NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 64 of 98

yo ai nasan kwanan zancen, dama na faɗa ne kawai don naga hankalinku kuma sai gashi nagani. To ku babu ma mai zuwa ita da Abba kawai ya isa su tafi su lafiya insha'Allah, ato ni na gama magana kunga tafiyata”. Tana rufe magana bata jira cewar Baba da kowa ba ta ja hannuna muka bar wurin. Baba yayi ƴar dariya yace, “ni zan fita babu mai magana?”. Baba ya tambaya da buƙatar amsa. Shiru suka yi, alamu ya bashi babu mai magana suka yi mashi fatan alkhairi ya fita. Bayan komawar mu ɗaki kuwa Gwaggo ta shiga haɗa min kayana da duk wani abin buƙata ta kuma jaddada mani akan na riƙe azkar sosai kar nayi wasa da shi, ta kuma haɗa min magungunan da zan riƙa sha ina shafawa, duk da tasan bai yiwu lallai nayi amfani da shi ba. Na dubi Gwaggo nace, “naga Gwaggo sai haɗa kaya kike, kuma naga ba yau ne tafiyan ba sai gobe”. “yo ke banda ke da abinki, ai saboda karki manta wani abin, nifa idan zanyi tafiya tun ya rage sati nake kimtsa komi nawa, saboda gudun mantuwa, bare kuma Sahibina Allah sarki, Allah ka jaddada Rahma a gare shi". da Amin na amsa mata bayan na samu wuri na zauna. Gwaggo ta ɗakko wancan ta ɗakko wannan duk tana yi min bayanin wanda zan bama idan Allah yayi tafiyan nawa gobe. *Ɗaya Ɓangaren.* Kwance yake a makeken gadonsa, mai kyau da tsari, kayan alatu sun wadatu a ɗakin babu ƙarya, alaƙalami ba zai iya bayanin yadda ɗakin ya wadatu da tsaruwa ba sai ido in ya kalla. Sallama tayi fuskar ta ɗauke da murmushi. Ta samu gefe guda kan kujera a kusa da gadon ta zauna kana tace, “Bro barka da hutawa”. ɗan juyo da fuskarsa yayi gareta kana ya motsa bakin shi tamkar baya son magana fuskar shi babu yabo babu fallasa yace, “Barka dai Sis, dafatan an samu biyan buƙata ko?”. “umm an samu, amma sai an bani tukuici zan bayar don Mom haka tace”. ɗan murmushi yayi kafin ya furta,“me kike buƙata ki faɗi min, duk da nasan kinfi ƙarfin komi a wuri na, but tell me um”. “to shikenan, na yafe sai dai nayi fatan asha soyayya lafiya yasa kuma ita ne Aunty’nmu”. Amin ya amsa da shi kafin yace, “duk kinsa ni ƙaguwa, kin gagara bani na gani”. Ƴar ƙaramar takarda ta miƙa mashi, ya ɗakko wayan shi yayi dialing number, da ike yana Amfani da true caller a ta ke sunan ta ya bayyana, ba shiri wani ƙayatatcen murmushi ya samu muhalli a fuskarsa. “bari naje wurin Mom kafin nan ka gama”. da to ya amsata sannan ta fice a ɗakin. Sau biyu yana kira bata ɗauka ba sai ana uku ya yi sa’a ta ɗaga tare da yin sallama, sallamar da tayi barazar ɗauke numfashinsa cancakas, da gaggawa tare da nasarar ubangiji ya samu ya dawo gareta ya amsata yana faɗin. “Ina fatan ban katse ma Beauty baccin da ta ke mai cike da farin cikin ganina a cikinsa ba”. Jin kalmar Beauty yasa tuni na gano wanda ke magana, hakan yasa nace,“Barka da Safiya Sir, ina kwana, na tashi a bacci tun ɗazu, yasu Mom?”. “Masha Allah, Mom tana lafiya. How was your nyt?". "Alhmdl Sir". Na faɗa ina jin wani yanayi na jin nauyi a tare da ni. wucewar wasu sakanni na katse shirun daya ratsa nace,"amma Sir where do you got my number?". Murmushi naji yayi, bai kuma ce komai ba. Na kuma cewa, "Sir ina tambayanka ne fa, answer me please". murya a ɗan murɗe yace,"Do you think I will let you go without paying me for what you stole from me. Abune fa mai muhimmanci kika sace min, so I have to find you wherever you are, even if it's not on the phone. Ko da kuwa zan murɗa keke nane naje har birnin sin". Gabana ne ya buga ras, naji kamar an karza min magogin kaushi, tuni idona ya ciko, muryana a raunane nace,“nifa wallah ban maka sata ba, kuma ma naga nace ka faɗi min ko nawa ne Allah zan biyaka, amma ka daina cewa nayi maka sata, har ga Allah bana so ake dangantani da wannan kalmar”. ba tare da na bashi damar magana ba na karawa Gwaggo wayar a kunne ina faɗin,“Gwaggo ki sanar da shi ban taɓa sata ba, ya daina cewa na masa sata...". "shine muna malamin da yace kin masa sata?".Ta tambaye ni tana dafa katifa ta miƙe daga kwancen da ta ke. Kamin na bata amsa yace, "Gwaggo ina kwana". Naji ya faɗa cike da girmamawa. Gwaggo ta ƙura min ido, na ɗaga mata kaina alamar ehh, tayi gyaran murya sannan tace da shi,"Kai kuwa bawan Allah tsakani da Allah haka ake rayuwa, haka kawai saboda ɗaukar alhaki kace ɗiyar albarka tayi maka sata, to gaskiya ka sauya hali saboda wannan ba halin ƙwarai bane. Ni Ƴar jikalle tah ko tsinke bata taɓa sata ba, atoh sai kaje can ka nemi wanda yayi maka sata, idan ba haka ba hukuma ce zata raba ni da kai, ba zan lamunci ganin ka ɓatan sunan Jika ba, a hakan ma ƙazafin da kayi mata kaje kai da Allah, yo wannan ai kai fitinannen bawa ne". Daga inda Muhsin yake yay dariya mara sauti, yanzu ya gane Gwaggo Kakata ce ba mahaifiyata ba, ya buɗi baki zai magana Gwaggo ta tari numfashinsa da faɗin,"yo tsaya yanzu mene na kiranta a waya ma, ko wani sharrin zaka kuma ƙulla mata?". Nayi caraf nace, "Gwaggo haka fa yace ba zai taɓa barina ba duk inda na shiga, dole ne sai ya nemo
🏠