tare”. sai kuma na kwaɓe fuska nace,“amma fa gaskiya Gwaggo kibar cewa ina da aljanu, waye ke son su, amma ke duk magana ɗaya sai kice aljanu, mutum ba zaiyi dariya ba sai ya zama jinnu”. na faɗa ina yin ƙasa da kaina tamkar zanyi kuka. Ganin haka yasa Gwaggo kamo hannuna tace, “haba ƴar lalen Gwaggo, kinga kece naga sai murmushi kike ke ɗaya kuma kin san Allah da yayi ni ina da tsarguwa shisa kika ga nace haka, ko kuwa akan maganar ɗazu shi ne duk kike faman wannan murmushin, ko dai a makaranta kin samu ɗan..”. bata ƙarasa maganar ba muka haɗa iɗo, sarai na gane inda ta nufa sai na waske nace. “Gwaggota kenan mai abin mamaki, ki bama mutum daɗi ki bashi haushi, nasan fa abinda kike nufi, to ni bashi yake sakani nishaɗi ba, kawai dai ina son zuwa Kano saboda naga Farhana, kuma naga dangin Mama shi ke sani nishaɗi wallah. Kuma duk lokacin dana tuna yadda Kike tattalina kamar ƙwai sai hakan ya kuma tsundumani cikin nishaɗi da jin daɗi, ke dai Gwaggo Allah kaɗai zai biyaki ya kuma ƙara maki nisan kwana mai amfani ya ɗora ki kan maƙiyanki. Ina son ki Gwaggota”. na ƙarasa faɗa ina bata sumba a goshi. Gwaggo ita ma ta shafa bayana tana saka min albarka tana faɗin, “ai kema kin san indai akan kine sai inda ƙarfina ya ƙare, Allah dai ya haɗaki da miji nagari. Oh Allah ka nuna min wannan rana, gaskiya ranar akwai shagali, ke ranar sai na kwaso shoki, don ma wai babu Sahibina a kusa da nake faɗi maki abin sai yafi armashi”. Dariya nayi na janyo kwanon abincin da ta kawo min ɗazun na fara ci kafin nace, “ɗakko wata hirar don yanzu idan kika fara labarin Sahibin kin nan sai mu kwana mu yini baki gama ba, sai kace Sahibin kin nan yafi kowa”. ta ɗan dungure min kai, “munasira!, yo har kya faɗi min wani zancen Sahibina, baki ji akace kowa da bazarsa yake taka rawa, to ni tawa rawar da ta Sahibina ce, yo Allah na tuba ke har kya yimin zancen zan ɗakko maganar Sahibi, kema fa idan kika samu wuri tsaf nasan sai kin zarce ni, yarinya baki san loɓe ba(love)”. wata dariya ce ta suɓuce min wadda yayi sanadiyar zubar da abincin da nake ci waje, Gwaggo tamin duban sheƙeƙe kafin tace,“kinga ba nayi magana kice ke baki san zance ba, yo meye abin dariya anan?”. ta tambaya babu wasa a fuskar ta, da alamu ta ƙulu, don haka nayi gaggawar tsayar da dariyar da nake yi kafin nace,“yo Gwaggo kece da fama, sai kice sai kinyi turanci kuma baki iya ba, ai sai ki haƙura haka, idan kuma ba haka nace maki zan fara koya maki haruffan hausa shima kinƙi da duk kin san yadda ake faɗan words a hankali”. “ke kika san wani was(words), hakan ma tunda zan faɗa a gane ai shikenan tunda ba wurin wani naje na faɗa ba, bare naji kunya ato”. “yo ai kuwa wataran zaki faɗa a wurin wani wallah idan baki daina ba”. Gwaggo tace, “yau naga iya shege, ke Sabina fice min da gani”. Daga haka na miƙe ina dariya har na fice a ɗakin, dama yau na gama shiri na ba zan kwana wuri guda da Gwaggo ba duk tabi ta dameni da hayaƙi. Kai na tsaye nake tafiya dariya nacin cikina, har na isa corner da zata sadaka da kitchen kaina a ƙasa naji nayi tuntuɓe da abu da sauri na ɗago kaina ina duban meye ne, karaf muka haɗa ido da Yaya Haidar, da sauri na zaro ido shima ni yake kallo da irin kallon wanne abu zan maki na huce. ni kam ganin kallon da yake watso min tuni na sauya hanya, nayi gefe da niyyar wucewa yace,“dutsen da kika taka hala bai ji maki ciwo ba?”. Na ɗan ɓata fuska nace, “eh bai jimin ba”. ina faɗar haka na kuma niyyar wucewa. aiko a zafafe ya damƙo hannuna, tuni ido na ya raina fata, duk lokacin da muka haɗu sai naga kamar zai kuma tsotsen baki ne, fuskata ta cika da tsoro, baki na fal in-ina nace, "ka..kaj..kaji tsoron Allah kaga dai ba abinda nayi maka karka tsotson baki don Allah”. ina gama faɗar haka hawayen da suka cika ido na suka samu nasarar sauka kan ƙafar Yaya Haidar ya kuma ƙulawa fuskarsa tamkar ta bijimin sa yace,“an faɗa maki kowa ɗan iska ne kamar ke, da za’ayi tayin abu guda, ko an faɗi maki kowa maye ne kamar ke sha uku kawai, goge min ƙafa na ko na zane maki ƙaramin mazaunanki nan”. takaici ne ya ishen, a zuciyana nace, _wallah kamar na zabga maka mari nake ji._ zaro idon da Yaya Haidar yayi yasa ni tsorata ba ƙarama ba, don wata iriyar damƙa ya kuma yima hannuna ya matsa min ya kuma galla min mintsini, take na buga tsalle idona ya cigaba da zubar da hawaye da ƙarfi ya buga min tsawa yace,“ni sa’an kine, Sabina ina wasa da ke ne, ni zaki kalli tsabar idona kice za ki mara?”. ya ƙarasa maganar yana nuna kansa. “wallah zancen zuci ne ya fito fili ban san na faɗa ba, don Allah kayi haƙuri please Yaya Haidar Allah ban san ya fito ba”. ɗan cif-cif gemunsa ya kama yaja kana ya kawar da kanshi gefe guda, ban ankara ba yaja hannuna fuuuuu sai ɓangaren shi. ina ta bashi haƙuri amma sam bai kulani ba, saboda maganar tayi mashi ciwo, yana shiga yasa key a ƙofar ya saki hannuna, nan na shiga bashi haƙuri akan ya barni na t