ba". "au saboda ba ki da kunya ni kike faɗawa wannan maganar, yo ba ƙwamma ita bazawara ce ba, ke kuwa fa. Shekaru 19 kina ƙoƙarin dosar ashirin amma ba ki taɓa leƙan gidan miji ba. Ba tun yanzu ne nake tambayar yaushe ne za kiyi aure ba? Ganin sa'anninki duk sunyi aure, Amma ganin laifina ake ba'asan mutunci nake nema miki ba". abun yay min ciwo, ban san lokacin dana fara ce ma ta, "Addah Jummai, Inna Talatu, Gwaggo Ladi, Hajiyan Jos. Inna Sa'anninki da yawa duk sun jima a ƙabarburansu, mene yake faruwa dake ne? Ya akai ke shiru haka? Ya naki labarin tafiyar? Yaushe ne za ki mutu? me yasa aka zuba maki ido har yanzu ba ki mutu ba?". Ina dubanta naga tayi shiru, nace, "Inna tambayarki nake ki bani amsa". Nan ma shiru tayi min, na sake cewa, "To Innah Yanda mutuwa bata da lokaci haka ma aure, yanda mutuwa ba gasa bace hakama lokacin aure, yanda burin kowa Aljannah haka burin duk wani marar aure abokin rayuwa nagari. Yanda ba'a rubuta ma kowa lokacin mutuwarshi a goshin shi ba, hakama wasu ba'a rubuta musu rabon aure a rayuwarsu ba, kuma ba'a rubuta musu lokacin auransu ba a goshi. Ni kuma bana rasa mijin aure bane, ban shirya yi yanzu ba, ki bar ganin banda mashinshina. Don Allah Innah ki sakar min mara kiji da Mardiyya ita da zaman ɗaka kawai ta ke babu arabi babu boko". Ina kallon Gwaggo na dariya ƙasa-ƙasa, ni kuwa na miƙe nai wucewa ta ɗaki, ina jinta tana faɗin, "to aini da na shigo wannan daular niyyata na jima ina shan jar miya mai naman ɗawisu acikinta, ashe tafiyata dole ta kama gobe goben nan". Gwaggo tace da ita, "kofa mene ke kika ja ta gaya miki haka, akan me kuma za ki ji haushinta". Kwanan Innah biyu muka wuce kano, naji daɗi da bamu taho da Yaya Abba ba, a gidan Hajiya na sauka wadda ta haifi Mamana, tayi farincikin ganina sosai. Abinci kawai naci na miƙe na shiga wanka, ban ɓata lokaci ba a shirin da nake yi, nayi kwalliya mai kyau, hijab ɗina sai tashin ƙamshi yake na fito, Hajiya dake kishingiɗe a parlo ta dube ni tace,"ke kumburin burodi ina zuwa kuma daga saukarki? Ko abincin da kika ci fa bai gama tsarga miki ba". Ni kam bana son wannan sunan da Hajiya ke kiran da shi, da yake itama ƴar ayi ce irin Gwaggo, na ɓata rai ina cewa, "Hajiya na fa yi girman da ya kamata ki daina ce min kumburin burodi". "to Mama'nki ma har ta mutu ban daina ce mata kumburin burodi ba, kinga kema kuwa banga ranar daina faɗa miki ba tunda kinyo gado". Na turo baki gaba ina yin kamar zanyi kuka, ta kamo hannuna ta zaunar dani Saman cinyarta, ko nauyina ba ta ji. "haba jikar Hajiya da Gwaggo sarkin shagwaɓa, ƴar lelen Babanta, maida bakin naki kar ya tsaya a haka samari suce basa so, kinga yayi dogo da yawa sai kace payis". Ta faɗi hakan tana ɗan yimin cakulkuli, na ƙyalƙyale da dariya kamin na kuma cewa,"amma dai kin daina cemin Kumburin burodin ko?". Tace, "kema kin san ba zan iya ba, saboda duk sanda na tsokane ki da haka kina tuna min da marigayiya ne, komai naki sak na mahaifiyarki har wannan shagwaɓar. Itama idan nace kumburin burodi haka zatai ta aikin buga ƙafa tana cewa bata so, Babanta kuwa hake yake ce mata kazar gona, shi kam daya faɗa zata fashe da kuka sai ansha da ƙyar zata yi shiru, Sabina wallahi komai naki babu maraba da Halima". "Allah sarki Mamana Allah ya jiƙanta. Hajiya naso ace naga Mama ko da sau ɗaya ne, amma ko da yaushe sai dai na kalleta a hoto ina jin kamar na fito da ita tayi min magana". Ta goge min hawayen daya sakko tana cewa, "karki kuka mana kuma ki ɓata kwalliyar taki, ba gashi Allah ya bar miki mu ba. Ina za ki ne haka kamar wadda ta shirya gasar kyau?". "da gaske Hajiya nayi kyau?". "wallahi sosai ma kinyi kyau, tsab za kisa ɗa namiji tuntuɓe a hanya. amma ni kin san bana son fice-fice ina zuwa haka?". Ina roƙonta nace, "don Allah Hajiya yanzu zanje na dawo, gidansu Farhana zanje". Da ike itama tasan Farhana tace to saina dawo amma kar na jima. ina tsokanarta nace, "to Hajiya idan kinji shiru sai ki bini Abuja". Dariya kawai tayi ni kuma na fice, sai dana bari nayi nesa da gida kana na tari mai napep saboda kar Uncle Musbahu ya ganni, don naji yana shago yana ɗinki. Sharaɗa nace masa ya kaini, har inda Yayana yake zama ya sauke ni, na fito ina kallon wajen har ya fara sauyawa saboda yanda aka yiyyi gine-gine, shi kansa kangon da Yayana ke zama ciki har an fara sa masa dakin, waje ma anyi masa fulasta. Ƙafata tayi sanyi, ƙirjina na bugawa na ƙarasa ƙofar kangon, gaba ɗaya na dudduba banga alamar ƙyallin ko inuwar mutum ba. Tuni naji komai na duniya ya daina min daɗi, na shiga tsananin damuwa, ina taka ƙafa da ƙyar na ƙarasa wurin wani mai shago, sallama na masa ya amsa min, na tambayeshi don Allah ko yasan wani bawan Allah dake zama a kangon nan na kusa da shi. "wani ɗan shaye-shaye ko?". Ya tambaye ni. banji daɗin tambayar da yay min ba, domin da a hayyacina nake zan gaya masa babu daɗi, na ɗaga masa kai kawai. Yace, "Ayyah ai wannan ƴan sanda sun jima da yi mana maganinsa...". Bai ƙarasa ba na katse shi, "ban gane me