kumbura suntum ɗayar kuma ta ɗan sace ba kamar da ba. ya ƙara maimaita kalmar innalillahi a cikin ransa, ko daya miƙe tsaye, ko da yace zai gudu, la shakka babu inda zai kai ga ɗora ƙafarsa zasu cimma masa, da ƙyar ya takawa, irin takun da ko kusa ko kaɗan ba zai iya yin gudu ba. maimaituwar kalmar innalillahi a bakinsa ta haɗe da damƙwar kwalarsa da ɗan sanda yayi, ya fizgo shi ya miƙe tsaye, sannan ɗayan ɗan sandan daya ƙaraso shi da wasu mutane ukun da bai sansu ba ya kama hannunsa ya saka masa ankwa. sannan suka tasa ƙeyarsa zuwa cikin mota suka tafi. _"gani nan Yaya. Yaya gani nan, karka bari ƙwallar ta zubo dan Allah"._ maganar daya ji na shiga kunnensa kenan, muryar Sabina ce, daga ina?, tana ina?, ya rumtse ido da ƙarfi ya kuma buɗesu, acikin motar dai yake, cikin motar dai daya ji ana faɗar direct gidan gyara hali za'a kai shi. bai san lokacin daya daki kansa da jikin motar ba, inda tasan abunda ta ke haifar masa, da ta hana ganinta da jinta suna yi masa gizo, da ta hana sunanta ambatuwa acikin zuciyarsa. kuma buguwar da yay a wannan lokacin shi yay sanadiyar ɓallewar jini daga kansa, saukar jinin da yay sanadiyar tsayar komai acikin kansa, ya daina ji da ganin komai.
*Abuja.*
"haka za ki fita ba ki ci komai ba?".
"ina tsoron layi ne shiyasa, idan naje can ɗin na sami resturant a kusa saina saya na ci". "hakan yayi, a dawo lafiya. Idan kinga mutane ba sauƙi a wurin ki dawo ya ba ki kuɗi a hannu kawai saiki amfani da shi". "ameen..tom Gwaggo". Na amsa ina gyara yafa mayafina. Da sauri na fito compound, ina zuwa na tarar motana babu mai, na daki kai ina jan tsaki, ni yanzu ya zanyi? Shine tambayar da nayi ma kaina, ga Yaya Abba baya nan, ni kuma bana son kula Yaya Haidar bare nace ya ara min tasa, to ya zanyi dole haka zan haƙura neje wurin nasa tunda dai babu wata motar a ajiye sai ta matan gidan, su kuwa ba shiri muke ba bare nace zan ari tasu, shi yasa nacewa Baba a ɗaukar mana driver a aje, yace a'a baida amfani tunda dai kowa ya iya motar nan kuma ga Yaya Abba da Yaya Haidar ma. Har na nufi part ɗin su Yaya Haidar na hango Anty na shirin fita, na dawo da sauri na ƙarasa wurinta lokacin harma ta shiga mota tana ƙoƙarin fita, na tsayar da ita, ta zage glass tana jiran cewata sai faman haɗe rai ta ke tana min gani-gani. cikin ƴar murya nace,"Anty please bari na biki ki ajeni a bank, motana babu mai aciki, jiya su Yaya sunyi tafiya ina tunanin basu san ya ƙare ba basu tsaya sunsha ba, idan nace zan bari aje a sayo zan ƙara yin late". Nace da ita ina maganar da sigar roƙo na lallami. "tunda ubanki ya saya min motar ai dole ne na zame miki driver, to ko na rasa abar ɗauka a motana bana yayibi mai aljanu ba na kwasarwa kaina matsala". Ta faɗi hakan tana ɗauke kanta akaina taja motar ta fice a gidan. Oh ni Sabina, yanzu har ta kai ake min gorin mai aljanu, na goge guntun hawayen daya sakkomin, _Allah ka yaye min da ni da sauran ƴan'uwana ba ki ɗaya._ nayi adu'an a zuciyana ina nufar hanyar gate, saboda na san idan na koma Gwaggo cewa zata yi na fasa zuwa, ni kuma nafi so nayi abuna yau na huta, don akwai terming ɗin da nayi. Har na kai gate zan buɗe ƙofa na jiyo Gwaggo na ƙwala min kira, na juyo na ganta tsaye tana jan kwandon shara, ko ina zata da shi oho, rigima dai irin tata kawai, Baba yace su Zainab suna zuwa suna mata aiki tace bata son marasa mutunci suke zuwar mata inda take, Inna Karima zata kawo mata mai aiki. daga inda ta ke tsayen tace, "idan kin gama ƙare min kallon, nace har yanzu ba ki tafi ba dama?". "ummm motan nawa ne babu mai, zanje na hau ta haya sai na tafi". "to zuwan yau dama dole ne ko ƙaƙa?". ina ɗan marairaice fuska nace, "nafi so ne nayi yau ɗin, please Gwaggo ki barni na tafi". Ina kallo ta taɓe baki, "wai please, dole dai idan za'a maka magana sai an haɗa da ɗan iskan yaran da ba jinsa kake ba, yare bana uwa ba bana uba ba, shegen bature duk ya lalatawa ƴaƴan musulmi harshe, banda kece ma da sai nace zagi na akai". Ina nesa da ita banji mai tace ba, na juya zan tafiyata tace, "riga Malam masallaci ai ban gama maganar da ke ba, ina Abba ko wannan yaron Haidar?". Tana rufe baki Yaya Haidar na fitowa daga ɓangarenta, yana gyara maɓallin hannun rigarsa fuska a haɗe yace, "ni fa ba yaro bane karki kuma ce min yaro". "to ubana". Tace da shi tana hararsa. Sai kuma tayi masa kallon tsab kamin tace, "fita zaka yi ne?". "umm". Yace da ita yana tafiya. "yauwa to ga Sabina nan zata je banki, sai ka ajeta a can motarta ce babu mai". "ni ba driver bane, taje ta nemi nepep ta hau mana". Tace da shi, "yanzu Haidar ni zance kayi abu kai tsaye kace min ba zaka yi ba saboda banda girma a idanunka. Wannan yarinyar fa ƙanwarka ce, me yasa kake nuna mata tsana da yawa har haka ne, idan baka ɗauketa ba ai kaje ka ɗauki wata ƙatuwar banza. Kuma motar nan dai naga ai Babanta ne ya saya maka ita, amma saboda kai mutunci bai gama ratsa jininka ba shine zaka ce ba zaka kaita inda take so ba". cikin jin haushi yace da ita,"da nayi magana