i ba. ganin yanda ransa ya ɓaci yasa nace,"Yaya Abba dama ana halittar mutane iri guda ko da ba identical twins bane?". Ko kallo na bai ba, sai guntun tsaki daya kuma ja, bai ƙara saurarena ba har muka isko gida. Ina shiga parlo na faɗa jikin Gwaggo dake zaune, ko ta kaina bata bi ba sai taɓe baki da tayi, ganin dai kukan nawa bana ƙarewa bane tace. "ke wai Ubanki Auwalu aka yi miki da za ki zo ki sani a gaba kina faman kuka, bayan kin san ba abinda ke ɗagan hankali a duniyar nan sama da kukanki, za ki faɗan mene ko kuwa?". na mata shiru ina ƙara ƙanƙameta, a gaskiya ina bala'in son ganin Yayana, dan a yanzu jin zuciyata nake na wani matsewa sa zafi. Ta tureni da ƙarfi tana cewa, "je can ki ƙarata da halinki ke ɗaya, idan kika ƙarar da hawayen kya rasa na zuwa ɗakin miji ace ba ki da kunya, ke baza'a taɓa tambayanki mene ke damunki ba ki faɗawa mutane ba a lokacin, sai kin gama iskance-iskancenki tukunna. to Wallah ki ka kuskura kishiya ta gane ma ruwan hawayenki gasa ki zata dinƙa yi". Sai a sannan ne nayi shiru, nace mata, "Gwaggo tunda munyi hutu yau don Allah ina so naje naga Hajiya da Mami da su Uncle Nasir". Ina nufin dangin mahaifiyata. Taja tsaki tace, "amma ke kuwa kina da abin haushi, dama abinda kike wa kukan kenan?". "a'a bashi bane. Wani Malaminmu ne yace na masa sata, har da kirani ofishinsa ya ƙara min wulaƙanci, shine nasa kuka sai yace wai Kukana kamar kukan Shanuwa, ita kuma ɗayar Malamar tamu tace min daƙiƙiya". Gwaggo tai wani zabarin gyara zane tana furzar da goron bakinta tace,"shi Malamin naku? Yace kin masa sata kuma kukanki kamar na shanuwa?". na ɗaga mata kai alamar tabbatarwa. ta jijjiga kai da kyau sannan tace,"To sata ta ƙare a ahalinsu, kuka kuma nasa ne ke kama dana tumaki. Ita kuma Malamar itace babbar daƙiƙiya da ta kasa fahimtarki. Kuma suje da halinsa na rashin kyautawa Allah zai saka miki, yanzu kije ki wanke fuskarki kizo kici abinci, na san babu abinda kika ci ki ka fice karatun da ba lada ba zunubi". na goge hawayena ina tambayanta cewa,"to Gwaggo zanje ɗin?". "za kije mana, ba kunyi hutu ba?". "ehh munyi har na wata guda ma". "to kinga kuwa kina da lokacinma da za ki je ki zazzaga musu. Ki bari idan Karima tazo sai ku wuce tare idan zata koma". Na miƙe ina cije leɓe nai ɗakina, gado na faɗa ina jin farinciki da nishaɗi, zanje naga Yayana, kuma mu taho tare da shi don bazan kuma barinsa acan ba, dole ne ma ya biyoni. Na rugume pillow inata murmushi ni ɗaya, dana rufe idona babu hoton dake haska min sai nasa, zumuɗi duk ya hanani sukuni, na ɗauka waya na kira Inna Karima na tambayeta yaushe zasu tace sai nan da sati biyu, ina jin haka ban san lokacin dana gilla mata ƙaryar ai Gwaggo bata da lafiya ba, aiko hankalinta a tashe tace min suna kan hanyar zuwa gobe ko jibi. Na kashe wayar ina dariya sai kuma na fara Allah na tuba Allah ka ƙarawa Gwaggo tah lafiya, ina haka ta shigo, hannunta ɗauke da kwanon abinci, yanayin da ta riske ni yasa tace, "ke lafiya?". "lafiya lau Gwaggo". Ta dire min abincin saman table tana faɗin, "da dai sauƙi kam, Allah ya bada lafiya inda rabon samunta". Ta juya za ta fice na dakatar da ita da tambayata. "Gwaggo kin taɓa ganin Halitta ɗaya a mutum biyu?". ta wani juyo a sukwane tana ambaton sunana, jin na amsa yasa ta cewa,"ohh ke ɗince dai". sai na ɓata fuska na turo baki gaba nace,"wai Gwaggo ba zaki bar ce min mai aljanu ba". tana gyara ɗaurin zanen da a ko yaushe nake takaicinsa tace,"to ai tambayar taki ce Sabina ta a bincika ce". "to ni dai ki bani ansata". "ansar me zan baki Sabinan Gwaggo?". na ƙara jefa mata tambayar, a wannan karon daya kasance tana fuskantata ne sai kawai ta bini da ido tana kallona da kyau cike da nazari, sai kuma tasa kai tayi hanyar fita tana faɗin,"to Allah yasa ba gamo kika yi ba...ni dai Rakiya Allah kayi min maganin abubuwan da suke neman fin ƙarfina".
*Please Vote, Comment and Share.*[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(18)*
bayan fitar Gwaggo kuwa raina fes nake jin shi, murmushi kuwa idan ka kalla fuskana kai kace gonar auduga ce saboda yadda haƙorana suka gagara rufewa. Har sai da Gwaggo ta dawo ɗakin ta iske ni kwance kan gado still dai murmushin nake, ina kuma ta faman juyi akan gado, sai da ta ƙare min kallon tsaf kafin ta samu gefen gadon ta zauna kana tace. “Allah mai girma da ɗaukaka, yau naga Mace. Anya Sabina lafiyarki kuwa, na fita kina dariya haka zalika na shigo kina dariya, to ki daiyi a hankali don wallah dariya illah ce, kuma kin san bana son dariya”. matsowa nayi kusa da ita, na kuma sakin murmushi. Sai naga ta miƙe tsaye zata nufi hanyar fita nayi caraf na riƙe hannunta, ina ƙunshe dariyar da ta ciyo ni, don nasan sarai abinda ke ranta nace,“wai Gwaggo me kika gani, ina zaki je dana ga kin miƙe?”. tace, “yo Sabina na sani ko aljanun ki ne suka dawo, wannan dariyar haka sai kace an maki bushara da shiga aljannah”. “yo Gwaggo kika sani ko busharar aka min, kinga ai sai mu tafi