NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 55 of 98

damuwa. "mene? Me kake so?". Na tambaye shi cikin sanyin murya da tausayawa. a wannan lokacin na manta da tunanin ruɗanin dana shiga cikin wucewar wasu daƙiƙu. baiyi magana ba sai nuni da yay min da kansa, saboda haka dana fahimci me yake nufi saina duƙa, ina tsugunawa gabansa naji yana faɗa acikin wayar. "Mom ga Beauty zaku gaisa". Ya faɗi hakan yana kara min waya a kunne, kenan da mahaifiyarsa ne yake waya tun a ɗazu, dole ya kasance cikin nishaɗi, _me mahaifiya a raye shike jin daɗin rayuwa,_ na faɗa a zuciyata ina sanya hannu na goge ƙwallar idona. Na maida hankali kan maganar da Mom ke yimin. "Beauty nah". Itama naji ta kirani da wannan sunan, duk da mamakin daya kamani sai na kawar, ban san lokacin da muryana ya koma na shagwaɓaɓɓu nace, "Mom ba sunana Beauty ba". tai murmushin manyance tace, "to ya sunan ɗiyar tawa?". nace, "Sabina, Sabina'n Gwaggo". maganar tawa ta sakata yin murmushin mai sauti, sannan tace da ni. "Allah ya albarkaci rayuwanki Sabina tah, ya kuma dawwamar dake a farinciki". na amsa da,"ameen Mom, na gode sosai. Kema Allah ya ƙara maki lafiya da nisan kwana". Ta amsa min da, "amin ɗiyar kirki". Sai yanzu na tuna ban gaidata ba, nai saurin rufe bakina ina zaro ido na kalla Proff dake aikin kallona, a hankali nace, "Mom ina yini. Kiyi haƙuri don Allah tun farko ban gaida ki ba". tace, "dont worry my daughter, jin muryanki ya fiye min gaisuwan, tabbas yau ɗin nayi farinciki da jinki. Ina Yayan naki?". Tana faɗar haka na ɗago na dube shi, zuciyata na kuma tsinkewa da lamarin, dan da Mom tace Yayana sai naji kamar wancan Yayan nawa ne da gaske. "Daughter". Nai firgigit daga gajeran tunanin dana tafi, "na'am Mom". "ina Yayan naki?". ta kuma tambayana. "Mom gashi nan". "oak bashi wayar, Idan kinje gida ki gaida min da Gwaggo sosai kinji". nai knodding kaina kamar a gabanta nace, "tom Mom zataji". lokaci ɗaya saina sami kaina da yin wasu abubuwa da ban san lokacin da nake yin su ba, shi kansa abunda nace mata a yanzu sai daga baya na san na faɗa. "Mom ki cewa Yaya ya daina ƙarya ba kyau, shi dai babban mutum ne". Nai maganar ina masa kallo mai harara. murmushi naji ta sa ki kana tace, "shikenan zanyi masa faɗa, daga yau ba zai ƙara ba Beauty nah, oak Bye bye". "aha Bye Mom". Na faɗa ina miƙa masa wayar, yana ansa kuma na miƙe daga tsugunen da nake da zummar barin wajen ya maidoni na zauna. Ina faman cin magani nake kiciniyar ƙwace hannuna daga nasa amma yaƙi bani damar hakan, su kai sallama da Mom, cikin ɗaurewar fuska yace dani, "ba ki da kunya dama? Sa'anki ne ni da kike hararana? Ko dan kinji nace a kira min ke, yanzun nan sai na baki carryover, kuma idan aka faɗi course ɗina har spilling". Wayyo Allah nah ni Sabina, a wannan lokacin ji nayi kamar na ɗora hannu akaina na kurma ihu, domin maganar da yake a cikin tamkewar muryar nan sai ya kuma rikeɗe min zuwa Yayana. to ni maganar carryover ma bata bani tsoro ba kamar yanda shi yake bani tsoro, babu maganar da na tuna sai ranar da Yayana yace karna kuma zuwa inda yake idan ba haka ba sai ya mani fyaɗe, sak da irin wannan sautin muryar ne. a yanzu cikin ɗaurewar fuska yace da ni, "binciken me kika mani ɗazu a jikina?". nace, "na duba ne naga ko kai ɗan yankan kaine". Na faɗa cike da jin haushinsa. sai Yay siririyar dariya yana cewa, "shine sai kika zo kina bincike ni right?, ta yanda Koda ni ɗin ne kamin na gama waya da Mom kin arce ba? Ke gaki me wayo ko, to yanda kika shigo office ɗin nan kin shigo kenan har busa ƙaho kina nan". na nuna masa ko kaɗan ban kaɗu da maganarsa ba, dan na lura irin Malamn nanne watsatstsu da idan mace ta biye musu zasu kaita su barota. dan haka kai tsaye na jefa masa tambayan,"kiran nawa na menene?". na faɗa ina miƙe da ƙoƙarin ƙwace hannuna daga riƙon da yay min. kuma muryarsa ta fito kai tsaye zuwa kunnena da cewan,"zamu je gidanku ne na faɗawa Daddy'nki, daga shiganki exams hall kika yi min sata, hakanne ma yasa na binciko files naki na duba address na gidanku, ko da idan na tambayeki za ki min ƙarya". *Please Comment, Vote & Share.* [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(17)* a lokaci guda furucinsa ya daki tsakiyar kaina. Na zaro ido a tsorace ina dubansa nace,"na shiga ukuna, ni ɗin na maka sata?". Ya ɗaga min gira ɗaya alaman ehh, a ruɗe na shiga ce masa,"wallahi ko Gwaggona tasan bana sata, Kuma ban taɓa yunƙurin yi ba. kuma don Allah karka je kace ma Baba na maka sata, ba zai tsaya jin komai ba zai ɗauka tsatstsauran mataki akaina. Ni dai nasan ban maka sata ba amma ka faɗa min ko mene indai kuɗin account ɗina ya kai zan biyaka ta ke anan". Ina faɗa duk na rikirkice, tsorona Allah tsorona Baba ya kuma korata daga gida. a wannan duniyar tashin hankain da Proff ya jefani naji maganarsa na shiga kunnuwana da cewa,"kuɗi ko kuma wata kadara ba zata iya biyana abinda kika satar min ba, dole Baba da kike tsoro shi zansa Daddy nah yaje ya sama ya faɗa masa, ta yanda Baba da Daddy nah zasu yi sau
🏠