NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 53 of 98

da muryar tausayawa ina daɗa bin bayansa da kallo. "ehh shine". Intisar ta faɗa. "baki ga akan stage aka ɗora shi ba daga shi sai halinsa, wannan exams idan baka yi karatu ba ai kana tsakiyar ruwa". ta ƙara faɗa. sai Rahina tace, "ke he is not a student, He is the Financial Accounting lecturer, baya ɗaukan ƴan Level one lectures until level two, Becouse he can't walk bare ya miƙe yay explaining a board, So at level two kuwa bayani ne zaizo yay maku verbally using projecter, ita Malama Muhsinah ƙanwarsa ce, ita ke karɓa masa a L1 nd also she is the one taking care of him at school". "eyyah Allah sarki, Allah ya bashi lafiya". Muka faɗa a tare ni da Intisar. "amma dai baida mugunta ko?". Na tambayi Rahina ina waro ido waje. "ehh to gaskiya bashi da mugunta, amma fa ya iya tsara questions, aima kun gani yanzu, kuma gashi da fara'a murmushi har tunbuɗinsa yake, kuma ba'a faɗuwa course nasa gaskiya saboda kunga yadda ake dagewa, nima ƙaddara ce ta dawo da ni". Muka ci gaba da tafiya muna hirarmu, daga bayanmu muka ji ana mana magana, muka dakata da tafiyar muka juyo. Saurayin yace da ni, "Beauty Malama Muhsina is calling you". Ya faɗa yana nuna ni. Na kallesa ina yamutsa fuska saboda ranar data haskemu. ina nuna kaina nace, "kuma ni tace ka kira, ai ba sunana Beauty ba, sai dai ko ƴan gabanmu ta ke nuna maka". Na faɗa ina maida kallona ga ƴan gabanmu dake tafiya. Murmushi naga yayi yana cewa, "na san ba ainihin sunanki bane, nima ce tayi min na kira mata beauty gata can tana tafiya with pink veil, ai farko dana kira ku Sisters kuka ji ina cewa ko?". Su Rahinat suka ce masa "ehh". Ya kuma cewa,"to da ku ka juyo na kalleki sai naga ehh lallai kin cancanta da a kira da suna Beauty, hakan yasa nima na ɗana. Allah ya tsare miki wannan kyawu naki". Ya faɗi hakan yana wucemu. Na kalla su Intisar da suke kallona suna murmushi, na sauke numfashi na ɓata rai sannan nace. "sarai kun san Malama Muhsina bata da kirki, maimakon ku tayani jimami ku abinma daɗi yay maku, ban san kiran akan mene ba Allah dai yasa ba laifi na mata ba". "amin dai". Suka amsa. Intisar tace, "amma ai ɗazu ta tuna maki baki rubuta suna ba, kiyi gaggawar zuwa may be kin kuma mantawa da rubuta wani abun". Na dafe ƙirji na furta, "na shiga uku na". "Beauty ki dai wuce ki tafi kiran Malama kar ki ƙarama kanki laifi". Rahinat ta faɗa da sigar tsokana. Na kalleta na mata harar wasa, ko mene abin tsokana anan oho. "na san zaman da zanyi dake". Na faɗa ina barinsu. Tsaye na sameta a bakin admin block, dama bamu da nisa da wurin a tafiyan da mukai, ta harɗe hannaye a ƙirji tana jiran isowata, gabana ya faɗi da irin kallon da ta ke mani, na kuma sadda kaina ƙasa na ƙarasa gabanta, ina rissinawa nace. "Maa Someone said you were calling me". Na faɗa har muryata na rawa. Da alama dai tana da izza, tana jijji da kai tace min, "and now you have the opportunity to come After you finish westing my time, right?". Shiru nayi ban ce mata komai ba sai tsilli-tsilli da idanu da nake. ina kallo ta taɓe baki haɗi da maƙe kafaɗa cikin ɗagin murya tace min, "Comon jor my friend, ki wuce Proff want to see you". "Maa waye proff?". Na tambayeta da son ƙarin bayani. ai kamar na zageta saita ɗaga murya a zafafe tana faɗin,"wane proff kike tambayana? Duk faɗin waƴanda ke maku lectures akwai Malami Proff ne sama da mutum ɗaya, mtswww this girl you don't have manner of etiquette at all". Taja tsaki tana kamo kunnena ta bani ranƙwashi,"to daga yau ki san wane Proff, daƙiƙiya kawai, comon to write your name on script ɗazu ma kika kasa, and that is how you got in to university, kamata yay ace kina primary school. Ana magana kina zumɓurowa mutane baki, maida shi ko na bige miki laɓɓa". Nai saurin maida bakina, na ɓata rai ina jin kamar nayi mata mene, ta gallan harara tace,"ki same shi a office nasa". "aina office ɗin yake?". Bata ce min komi ba tai juwarta ta shiga admin block ɗin, na bi bayanta, muna zuwa office na huɗu tai min nuni da yatsanta sannan tai gaba abinta, nabi bayanta da murguɗa baki kana nayi knocking door. "Yes, come in". Aka ce dani, hakan yasa na buɗe na shiga ƙafafuna na rawa saboda duk a tsorace nake ban san laifin da nayi ba, ni da ko wani Proff ma ban taɓa sani ba. Ina wurga idanu nake taka ƙafata, ƙaton hotonsa na gani an rubuta Proffessor Muhsin Muhammad Na kowa, _"fatabarakallahu ahsanal khaliƙin"._ na faɗa a zuciyata. sai dai kuma kan na kai ga ɗauke idona akan hoton ƙirjina ya buga dummm, hakan yasa na murza idanu ina ƙara kallon hoton da kyau kamin wata faɗuwar gaba ta musamman ta riskeni. na sauke idona daga kan hoton kamin su ƙara tsayawa akan ƙatuwar calender ɗin dake gefena, ina daɗa kallon fuskar hoton na tsawon wasu daƙiƙu kamin na tsayar da tunanina akan abunda ke wucewa ta cikin kaina. ƙwarai na san wannan fuskar, na santa farin sani, nayi mata sanin da zanenta ba zai taɓa ɗaukewa a idona ba, to amma mene alaƙarta da mamallakin wannan ofishin?, tukunna ma wannan sunan d
🏠