a muƙamin daga ina ya samo su? a yaushe?. mamaki ya kamani zuwa nisan da ba zai kwatantu ba, wani abu ya daki ƙwaƙwalwata a lokaci guda, Yaya! Yaya dai!, dama waye shi?. dukkan tunanin dake cikin kaina da ma abinda zuciyata ke rayawa ya tsaya acak a sanda idona ya sauka akansa, lokacin daya juyo ya fuskanceni, dan sanda na shigo ya juya min baya. sai na zama kamar wadda aka dasa a wurin, idanuwana na gaza ko da ƙiftawa daga kallonsa, kallon fuskarsa dake ɗauke da ƙayataccen murmushi da yake, irin murmushin nan daya taɓa yi a waccen ranar da yace zaiyi koyi da ni. kuma a take dukkan faruwar wani abu ya shiga haskawa cikin idona, tun daga ranar dana fara ganinsa zuwa ranar ƙarshe da naje wurinsa, da ma sauran ranakun dana ɗiba ina zuwa ban same shi ba. waccan rayuwar dana sansa ba irin wannan bace, haka zalika wancan yanayin da na sansa da shi ba irin wannan yanayin ba ne. yanayin da yake ɗauke da shi a yanzu yanayi ne na nuna yana cikin nishaɗi da jin daɗin rayuwa. kuma da dukkan wata alama wayar da yake ne yasa shi hakan. _ko dai mafarki nake?_ zancen da zuciyata keyi kenan, dan haka saina sadda kaina ƙasa na rufe ido, sannan na buɗe da dukkan yaƙinin zanga saɓanin abunda nake gani. sai dai wannan muryar tasa da ba zan taɓa mancewa da ita ba ta shigo cikin kunnuwana ta sami mahalli acikin ƙoƙon kaina. "Beauty bismillah come have a sit". Ya faɗa har zuwa wannan lokacin bai bar wayar da yake ba, na ɗago ina duban kujeran da yake min nuni da shi, sannan na ƙara masa wani kallon, kallon dana kasa fassara shi da irin yacce zuciyata ke lissafi. abu guda ɗaya kawai da na sani shine a lokacin da ma guda ɗaya nake nema da zanyi masa wulaƙancin da har mutuwa ba zai manta da shi ba. a rayuwata na tsani mutane guda uku, munafuki! maƙaryaci da kuma mayaudari. dan haka na ɗaga ƙafafuna na ƙarasa na zauna akan kujerar, gaba ɗaya ma zuciyata ta kasa lissafa abunda zanyiwa wannan bawan na Allah, duk da a gefe guda zuciyar tawa ta kasa gasgata shi ɗinne. dan wancan da na sani, ko kusa bashi da wata alama da ke nunin yana da wata rayuwar ta daban bayan wacce yake acikinta.
sai dai har yanzu tunanin guda biyu ne acikin kaina. idan wancan dana sani ne to wanene shi?, haka idan ba shi bane to wannan wanene?. sai dai a irin alamomin da nake gani kamar ba mutumin da nake tsammani ba ne, dan shi wannan nunawa yake kamar bai taɓa sanina ba?, beside ma Yaushe ya zama gurgu? ko kuma hakan duk na cikin takun basajarsa?. na ɗago ina ƙare masa kallo, me yasa nake jin bugun zuciyata na tsananta ne idan ina kallonsa, alhalin shi wancan bana tsintar kaina a irin hakan. gaba ɗaya yay shiru yana sauraren maganar da ake masa ta cikin waya, ya ɗago karaf muka haɗa ido da shi, ya sakar min sanyayyan murmushi, hakan yasa na ɗauke nawa idon daga kansa cikin ɗaurewar fuska. zuciyata gaya min ta ke Wannan ba wanda na sani bane, domin ba zan taɓa manta duk wasu abubuwa da suka danganci Yayana ba, sai dai tsananin kamarsu da wancan ya ɓaci, tamkar an tsaga kara, ba su da wata maraba daga kamannin fuskar har surar jikin, hatta muryarsu iri guda ce, kawai shi wannan gurgu ne kuma yana da fara'a, to amma shima wancan ai halin rayuwan daya tsinci kansa ne yasa baida abubuwan da wannan yake da su. ban san lokacin dana miƙe tsaye ba, na tsaya akan ƙafafuna, fuskata a turɓune babu wani ɗigon annuri na zagayo gabansa, don in samu in tabbatar da zargina, yazo nan yana musu basaja kamar yanda yake yi a garin Kano. Ina tsayawa gabansa na kama ƙugu da duka hannu biyu ina faman jijjjige-jijjige, ƙiyasto abinda zan masa nake idan har na tabbatar da shi ɗin ne. sai dai nayi istigfari sannan na kamo hannunsa, saboda na san hakan da zanyi haramunne ya saɓa da shari'an musulunci, sai dai bani da yanda na iya, fatana kawai na fita daga duhun da nake ciki, links ɗin hannun rigarsa na ɓalle na yaye hannun rigar tasa. shi dai bina da ido kawai yake yana kallon ikon Allah, saboda farko dana riƙe ya janye saina kuma janyo shi na damƙe, na kuma tsorata da yawan gargasar da na gani a hannunsa, wanda wannan gargasar ita ta ƙara tsoratani har na ɗan ja da baya, babu shakka wancan mutumin da nake kira da Yayana ne. amma me yasa yaywa rayuwar masu saurin yarda irina haka? Yaudara!. sai dai har yanzu ina cikin shakku, ban gama yarda shi ba ne, haka kuma ban yarda ba shi bane. sai kuma na ƙara kamo ɗayan hannun nasa daya ke riƙe da waya, na amshe wayan na aza masa a ɗayan hannun yaci gaba da wayarsa, kuma a wannan hannun ne na sauke a jiyar zuciya, saboda hannun hagun wancan mutumin da nake kira da Yaya akwai lamɓaceciyar ƙunuwa a wurin, wannan kuma babu wata alama ta hakan. Na rufe ido ina aikin sauke numfashi, sai kuma kunya ta baibayeni nasa hannu na rufe fuskana, na ma kasa ɗaga ƙafa na koma mazauni na. sai naji ya kamo hannuna, nai saurin buɗe fuska ina kallonsa, sai naga yana ƙoƙarin miƙewa amma ya kasa, ta ke naji ruwan hawaye sun cika min ido saboda tsantsar tausayinsa, shima kuma yanayinsa ya koma zuwa na