NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 61 of 98

sai kice bana ganin girmanki, shi yasa idan kina magana nake miki shiru. Kuma shi Baban daya saya min motar ai ba cewa yayi gata nan ka zama driver'n Sabina ba. And again motana bata ɗaukan marar kunya ne". "idan bata ɗauka mara kunya ba ai ta ɗauka fitsararru". Gwaggo ta sa ki wani guntun murmushi kamin tayi ƙwafa tace, "hmmm ina jiye maka ranar ƙin dillanci. Ina roƙon Allah kar ya jarabce ka da son wannan yarinyar kayi tunanin zan baka ita Aliyu, ko da zanga ledar jini gefe, ledar ruwa gefe babu zancen mallaka maka Sabina, atoh ka jini da kyau". "nima kar Allah ya nuna min wannan ranar, dan babu abinda zanyi da wannan mummunar jikar taki. Da za ki ce mata ma ta daina kwalliya idan zata fita may be ta ke yin samari, wannan kwalliyar babu abinda ke ƙara mata sai girman ƙwailancinta, ƙwaila kamarta ace babu mai so, ki miƙe tsaye ki samu ki haɗata ta farfaɗo don tayi tsala da yawa". "akwai babban tsala ma irinka, kai wacce asararriyar macen ma zata iya aurenka, cikakkiyar mace dai cewa zata yi baka girma ba, tunda gaba ɗayanka yaushe ne ma aka cire maka shayi". Wani shu'umin murmushi naga yanayi yana cizon leɓe, yayi ƙwafa murya can ƙasa yace, "to Gwaggo koma wace a bamu ɗaki ɗaya da ita a jira wata tara a gani. Anan za'a tantance darajar kaciyar tawa". ni kaina kalmarsa ta ƙarshe ba kaɗan ɗin kunya ta bani ba. Gwaggo kam sheƙeƙe tayi tana kallonsa kafin tace,"kai dama ai ba kunya gareka ba, Allah dai ya shiryeka idan na shiryuwa ne, idan kuma bana shiryuwa bane yay mana maganinka". Murmushi kawai yay mata baice komai ba, yasa key ya buɗe motar, tana dubana tace, "to ki taso ku tafi". Yay saurin waigowa ya kalleni ya kalleta, "ni fa babu yarinyar da zata shigar min mota, tunma wannan jikar taki mara kunya. Yarinyar da gaba ɗaya kayan jikinta suka girma a gabanka amma ji take kamar ita ta baka nono". kawai saina Durƙushe a wajan na fashe da kuka, idan da kalmar dana tsana naji yana cewa na girma gabansa, ranar nan haka yace min tun twins ɗina na ƙifil-ƙifil ya sansu amma saboda yanzu sun cika min ƙirji shine nake ganinmu kai guda da shi. masifa naji Gwaggo na masa na ɗago ina dukan ƙafa a ƙasa ina ƙara sautin kukana. "ni dai Gwaggo Allah na gaji da ganin Yaya Haidar da Anty a gidan nan, duk su biyun sun tsaneni". "ita kuma guntuwar me tayi miki?". "ɗazu itama fa daga nace ta rage min hanya take cewa ba zata yayibi mai aljanu ba...". Ban ƙarasa ba ta tareni da cewar, "ita Guntuwar ta gaya miki wannan kalmar mai ɗacin saurare?". Na ɗaga kaina ina ƙara cewa, "kuma ai duk ke kika jawo min koma wacce magana ce, ina zaman zamana kin tashi kina yaɗawa mutane wai ina da aljanu". Jikinta naga yay sanyi, sai kuma ta duba Yaya Haidar tace, "kira min Auwalu a waya kace yazo ya sameni cikin gaggawa, ke kuma tashi muje ciki". Ta ƙarasa maganar tana dubana. Na miƙe zan bita sai ga Baba ya ƙaraso wurin, ta zuba masa ido tana faɗin, "yauwa Ashe kana cikin gidan?". "ehh inan ban fita ba. Daga wurinki nake naga duk baku nan, ina fitowa kuma na hangoku anan". Ta shiga goge hawaye, a cikin muryar ƙonewar zuciya take faɗa masa. "yanzu tsakani da Allah abinda matanka suke a cikin gidan nan suna kyautawa, kwata-kwata basu san hakkin maraya ba, kai kuma gaka sun gama shanyeka babu abinda kake iya tsinanawa, ni kuma gaba ɗaya baka tausayina, nasha wuyar kishiyoyi zan kuma sha ta matanka, to wannan a baya ne akayi baza a kuma ba. Babu shegiyar da zan zubawa ido acikin gidan nan tana cin zarafin marayun yaran nan, wanda suka yi a baya ma su da Allah. Ƴar nan ko ɗumin hannun uwarta bata ji ba da ta zo duniya amma hakan baisa aji tausayinta ba, Yanzu har ta kai da su dinƙa goranta mata akan tana da aljanu, to ita ta ɗorawa kanta ne? shi dai ciwon nan bai wuce kan uban kowa ba, to Kaja musu kunne su shiga hankalinsu da taɓa yarinyar nan idan ba haka ba kuma billahillazi zan ajiye sanyin da nayi a gefe na zazzage musu buhun rashin mutunci, na zama kalar uwar mijin da ba'a so. Wannan ƙiyayya da ake nuna mata haka tun ina da rai, to randa babu ni kuma fa? to ni wallahi da a taɓa min Sabina ƙwamma a fito fili ace min Hannatu na tsaneki, in yaso ayimin zagin ƙare dangi zanfi jin daɗin hakan, ɓacin ranta yana damuna haka kukanta yana ɗaga min hankali, ka gayawa wannan guntuwar karta ƙara yin abunda tayi saboda hukuncin da zan ɗauka akanta ba zaiyi mata daɗi ba". Baba dake tsaye yana sauraronta ya ɗago ya kalleta yace, "ni dai don Allah Gwaggo ki bar wannan kukan bana so, ki kuma yi haƙuri zanyi musu faɗa hakan ba zai kuma faruwa ba". "karka kuma bani haƙuri akan laifin matanka domin cutata kake, kai da ubanka marigayi babu abinda kuka iya idan an cuce ni sai bani haƙuri, to ni wannan mugun kalmar na gaji da jinta, tun ina zaman gidanka wancan Zamanin na zaman Halima da Hajara kake zaluntata da wannan kalmar, karka ƙara idan ba haka nayi maka irin yanda nama Sulaimanu. Maganar ƙarshe da zanyi wallahi wallahi kaji na rantse ko, duk ƴar wofin da ta kuma shiga harkar Sabina a gi
🏠