NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 6 of 98

n yanda ta ke banka masa wata uwar harara. na san yaji rashin daɗin abinda tace, amma gani nake kamar nafi shi rashin jin daɗin hakan. "haba don Allah Farhana, ya za ki dinga aibata ɗan'uwanki musulmi da irin waɗannan kalmomi marasa daɗi, bayan ba ki da masaniyar komai a kansa. Ki tuna fa addininmu ya yi hani da tozarta musulmi". "hmmm! lallai har yanzu ba ki da wayo Sabina, kuma indai za ki ci gaba da biyewa wannan zuciyar taki zata kaiki ta baroki akan saurin taimako da kuma tausayi. kuma ina mai gaya miki tun wuri ki bar wannan ɗan shaye-shayen kizo mu tafi, don wallahi irinsu ne tantiran ƴan iskan nan masu lalata ƴaƴan mutane, waɗanda bakin uwa ya gama binsu". maganarta ta ƙarshe tai wani dukan ganga a zuciyar Alhussain, dan haka yay saurin rumtse ido da gaggawa ko ya sami sassaucin raɗadin da maganarta ta haifar masa. yau rana ɗaya kuma rana ta farko da aka taɓa faɗa masa kalma mafi muni da ɗaci a rayuwarsa. lalata! bakin uwa!, to shi da bai taɓa ma yin gaba da gaba da wata ƴa mace ba ta ina zai lalatata? wama ke raɓarsa daga maza har Mata? Babu! Shi ɗaya ne a rayuwarsa, kuma bashi da iyaye balle yace yana da uwar da bakinta yabi shi...amma sai gashi yau har ana kiransa da ɗan daba, zai iya rantsewa a iya tsayin rayuwarsa baya tunanin ya taɓa riƙe wuƙa ko makami, yaji yana shan wiwi amma baya taɓa ɗarawa daga kanta, itan ma dan ya kanji sauƙi ne idan yasha...sai gashi yau ƙanƙanuwar yarinya na gaya masa son ranta ba tare da ta san shi ɗin waye ba kamar yanda shima bai san kowaye ba. ƙwayar idonsa tai masa nauyi kamar an baɗa masa ƙasa a ciki, buɗe su yayi da matsananciyar damuwa gami da ɓacin rai, bai da ikon yi ma ta komai saboda ya cancanci a faɗa masa dukkan wasu kalmomi masu muni. idonsa yana bin Farhana da kallo da saƙa wasu abubuwa cikin ransa, yana jin tsakin da ta ke taja acikin kansa. sai ya cire hannunsa daga nawa, na dube shi da rashin jin daɗin abinda Farhana tai, tausayinsa naji ya daɗa kamani, ko da wannan ɗaga ƙafar kaɗai da yayi mata zan iya shaida na rantse yana cikin wannan halinne kawai dan bashi da yanda iya, amma ba da son ransa ba. Muryarta a sanyaye nace da shi, "don Allah Yaya kayi haƙuri da abinda ƙawata tayi maka, rashin fahimta ne ya janyo hakan, amma a madadinta ina mai baka haƙuri, na san kowane aka yi masa ba zai ji daɗi ba, karda ka sanya ɓacin ran hakan a ranka ya kuma haddasa maka damuwa". sai kawai naji ya buɗi baki yana cewa, "kema kar da ki damu, dama na shirya fuskantar wannan ƙalubalen, irin wannan kalaman ba zasu dameni ba, ko da finsu ne ma ba zanji ciwo ba...da sannu kema za ki faɗa min su ne, wataƙila yanzu, wataƙila zuwa wani lokaci". "Allah ya kiyaye bana fatan hakan ko da ba akanka ba". sautin muryarsa ya washe da ce min, "ke kam wai ba kya da tsoro ne?". Ya faɗa murya da ɗan ƙarfi. sai nace, "Allah shine abin tsoro ai, kuma kai ɗin ai ba kayi kama da mugu ba da har zan tsorata da kai. Yanzu dai kazo mu tafi kaga magriba na gabatowa kuma Gwaggo nah zata mani faɗan ban dawo da wuri ba". "baki sanni ba, baki san wane ni ba amma kina nema na raɓe ki, nace miki bani da gida, anan wurin nake rayuwa ta. Shin wai baki gudun na cutar dake ne ke kam?". na marairaice idanuwa ina dubansa da rashin jin daɗi nace, "Annabi S.W.A yace *KAMATUDINI TUDAN* (duk abunda kayi sai anyi maka). kai ɗin kana da Mama, kana da Ƙanwa, ƙilan ma kana da Yaya mace, nan gaba zaka auri mace, kuma ta iya yiwuwa ka haifi ƴa mace. Kaga kuwa nayi amanna da cewar ba zaka cutar dani ba saboda ba zaka so wani ya cutar da naka ba". sai yaja dogon numfashi ya sauke sannan yace min, "ki dinga kiyayewa. Yanzu kibi bayanta ku tafi gida, kar Gwaggo'n ki tayi miki faɗa". maganarsa ta haddasa jikina yin sanyi, naji raina fayau, nai ƙasa da idona ina kallon yatsun ƙafata nace,"to idan na tafi kai fa?". "so nake ki yarda dani, bana magana balle har ta kai ga nayi ƙarya. inda kika ganni anan nake rayuwata tsayin shekarun dana faɗa miki, idan har nabi ki bani da wani gida da zan nuna miki nace ina da alaƙa da shi. don haka ki tafi kawai ki ƙyaleni". "to amma kayi alƙawari idan na tafi na barka ba zaka kuma shan wannan abar me cutarwa ba?". sai ya rufe ido ya ɗan kauda kai gefe, ba zata taɓa fahimtarsa ba, ba zata taɓa ganewa ba. "akan mene zan ɗauki alƙawarin da bazan iya cika shi ba? Kawai ni dai ki tafi kuma karki kuma dawowa inda nake". "kana nufin ba zaka iya daina shanta ba kenan? Na faɗa maka fa shanta haramune, ko ka fi so ka aikata abunda Allah ya haramta?". idonsa a kulle ya shiga girgiza min kansa alaman A'a. "to in dai haka ne, don Allah kar ka kuma shanta daga yanzun nan. Kaga shi yasa ma mutane ke maka kallon ɗan iska, kuma alhalin kai ɗin ba shi bane. Wannan ba zata yi maka maganin damuwa ba sai dai ta cutar da kai, ka miƙa lamuranka ga ubangiji sai kaga ya yaye maka damuwar dake tare da kai. Ƙilan mu kuma haɗuwa ƙilan ba zamu kuma haɗuwa ba, amma ina roƙonka da Allah karka kuma shan taba, ka nisance ta nisa
🏠