu bar gari nazo har sau huɗu bana samunka, har a ƙarshe na bar maka saƙo wanda idan ka gani zaka neme ni. ba haka kawai na daina zuwa inda kake ba, mun koma Abuja da zama ne sai yau na sami daman zuwa, kuma na bar niƙab ɗina a can shisa, ita kuma Hajiya bata da shi bare na amsa na saka. Yayana tunda na tafi kowanne rana a cikin tunanin halin da kake nake, haka zalika a cikin kowanne daƙiƙa na bugawan agogo jiran tsammanin kiran wayarka nake amma shiru. Yayana ina ka tafi a wancan lokaci? Me yasa na dawo na sameka a wannan halin?". idonsa na ka