kin girmamawa yake min magana yace, "duk abinda ke wakana ta nan oga yana gani ta cikin CC, kuma idan har na saɓa umarnin shi zan iya rasa aikina ta dalilin hakan saboda yace ke ɗin mai muhimmanci ce, ki taimaka min wannan aikin da shi na dogara nake ciyar da iyalina". Abun ya ɗaure min kai, na ɗaga ido ina kallon CC camera ɗin dake hasko mu, to wane shi ɗin? na sauke ajiyar zuciya na ƙarasa wurin ATM machine ɗin saboda karna ɓatawa jama'ar wurin lokaci, na ciri kuɗina na bar wurin, zan fita a gate maroon ɗin mota ƙirar accord sabuwa fil tasha gabana, ina jiran ta wuce sai driver ɗin ya fito ya buɗe bayan motar yace na shiga. Wani duba na tsaya ina yi masa, a yayin da duka idanun mutane ya dawo kaina, banyi maganar da zanyi ba ya miƙo min waya yace ana magana. "wa...?". Ban ƙarasa tambayar ba Kawai naji an ɗora min wayar a kunne, na waigo don ganin waye haka, mace na gani da black skirt with white longslip a jikinta kuma ba musulma bace, da alama itama security ce, ni dai mamaki duk ya baibayeni, ta cikin wayar naji yana cewa,"don Allah Beauty ki shiga motar ya sauke ki a gida, bana so kina tafiya wani halittar ɗa namiji na kallonki, bana son gardama". Yay maganar cikin sigar roƙo. laɓɓana suka haɗe wajen furta, "kana school kana nan, to kai ɗin wane? Kuma nazo kasa anyiwa mutane rashin adalci, sunyi sammako sunzo wuri suna jira, ni kuma da ban haura rabin awa da zuwa ba nayi na gama, hakan da kayi adalci kenan matsayinka na shugaba? Ni ɗin nafi kowa ne?". Ajiyar zuciya naji ya sauke, muryansa a hankali yace, "idan har akanki ne to a wurina nayi babban adalci, babu ta yanda za'ayi ina da iko a wuri kuma na barki da shan wahala. Yanzu awajen nan idon kowanne banzan namiji akanki yake, ki taimaka ki shiga mota ku tafi, idan kin ƙarasa gida za muyi waya". Maganar ya ƙarasa min ita yana ɗan ɗaga murya. "Beauty". Ya katse min shirun da nayi. "mene kuma? Nifa babu motar da zan shiga, ai da zanzo bada taimakonka nazo ba, kuma Gwaggon bata bani wannan tarbiyar ba". Nace da shi. Sai naji ya fitar da iska daga bakinsa, "da ace ina da lafiyar takawa da nazo da kaina na kama hannunki na tilasta miki, sai dai bani da damar hakan". Na taɓe baki, kiran wayar Yaya Haidar ya shigo wayata, na ɗaga yace, "Malama kina tsayuwar mene anan da ba za ki fito ba, ko zanyi ta zaman jiranki ne?". murya a kumbure nace, "to ni nasan kana nan ne, kuma ai naga bance kazo ɗaukana ba". banma ƙarasa faɗar abinda zan faɗa ba ya kashe wayar. nayi nazarin ƙwamma na fita na bishi, wannan proff ɗin na gane yana min wayo ne so yake na yaga gidanmu. Don haka na raɓa deiver'n dake tsaye gabana na fice da sauri, Yaya Haidar na ƙoƙarin kunna motar na buɗe na shiga, ko magana baiyi min ba bare kallona. Nace da shi, "Yaya Haidar wai zaman jirana kayi ko kuma dawowa ɗaukana kayi?". Kansa na kan tuƙin da yake yace, "ko hakan bai maki bane na saukeki?". "a'a kawai dai dama na tambayeka ne". Haka na dinƙa masa hira yana amsa min jefi-jefi har muka iso gida, ina kallon wayana na ringing ban ɗauka ba tunda na lura numban proff ne a jiki.
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(19)*
Washe gari da safe bayan mun karya ina ɗaki muna waya da Farhana ina faɗa mata zanzo kano ba ƙaramin daɗi taji ba, Gwaggo ta shigo ta samu gefe ta zauna tana jiranmu gama wayar, kuma da alamun fuskarta tana so tai magana dani ne, Amma sam babu alamun zamu ƙare wayar, da ta gaji da jira tace. “yau naga ikon ubangiji, yo sai kice min Gwaggo tashi ki fita ba yanzu zan gama wayar nan ba”. Ina jin haka nace da Farhana. “ga Gwaggo ku gaisa”. Washe baki tayi kana ta ke faɗin,“ahh haka za ki ce min Farhana ce mutan kano”. Farhana ta gaishe da Gwaggo ta amsa mata, Gwaggo tace,“Farhana ki gaisar min da Hajiyarki sosai da sosai, insha'Allah idan na shigo kano zanzo har gida mu gaisa, eh kifa gaishe ta don nasan halinki sarai kamar yadda nasan na ƙawarki ato”. Ni dai karɓa nayi ina dariya Gwaggo tace nayi na gama Baba yana jirana. Jin haka yasa na katse kiran duk da ina son tambayar Farhana ya Yayana yake, kamar wadda na bata ajiyarsa, amma ban samu damar hakan ba, saboda Gwaggo ta kafa ta tsare. Ina fita na iske su Gwaggo da sauran matan gida duk a parlo ni ɗaya ne babu, gefe guda na samu inda Gwaggo ta ke bayan na gaisar dasu Baba da sauran Matan gida da Yaya Abba. Ko kallon inda Yaya Haidar yake banyi ba, Gwaggo ce kawai ta lura da haka. Gwaggo tace, “yauwa dama ba komi bane, Sabina ce zata je ganin dangin ta shi ne nace barin sanar daku, har tafiya ta tashi ace bamu sanar ba, ato idan damai sha’awar zuwa shima sai yaje yaga nasa dangin”. Gwaggo tana rufe baki Umma tace, “ah ai kuwa ba za’a rasa masu zuwa ba, su Zainab ma zasu je dama suna son zuwa dama ce basu samu ba”. Baba yace, “sunyi hutu ne?”. ɗan sosa ƙeya Umma tayi kafin tace, “ai wai da naga Gwaggo ce tace idan damai sha’awar zuwa shisa na faɗa haka”. Gwaggo tace, “ai sanin asali shisa kare yaci alli,