rin yanke hukunci dai-dai da buƙatata". kawai saina fashe da ina faɗin, "wallahi tunda uwata ta haifo ni duniyar nan ban taɓa yiwa kowa sata ba. ko wancan karanma sharri Umma tayi min. dan Gwaggo nah ta bani tarbiya mai kyau wanda ko kallon abinda ba nawa ba bana iya tsayawa yi". Sosai nake kukan har sai dana kifa kaina a gwiwata, wannan wacce iriyar ƙaddara ce. Naji ya cika bakinsa da iska ya furzar, a cikin siga ta lallashi yake ce min, "ohhh Beauty please stop crying mana, am just kidding you ba zan faɗawa Baba satar da kika mani ba". na ɗago idona masu ruwan hawaye nace,"au da gaske ne ma na maka satar? To mene na satar maka?". y gyaɗa kansa sau uku kamin nan yace,"ofcourse kin sace min abu mai muhimmanci a tare da ni, amma i promise you i will not tell your Dad for now, but for sure zan faɗawa Momy nah, what ever she decide akai then...". Bai ƙarasa ba ya kanne min ido guda yana cije leɓensa na ƙasa, yana abu kamar Yaya Haidar. Ni kam na shiga uku, wannan rana ta yau bata zo mani a sa'a ba, na kuma fashewa da kuka, naji yana cewa, "shikenan idan kina so na bar maganar to ki bani haƙuri". Ai da sauri na ɗago nace, "kayi haƙuri". "haka ake bada haƙuri?". Na karayar da kai, na kama kunnuwana nayi exactly yanda nake bama Yaya Abba haƙuri idan na masa laifi, "Don girman Allah kayi haƙuri". Hasken flash yasa na ɗago ido ina kallonsa, ƙyasss naji ƙarar ɗaukar hoto, zanyi magana kawai na ƙyaleshi, ba buƙatata kenan ba. "Sabina Auwal right?". Ya jefo min tambaya. na ɗaga masa kaii "ehhh". "nice name Beauty". Na murguɗa masa baki, ya tari numfashina da cewa, "yauwa and i will also tell Baba kina murguɗawa manya baki". Na ɗago zan bashi haƙuri na tuna abinda Gwaggo tace min duk sanda wani yace ina murguɗa masa baki. Na turo bakina gaba nace, "ai dai ko Gwaggo tasan ina yi, kuma ma ai a wurinta na koya. Saboda haka ko an kai ƙarata wurin Baba ba abinda zaice, "Ƙaramar dariya naga yayi, ina marairaice fuska na haɗa hannuna nace, "don Allah kai wane?". a karo na babu adadi ya janyo leɓensa na ƙasa ya cija sannan ya shafo sumar kansa yace, "sunana Muhsin Muhammad Na kowa...". Bai ƙarasa abinda zaice ba na wurga masa tambayan, "a kano kake?". Ya kaɗa min kai, "nop, ni banma taɓa zuwa Kano ba. Mahaifina balaraben sudan ne, also my Mother she's shuwa arab, mu 6 duk an haifemu a misra, wata harƙallar aiki ta kawo Daddy nah nan Abuja, ataƙaice bamu haura 4years ba anan, like you see me ina da asali, kuɗi, gata da duk wani abu na jin daɗin rayuwa, sai dai banda lafiyan ƙafa, as soon kuma zamu koma can ƙasarmu da zaran Daddy ya kammala abinda yake. So kema sai ki shirya becouse we are going along with you, acan ne za ki amsa hukuncin satar da kika mani". Zan buɗi baki nayi magana Malama Muhsina ta shigo. "Brother is time for the meeting". Na kalla ya duba agogonsa yace,"oh shet". Sai kuma ya kalle ni ya kalleta yace, "Sister zo ki tayani lallashin Beauty tun ɗazun ta ke kuka taƙi yin shiru, kuma kin san na tsani kuka bare nata ma da babu daɗin ji kamar kukan shanuwa". Ya faɗi hakan yana wani toshe kunne, Zumbur na miƙe tsaye na ƙwace hannuna daga nasa, don cin mutunci kukana ne mai kama dana cow, ina tura baki na raɓa Malama na ɗauka jakata dake kan kujera nayi ƙofa. Sai dai a rufe take, na juyo na kallesa naga yanda yake dariya ƙasa-ƙasa, na kawar da kaina cike da jin haushinsa. Malama Muhsina ma tayi siririyar dariya ganin yanda na cukule tace, "Soryy Beauty ki rabu da Brother nah, idan kika biye masa zai ta sanyaki kuka ne. Bari nazo na buɗe maki". Ina kallo ta kamashi sosai kana ta ɗora shi kan wheelchair nasa, da alama dai ƙafafunsa basa aiki kwata-kwata, mutum ba isashshen lafiya sai ɗan banzan surutu da neman magana". tana buɗe ƙofa nayi ficewana raina duk a dagule, gefe ɗaya kuma ina saƙa abubuwa da dama a raina ina warwarewa, a wannan lokacin kowaye ya ganni yasan kwai abinda ke ƙasan raina saboda yanda nake zabga ƙwafa. ina kan hanya Yaya Abba ya kirani, na ɗaga wayan nace masa gani nan zuwa, Allah sarki bawan Allah ashe har yanzu yana jirana. Intisar ma ashe tun ɗazun tana waje zaman jirana, tana hangoni ta taso da sauri tana aika min tambayan me ya faru, ni dai shiru na mata ban saurareta ba nayi tafiyata ina sha re hawaye. ina zuwa mota na buɗe na shiga, da shigana na ƙara fashewa da kuka, tambayar duniya Yaya Abba yace me aka mani shima na masa shiru, gaba ɗaya ba komai ke damun zuciyata ba sai kewan Yayana, tausayinsa na kuma ratsa ni, ganin wannan mai kama da shi ya matuƙar ƙara tada min da kewansa, ya zama dole naje naga halin da yake ciki, bazan dawo ba har sai idan da shi ne, Allah yay mana wannan arziƙin da ba zan taɓa barinsa a wahala ba. dan Na gama gane Proff ba Yayana bane shi ya fiya surutun wofi, Yayana kuwa magana ma wahala ta ke masa. a ƙufule Yaya Abba yace, "ke ban san iskancin banza fa. Ina miki magana kin min shiru, exams ɗin ne tayi wahala?". Kai kawai na girgiza masa, sai yaja tsaki ba tare daya ƙara ce min koma