NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 52 of 98

zana last papper, kwana nayi ban runtsa ba ina karatu da nafila, amma fa a hakan sai da muka yiwa Gwaggo dabara tukunna, saboda tuni ta hanani karatun cikin dare, Yaya Abba ne ya sayo maganin bacci muka sa mata a lemu ta kwankwaɗe gashi har gari ya waye sai sharar baccinta ta ke. Allah sarki Yaya Abbana abin ƙaunata, kamar yanda naga rana naga dare haka shima ya gani, da daddare da Gwaggo zata kulle ƙofa ya ɓuya ga bayan labule, bayan ta wuce ɗaki ya fito, nima ko da na wuce kwanciya sai dana tabbatar tayi bacci kana na fito parlo muka hau karatu ni da shi, kamar shima exams ɗin zaiyi. Shap-shap nayi wanka na fito, ko mai ban tsaya shafawa saboda bani da lokacin wannan, mayafinma a bai-bai na yafa, sai dana fito Yaya Abba ya gyara min, shi yace zai taimaka yau ya kaini, da zamu fita muna jiyo ƙira'ar Yaya Haidar na tashi a masallacin cikin gida, na kirashi a waya nace idan ya idar ya sani a adu'a, yace "toh, Allah ya bada sa'a". Ƙarfe takwas dai-dai muka shiga ɗakin jarabawa, ba ƙaramin tsaro aka sa mana, duk an tarwatsa mu, wannan course ko bala'i, Allah dai ya bamu ikon hayewa, tun ba'a fara ba sai haɗa zufa muke, kwanciyata nayi kamin a raba peppers, har bacci ya fara ɗaukata, ganin Malamarmu ta taho da sauri Intisar ta dokoni, dama tazarmu da ita 1seat ne. Na farka a gigice na miƙe zaune, "masha'Allahu". wannan kalmar ko da yaushe ita nake furtawa a duk sanda nai tozali da Malama Muhsinah, ta ko'ina bata da makusa matar nan sai dai ban sa ni ba ko a halinta, amma iyakar kyawun halitta Allah ya bata, farinta tamkar wani madara-madara haka yake, amma a duk sanda nake zuzuta kyawunta sai Instisar tace wallahi na fita kyau, ko da yake dama ance wai mutum bai ganin kyawunsa, nayi dariya kawai idan naga tana ɓata rai ita alalle ba zance banda kyau ba. Inda nake Malama Muhisina ta ƙaraso, "get up". Shine abinda tace min, na miƙe, tace, "follow me". Na kwashi kayan rubutuna nabi bayanta, seat ta sauya mini ta maidani front seat, har wani lokaci ba'azo an raba mana script ba, nasa biro a bakina ina kallon wani bawan Allah dake zaune kan wheelchair a saman stage, ya juya baya baka ganin fuskarsa, Allah sarki ya bani tausayi sosai, shi kuma tasa jarabawar kenan, _Allah ka barmu da lafiyarmu, Alhamdulillah._ na faɗa a cikin zuciyata. Script aka fara raba mana, gabana ya faɗi, na runtse ido ina karanto wasu ayoyi da Baba ya bani, har aka gama raba mana questions pepper, kun san dai yanda ake tsintar kai a lokacin da aka shiga ɗakin jarabawa idan aka miƙo takardar tambaya musamman ma ace na course mai wuya ne, wani murmushin jin daɗi na saki da naga tambayoyin duk na sansu, aiko inata faman murmushi na duƙa kai na fara amsawa, cikin awa guda da farawarmu wasu suka fara submitting, kuma ni ce ta kusan 6 a gamawa. Ina sakkowa daga steps naji a jikina ana kallona, don koya aka ƙura min ido bada sanina ba sai naji a jikina, na ɗan dakata da saukar ina yatsine fuska, Supervisor namu naji ya doka min tsawa, "hey my friend what are you still waiting there?". Na tura baki gaba naci gaba da sauka ina murguɗa baki, na san dai koma wane mai kallona ya gani, ni ban son saka ido, dan bana buƙatar sanin koma wane dana ɗago na banka harara. Na ƙarasa na miƙawa Malama Muhsina script ɗin, har nai gaba naji ta kirani, na dawo tsna cewa da ni, "are you stupid?". na ɗago ina kallonta, tana nuna min script ɗin ta ke cewa, "what about your name and regestration number?". *Please Comment, Vote and Share.*[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(16)* ban ko bi ta kan Malama Muhsina dake bina da banzan kallo ba, abunda ya dameni shi ya damen, dan haka a wannan lokacin dafe goshi nayi cikin fargabar abunda ka iya faruwa da ace basu lura da rashin rubuta sunana ba. wallah shaf ni na manta da batun suna saboda zumuɗin fara ansering, daɗin question ɗin ya mantar da ni. na bawa Malama Muhsina haƙuri na amshi script ɗin na duƙa ina rubutawa, haka kawai sai na tsinci gabana da faɗuwa a lokacin, ga kallon da ake min ya tsananta yawa, naja tsaki ni ɗaya, sannan na ɗaga kaina sama nai harare-harare da murguɗe-murguɗe, yanzu kam dai koma wane nasan ya gani ya kuma san da shi nake, sannan na ɗago na miƙa mata. "your ID card". Ta ƙara cewa da ni, na miƙa mata ta duba abinda zata duba ta bani na wuce na fita. A ƙofar class na tsaya jiran Intisar, babu daɗewa itama ta fito, hangoni yasata ta fara dariyar dake ƙunshe da murna, tana ƙarasowa muka tafa da ita, exams dai tayi mana daɗi gaba ɗayanmu, muna tattaunawa akan wata question sai ga wata ƙawarmu ƴar carryover ta fito, muka jera muna tafiya. Intisar tace, " kallah wani bawan Allah, Allah ya bashi kyau sai dai babu ƙafa". Muka juyo ni da Rahinat don kallon mutumin da take magana akai, ana tura shi a kekensa na guragu, har sun wucemu, kamar ɗazu dai bayansa kawai na gani, da tausayawa nace,"Allah sarki wallahi nima ya bani tausayi, har ƙwalla sai dana masa ɗazu, kamar shine muka yi exams tare ko?". Na faɗa
🏠