NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 65 of 98

ni ko da kuwa a keken guragunsa ne". tai wani zabura ta ƙara gyara zama kan tace,"au gurgu ne ma shi? Kai amma wannan anyi Fitinannan gurgu, ko da yake kunfi masu ƙafa iya shege, to ai sai ka fito sak a mutum kace mata kana barar na abinci ko na magani, sai a taimaka maka, amma ka wani fa-ke da tayi maka sata saboda rashin tsoron Allah. To na riga na gama gano ka taimako ne kake buƙata, sai kazo har gida ka roƙi Ubanta ya taimaka maka, ka daina bibiyar min ita da baƙin sharri, idan kuma ka ƙara cewa tai maka sata zanyi adu'ar kekenka ya wuntsula da kai a tsakiyar ruwa". Naji yay ƙaramar dariya, farinciki a tattare da shi yace, "Hajiya Gwaggo ai dama ni nafi so ta faɗa min inda gidan nasu yake, yanda idan iyayena ma suka zo Baba zaifi taimaka min". tana gutsurar goro tace, "aiko dai Auwalu zai taimaka maka sosai, kazo da kai da iyayen naka insha'Allahu duk wani kuka da kuka zo da shi zai share muku hawaye. Gidan ba wani wuya gare shi ba ai da kunzo...". Tunawa nayi da abinda yace min a wancan rana, Nai saurin saka hannu na rufe mata baki, duk na ruɗe nace,"Gwaggo karki faɗa masa inda gidan nan yake, wallah haka yace indai yazo sai ya faɗawa Baba na masa sata kuma ina murguɗawa manya baki". "iye". Ta faɗa tana jijjiga kai tare da cewa,"yo ai ce min za kiyi me haɗa husumiya ne shi kamar waccan shirgegiyar matar uban naki. To ɗan gurgu kana jina ba, laqad ja'akum baƙin sharrinka ya koma kanka. Kinga Sabina kashe min wannan wayar kar raina ya tugunzuma ya ɓaci nayi tattaki naje har inda yake". Na sauke mata wayar daga kunnenta ina dafe ƙirjina dake bugawa, ina jinsa kamin na kashe wayan yana roƙon Gwaggo don Allah ta masa kwatance, ni kuwa na kashe ina hararan wayar. Na lumshe ido na kwantar da kaina bisa pillow ina kallon sama, ina jin wayata na ringing naƙi ɗagawa, saboda nasan shine, sai dana ji ƙarar shigowan text tukunna na miƙa hannuna na ɗauka, na buɗe ina karantawa. _Please Beauty help me pick my call, na rantse za kisa naje na yiwa Mom kukan dana jima ban mata ba. My eyes are desperate to see your beautifull face, ba zan iya juriyan har sai an koma school kamin na kuma ganinki ba, i can't bear it anymore, dole sai kin biyani satar da kika mani zan ƙyaleki._ Ina gama karantawa na taɓe baki, na kuma murguɗawa saƙon nasa baki shima. Na jefar da wayar gefe na mayar da murfin idona na rufe, ina jin Gwaggo na min magana nai mata shiru. Gaba ɗaya tunanina da ɗokina ya tafi akan naje kano naga Yayana, idanuwana can see nothing fa-ce fuskarsa, haka zalika my ears can hear nothing but the sound of his golden voice wanda yake iri guda dana Proff, da ace zanje Kano na rasa Yayana tabbas zan dawo na kama Proff nace shine, saboda ban manta da wani kallo da Proff yayi min ba a wancan rana, sak kallon da Yayana yay min a ranar da nake bashi abinci a baki. Naja doguwar ajiyar zuciya na sauke, na miƙa hannu zan jawo pillow na rungume naji an ɗala min duka a bayan hannu, a zabure na miƙe naga Gwaggo na wurgan harara, na bo-ne fuska ina turo baki gaba sai fama ƙifta idanu nake. Yau rana ta farko da tace da ni, "mutum sai shegen turo baki gaba kamar shantu...in har ba ki daina wannan mugun abun da kowa ke ƙorafi akansa ba wataran sai jaɓa tayi miki kiss". na tuntsire da dariya sosai. nan ta kuma hau bambamin bata son wannan ƴr iskar dariya, Allah kuma ya rabani da sababinta a sanda ta jiyo motsi a parlo, ta fita da sauri tana faɗin,"ga Aliyu can ya shigo yi min ta'adi da sanyin asuba, yo ta'adi ai sata ne. wannan yaro dai da gani Unguwar Zoma bata gasa shi da kyau ba". [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(21)* Bayan Kwana biyu, Zaune nake kan plastic chair a balcony dake upstairs namu, ina karanta wani haɗaɗɗan novel mai ɗauƙe da wata iriyar soyayya mai burgewa, da kuma sawa kaji kana buƙatar kasancewa da saurayinka a lokacin, banma san sunan littafin ba sai da shafin ya yanke min, da sauri nayi scrolling back na duba sunan novel ɗin. *ƘADDARA TA RIGA FATA* naga an rubuta daga haziƙar marubuciyar nan mai suna Anty Nice, cikin sauri na Kunna da ta na buƙaci da a turo min sauran, babu ɓata lokaci kuwa sai ga Oum Ramadhan ta turo mani, godiya nayi mata sosai sannan na kashe datan naci gaba da karatuna, ban ɗau wani lokaci ba na kammala karanta shi, Soyayyan Hummy da Dr ta ƙayatar da ni, sosai littafin yayi daɗi ya kuma faɗakar, ba ƙaramin jinjinawa marubuciyar nayi ba. Daga nan kuma na ɗora da littafin Al'amari, tunda naci karo da page ɗin da ake zayyano kamannin Hammah Saddam na fara shiga wani yanayi, Gaba ɗaya yanayin kamannisa da ake lissafawa sai yake min kama da Yayana, Banbancin su ɗaya Yayana yafishi haske sosai, wani sanyayyan murmushi na sa ki ina ƙara gyara zaman karatuna, Saurin lumshe ido nayi a lokacin da nayi katari da wurin da Hammah Saddam ke nunawa Tasleem ɗinsa tsantsar so, Na jinginar da kaina bisa kujera ina daɗa lumshe ido ina ƙiyasto ni da Yayana. Ta ke kuma naji ruwan hawaye na cika min ido, kewar Yay
🏠