ana ta dakar min zuciya, ina shirin fashewa da kuka na jiyo ƙarar hayaniya a compound, tashi nayi na leƙa, su Aisha na hanga sun kewaye Inna Karima suna murnar zuwanta, tsallen murna na buga na wurgar da wayata akan gado na fice da gudu ina, "oyoyo Innah". Ina zuwa na ɗafe jikinta. "laaa kunga yarinya zata kada ni". Ta faɗa tana dafe jikin mota, Sakinta nayi ina dariya. Ita kuma ta bini da wani kallo tana taɓe baki, Kamar dai yanda na faɗa muku a baya, Inna Karima macece da Allah ya dasa mata zuciyar kushe, a hakan ma kallon da take mini tana taɓe baki neman makusa take a jikina, kai ni dai na godewa Allah da Gwaggo bata yo halinta ba, na basar kamar ban san tanayi ba, ina ƙara faɗaɗa fara'ar fuskata ina masu sannu da zuwa. Jakar hannunta na amsa, ina kallon Mardiyya a gefe sai wani shashshan ƙamshi ta ke, ko takanta banbi don ba shiri muke ba, na kalla yarinyar da suka zo tare, wanda na fahimci itane ƴar aikin da aka kawo mana, ina mata murmushi nace muje ciki ƴar ƙanwata, ina ta jin daɗi na sami abokiyar hira duk da ni bana zaman kaɗaici tunda ina da Gwaggo. Inna Karima ta yaba gidanmu sosai, ni dai hankalina na kan naji batun kwana nawa zasu yi. Ta kalla Gwaggo tace, "wai Matan gidan basa nan ne?". "suna nan mana". "amma naga babu wadda tazo ta gaida ni". "ni kaina da nake zaune da su ba gaida ni suke ba, gani dai uwar miji, basa ganina da girma wannan tarihin kin sani ba sai na ƙara ba ki ba, don haka kinga ni dai bana son magana don na san halinki, nima adu'a nake musu Allah ya shirya su". Abincin da Inna Karima keci ta tashi akai, ta fita compound tasa aka kira mata su Umma, tayi musu tatas wanda har dukanmu sai da muka ji dama bata zo ba, saboda yanda tasa Baba a gaba tana masa faɗa tana zaginsa, su kuwa kowacce haƙuri ta shiga bata don suna tsoronta, ita bata wasa kamar Gwaggo da ta ke ƴar barkwanci. Har dare Inna Karima bata bar masifa ba, Gwaggo dai bata ce mata komai ba, don dama idan tana masifa duk bakin Gwaggo mutuwa yake. mai aikinmu Iklima na kusa da ni a zaune, saboda ni bani da ƙyama, tunda suka zo nasa tayi wanka na bata kaya masu kyau ta saka, cikin lokaci kaɗan har mun fara sabawa da ita, yanzu haka ma kallo muke a wayata, Mardiyya na gefenmu tana waya da saurayinta, na bawa Iklima wayar nace taci gaba da kallon kamin na dawo. A parlo na sami Inna Karima tasa Baba gaba sai zazzage shi take akan yaƙi aurar dani, ya barmi sai kumbura nake ina jera kafaɗa da shi da matansa, ba zai aurar da ni ba sai karatun boko ya gama lalata ni tukunna, wannan kayan haushi da yawa yake. Shi dai Baba haƙuri yake bata yana kuma ƙoƙarin ganar da ita, amma kwata-kwata taƙi fahimta, har cewa ta ke da mahaifiyata nan ba zata taɓa zuba ido tana ganina a haka ba ban cika mace ba har yanzu, saboda ita tasan ƙimata kuma tana ƙaunata... "ni kuma da nake riƙonta ai kin san ba ƙaunarta nake ba". Gwaggo ta faɗa a ƙufule. "ni ba haka nake nufi ba Yaya, amma dai zuwa yanzu kam ya kamata ku gane yarinyar ta girma, kuna tare da ita amma kamar ba kwa ganinta". "yo ke da kike ganinta kuma kika gane ta gama haɓɓaka me zai hana ki aurar da ita wai, ni duk kinzo kin isheni da hayagaga baki sai warin goro yake. To ki sami damar yimin shiru tunda bake ce a gaba dani ba, da za ki sa ni a gaba kina min faɗa kamar wata uwata". Ta juya ga Baba tace, "kai Auwalu tashi ka tafi, ɗiyar albarka ce dai ba yanzu zan aurar da ita ba dan haka sai a bini da ido kawai. A jira har sai randa ta kawo min wanda yay male-male a zuciyarta tukunna". Baba ya miƙa ya fita bayan yay masu sai da safe, Gwaggo kuwa taci gaba da sababinta a yayinda Inna Karima taja baki ta tsuke, alamu dai taji haushin maganar da Gwaggo tayi mata. Gwaggo kam bata fasa maganarta ba, sai ta koma ma kamar bada Inna ta ke ba. "shi mutum bashi da shanka bare cinka amma duk yabi ya damu da zamanka a gidan ubanka. To ki faɗi kwanon shinkafarki nawa take ci sai a biyaki tunda kin gaji da ci da ita". "yo na kuma magana kice bakina na warin goro Yaya, gaskiya ce da kai ba'a son ka faɗa. Amma ita ai ba dutse bace da har zuwa yanzu zata ce ba wani abu dake tsikarinta". "yo Allah na tuba shekarun nata nawane gaba ɗaya, sha tara ne fa ta ke yanzu, girman kajin gona tayi shi yasa duk tabi ta tsone miki ido. Ga shi ita ba kazar ba ballantana kice za ki siya ki dafa kiyi mata cin yunwa, wannan luhu-luhun tsokar haka za ki ganta ki mayar da ƙwaɗayayyan yawunki". Dukansu haushin juna suke ji, Sai harar juna suke. Abin nasu yaso bani dariya, Na zauna kan kujera na ɓata fuska ina turo baki daka ganni kaga wadda ke cikin fushi. Inna Karima da baki bai mutuwa ƙara faɗa ta ke, "ji dan Allah yanda nono ya cika ƙirjin yarinya, komai yaji zamzam a halittarta amma an take gaskiya an Kama huɗubar bature. Ga sa'aninki nan a ƙauye duk sunyi aure, harda masu ƴaƴa Kin tsaya nan kina daka ta ubanki". Gwaggo dai ta taɓe baki, ni kuma na ƙara haɗe gira nace, "to wai Inna da kika damu da nawa ita Mardiyya da take jikarki mene yasa ita ba za ki sa mata ido