NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 62 of 98

dannan sai ka saketa ta koma gidan koko da wainar gero". Ya buɗe baki zai ƙara bata haƙuri sai kuma yay shiru. Ya kuma kalleni yace, "ke acikinsu wace ta gaya miki haka?". "Anty". Nace da shi. Wani kallo yay min wanda na lura da alamar bai yarda da maganar ba, domin baya taɓa yarda da laifinta. Na miƙe ina gyara ratayen jakata nace, "Gwaggo zan tafi". "kin bari sai gobe ko kuwa?". ta faɗa tana min wani kallo. Na zumɓuri baki ina kallon Yaya Haidar da shima ya ɗago a lokacin yana kallona. Baba har zai wuce kuma sai ya dakata da faɗin, "Gwaggo ina ce na hanaki shara, me tsintsiya keyi a hannunki da safiyar nan?". ya faɗa yana ƙoƙarin ƙarɓar tsintsiyar hannunta. tace da shi, "ban son shishshigi da ƙwala kai a faranti, bada tsintsiyar hannuna zaka ji ba da wannan abin zaka ji". ta faɗa tana nuna masa Yaya Haidar dake kusa da ita. kamin ta ɗora da faɗin,"Tun ɗazu nake fama da yaron nan akan ya ajiye Sabina a banki, yaƙi ya tsaya sai karta min maganganun banza yake, ka san jinsa yake kamar sa'nni muke". Kamin Baba yay magana da sauri Yaya Haidar ya kalleni yace,"kin fasa tafiyar ne?". Yay maganar kamar bashi ba, ni kuwa nayi kamar ban jisa ba, na ɗauke kai gefe ina hare-hare, shima kuma sai hararata yake ta ƙasan ido. Baba yace, "ita ina motar tata?". nayi saurin cewa, "Baba ciwo fa naji a ƙafana, bazan iya driving ɗin ba nace ya kaini don Allah tunda Yaya Abba baya nan, shine yace aishi ba driver bane, naje na hau napep, har Gwaggo ma sai da tayi masa magana yace shi ba zai ɗau mara kunya ba". Ina yin shiru shima yace, "Baba ƙarya ta ke yi babu wani ciwo da taji, Gwaggo tazo ta samemu ne muna maganan zanje na sayo petrol a zuba mata a motan nata tunda ni ina sauri ne". Gwaggo ta riƙe haɓa tana faɗin, "iko sai lillahi, au yau kuma ni zaka ƙaryata Aliyu, yau naga makirci a wurin ɗa namiji. To Auwalu ai ka gani da idonka, shi da Abba don suyi min rashin kunya su ƙaryata ni wannan ba komai bane a wurinsu, yau gashi harda su kissa. wannan yara dai ai albasa batayi halin ruwa ba musamman Aliyu, dan ba haka uwarka da ubanka suke ba, Allah zai kawo Sulaimanu gidan nan zanji idan shine ya ɗaure maka gindin yimin fitsara". ta numfasa da ƙara cewar, "to koma menene dai kaje dan kanka. ni ba wannan ne buƙatata ba, kawai Auwalu kace ya ɗauketa ya kaita inda ta ke son zuwa, ya jira har sai ta gama kana ya dawo da ita, don na tabbata maka babu inda za shi bacin shegen yawonsa da ba ƙararre bane". Baba ya dube shi yace, "wurin aiki zaka ne?...". Gwaggo tai saurin cewa,"ai kaji tsiya, shi har ƴaƴansa ma tsoronsu yake, kai da zaka balbale shi kamar wuta amma kana masa magana a ruwan sanyi". Baba baice mata komai ba, Yaya Haidar yace masa, "ehh Baba amma ai har zan iya ajiyeta, tunda ban makara ba". Baba ya dube ni yace, "ke mene ma za ki yo a Bank ɗin da wannan safiyar? Idan kuɗi za ki amfani dasu ba saina ranta miki ba, ko kuma kije wurin Anty'nku ta ba ki aro". Na zaro ido ina faɗin, "tabɗi, wannan matar ce zata ara min kuɗi, zanko mutu babu kuɗi a hannuna". Baba ya galla min harara, Gwaggo ta gyaɗa kai tace, "ah to gaya masa dai, ita wannan munafukar ɓoyen gani yake kamar ƙaunarki ta ke". Baba ya girgiza kai kawai ya wuce. Yaya Haidar kuma yace, "kizo mu tafi".ya faɗa yana shiga mota. Na zagaya na shiga ya tada motar muka tafi. ba ƙaramin da nasanin biyoshi nayi ba, fitowar da muka yi tun tara sai sha biyu ya kawoni bank, sai daya gama zagaye-zagayensa tukunna, kuma duk saboda ya ɓata min rai yayi hakan. Ni kuwa ko parking bai ƙarasa yi ba na buɗe motar na fice, ko da na isa layi ne maƙil a wurin, kamar zan koma kawai na haƙura, sai dana shafe awa guda kamin azo kaina, ranar waje duk ta gama zane min jiki. Haka na shiga cikin bank ɗin, nan ma wani layin ne na musammman a wajen customer care, shima mutanen dake gabana sunfi goma sha biyar, na durƙusa ina danna wayata. "who is Sabina?". Naji one of the customer ɗin na magana. Na miƙe tsaye ina ce masa gani, "come to the front". Yace da ni. na ƙarasa gabansa security ɗin wurin na biye da ni a bayana, aka ja min kujera na zauna akai, security ɗin yaywa na bayana tsawa akan duk su ja baya, na faɗi complain ɗina, in few minutes aka kammala min komai, nayi masa godiya yace babu komai Madam. Haka na fito daga wajen customer care, securities na biye da ni baya da gefe, ni dai abin na ta bani tsoro da mamaki, mutane kuwa kowa kallona yake, wasu na raya ko sata nayi wasu kuma na tunanin wacce mai babbar matsayin ce wannan. ATM machine na wuce shima na tsaya bin layi, ina tsaye nan sai ga wani security na daban yazo yace kowa ya bar kan layi yay baya, duk mutane na ta jan tsaki sukayi baya, sai naji yace da ni nazo na cira, abin sai ya bani mamaki, haka a ciki ma aka mani kamar wata ƴar mai faɗa a ji a nigeria. Hayaniya ta kaure tsakanin mutane kan ba'ayi musu adalci ba in har akayi haka, sai na duba security ɗin nace karka damu zan jira har layi yazo kaina. Duk da cewan dattijo ne amma haka yake rissina min, kuma ci
🏠