NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 59 of 98

afi kar ya kuma tsotson baki, sai kawai na tsinkayo muryar shi yana faɗin,“abinda yau yafi tsotsar maki baki shi zan maki, za ki gane shayi ruwa ne zalla, za ki san kince ni za ki mara marar kunya kawai”. Nan ta ke ya shiga cire rigar shi ya zama daga shi sai gajeran wando, na saka hannuwa na rufe idona, gabana sai dukan dubu-dubu yake yadda kasan ana surfe akan ƙirjina, zuciyata kamar zata faɗo ƙasa tayi dancing haka nake jin yanayin yadda ta ke duka. Ta cikin hannuna nake ganin shi yana takowa, sai daya iso har inda nake naji ya cafki hannuna, sai ji na kawai nayi ya wulla ni kan gado, yana ƙoƙarin hawa gadon nace,“na rantse da Allah idan ka hawo gadon nan kamar a bakin Baba, tunda na kalla sam baka tsoron Gwaggo ka mayar da ita sakarya Kuma wallah Allah indai...”. Ban kai aya ba na jiyo muryar Gwaggo tana ƙwalo min kira. Da sauri ya mayar da rigar shi da wandon shi ya samu wuri ya zauna ni kuma yace min, “tashi ki shiga toilet ki tabbatar kin wanke fuskarki ta wanku, zance ma Gwaggo kina wanke min toilet kuma wallah idan naji kin faɗa mata magana ɗaya akan abinda na maki”. ya nuna ni da yatsa alamun kin san sauran. Cikin hanzari kuwa na diro daga gadon na faɗa toilet ina shiga Gwaggo ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana faɗin, “a’a Zainab tace min Sabina’n tana nan, ko kuwa tayi wani ɓangaren?”. “Eh tana nan, tana wanke min toilet ne”. ya bata amsa ataƙaice, kansa na ƙasa kamar me yankan farce. “Tolet kuma?, yau kuma ƴar wankin tolet ka mayar da ita bayan wulaƙancin duk da kake mata a baya bai ishe ka sai ka haɗa da folishwan?”. ina toilet amma yadda ta faɗi kalmar Punishment ba ƙaramin dariya ya bani ba. Yaya Haidar yace,“Gwaggo wai yaran nan idan ba’a basu aiki dame zasu horu idan sunje gidan miji, ki riƙa kawar dakai akan Sabina mana bafa ita ɗaya ne ƴa ba”. “au tou, haba sai ka ce min kai kayi ƴaƴan ai har daka san horo, tunda har ka iya tsayawa tsegege ina faɗa kana faɗa, Aliyu ka shiga hankalinka dani, wai bance ma ka daina zuwa gefe na ba har ka ganta ka saka min ita aiki ba, Aliyu ka fita idona na rufe billahillazi tun kafin nayi maka abinda har ka koma ga ubangiji bazaka manta ba wallah”. tana ida zancenta, ta ƙwala min kira, ni kuwa dama ƙiris nake jira na fito muna haɗa ido tace,“jakar uban can, kar kace min kuka ka bata, don wallah mai barinka ka ƙara kwana gidan nan sai ikon Allah”. da sauri na girgiza kai ina tuna sharaɗin daya gindaya min nace,"a’a fa Gwaggo, ina wanki ne ƙwaro ya faɗa min a ido, shine kika kalla yayi ja haka, amma na fitar sai dai bai daina min zafi ba, muje”. naja hannun ta muka wuce don nasan zata iya fahimtar abinda ya faru. [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(20)* *Kano.* "idan ka gama ka kulle masallacin". limamin masallacin da ke tsaye akan Alhussain yace da shi. Alhussain da kansa ke ƙasa kan ƙur'anin dake hannunsa yana karantawa bai ɗago ba sai daya kai aya tukunna. sannan ya ɗago da kansa dake masa nauyi ya kalli Liman ya amsa mishi da,"tom Malam". har Liman ya kai bakin ƙofa sai ya dawo ya duƙa ya ajiyewa Alhussain naira 200 a kusa da shi. tsawon wucewar mintuna talatin sannan ya kammala karatun ƙur'anin, ya shafa adu'ar da yay sannan ya mayar da ƙur'anin ya kai cikin drower ya aje. ya dawo ya tsuguna ya ɗauki kuɗin da Liman ya aje masa yana tayi masa adu'a cikin ransa. sannan ya fita ya rufe duka ƙofofin masallacin ya ɗora mukullin a inda ake ajiyewa. bayan sallar isha'i ne lokacin, dan haka unguwar ta daɗa yin shiru sai haushin karnuka da kake shi, haka kowanne layi duhu saboda rashin wutar nepa. tafiya yake yana takawa a hankali saboda yanda ƙafafunsa ke yi masa tsananin ciwo, haka har ya fito bakin titi, anan ya hangi wata ƴar tsohuwa mai siyar da tuwa ya ƙarasa wurinta ya siyi tuwo da miya na hamsin, a wurin ya zauna yaci sannan ya tashi ya koma bakin masallaci inda yake kwana anan yanzu tun bayan fitowarsa daga cell. kuma a wannan zaman da yay ne gyangyaɗi ya fara ɗaukarsa, cikin baccin dake neman ɗibarsa yaji kamar hayaniya, dan haka ya buɗe idonsa da sauri, dai-dai lokacin da motar ƴan sanda ta tsaya a wurin, a gabansa, dan haka ƙwayar idonsa akansu ta sauka. bakinsa da zuciyarsa suka shiga furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un a sanda yaga Ƴan Sanda na tunkaro shi, wasu matasa kuma a tare dasu na faɗa musu cewar,"ehh shine, wallahi shine". kalmar shine ta bada tartsatsin tsawa acikin kansa, yaja numfashi ya sauke tare da lumshe ido. a cikin duhun idonsa abunda ya faru da shi kwanakin baya da suka shuɗe ya shiga haska masa, ko kaɗan baya fatan hakan ta ƙara maimaituwa masa, ko da a mafarki baya fatan ƙaddara ta ƙara kaishi hannun ƴan sanda. zuciyarsa a yanzu faɗa masa ta ke akan ya tashi ya gudu, ya tashi gudu tun kamin su cimmasa su kama shi, bai san dame suka zo ba wannan karan, idan har ya ƙara shiga hannun hukuna taya za'ai ya fito?. ya buɗe idanuwansa ya suke kan ƙafafunsa biyu, ɗaya ta
🏠