banza. Yauma kamar kullum nasa littafi a gaba ina karatu, kawai naga an ɗauke shi daga gabana, ina ɗagowa na kalla Gwaggo tsaye ta ɓata rai, tana min faɗa tace, "tashi kije ki kwanta ki matse idonki, kar ki soma farkawa sai na zo na tasheki, wallahi idan ba haka ba sai na ɓata miki rai". Zanyi gaddama naga babu fuskar hakan, na miƙe na wuce ina faman buga ƙafafu a ƙasa, ina ji tana ta faɗin,"ƙarshen buga ƙafa ki fasa tiles ɗin ki faɗa ciki, haba Mutum idan ba so yake ya haukace ba wannan karatun ai yayi yawa, tun takwas kike anan a zaune ga ƙarfe ɗaya na neman kawo kai, duk kinbi kin wani sukurkurce kamar ba ke ba, ƙashi kamar kayi magana su amsa maka, ɗan kumatun nan naki babu shi, su kansu dukiyar fulanin naki sun rame, yo to ni ai ba mahaukaciya bace da zan barki kina lalacewa ba, nifa idan ma babu dole wannan karatu sai ki barshi, tun farko da nasan haka yake ba za ki soma ba, iya wanda kika samu a baya Allah ya amfana". taja tsaki ta ƙarasa wurin Yaya Abba, tana zama kusa da shi tace, "kai kira min Babanku, kace masa idan zai taho ya taho min da tsire irin wanda yaji ƙuli a jiki sosai, Ita kuma Sabina ya sayo mata kaza mai nagartaccen haɗi da kuma youghrt shima mai kyau, ya haɗo da kayan marmari ma namu ya ƙare". Ya ɗago ya ƙura mata ido yana kallonta, jin yayi shiru ta waigo daga kallon tv ta kalleshi, "to abinda na faɗa ne ba dai-dai ba dana zama abar kallo, ko kuma ƙa ƙa?". yace,"a'a Gwaggo, ke da kuɗin ɗanki, duk wani faɗi tashi fa kece kika yi a kansa har ya samu ya kai wannan matsayi, don haka ko garin Abuja kike son ci gaba ɗaya ai dole ya saya maki". Ta masa kallo mai kama da harara ta ɗauke kai, "to aini ba Gara bace da zan kama cin gine-gine, idan zaka kira min shi ka kirawo shi, idan kuma baka iyawa na tashi naje na sami Haidar ya kira min shi, tunda shi yanzu sai dai na taka ƙafata naje inda yake, ban kai matsayin da zai zo wurina ba, sam yaron nan baya girmamani". Abba ya fashe da dariya, bayan itace ta kora Haidar da muciya tace idan ya kuma zuwa inda take saita mummuƙa masa muciya aka, ta gaji da zuwan da yake yana mata dafe-dafe a kitchen, kuma tunda ta kore shi ɗin ya daina zuwa, tana cewa ta sami lafiya amma kullum zancenta ina Haidar, har zuwa ɗakinsu ta ke ta gani ko yana lafiya, shi kuwa yay biris da ita ko a compound suka haɗu ɗauke kai yake. Abba ya zura hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa, sai bayan daya kira Baba yake roƙon Gwaggo akan don Allah ta barni nake karatun nan, hutun yana gaba yayin dana gama exams, yanzu jarabawa ce zamu fara dole take ganina ko da yaushe akan littafi, kuma hakan shine dai-dai, dole sai na dage zan cimma nasara. "sai na barta jikinta ya lalace saboda ba kai zaka aureta ba ko, mtswww ni karka ɓata min rai Abba. Akan wannan karatu yarinyar nan ko lokacina bata da shi, to yanzu dai na ware masa lokacinsa, ba zan ɗauka ba, kuma fa karatun nata lissafi ne naji Zahra'u na faɗa, tace har hauka yana sanya mutum, ta kwatanta min da ƙanenta tace idan na ganshi ai zan lura bai cika hankali ba, to itama haka kake so ta zama? ko da yake kai dama ba ƙaunarta kake ba, aikinka shine kasata gaba kana faman tayata dukan wannan abar ta lissafi sai kace za ku ƙirge kuɗin duniya". Baice mata komai ba sai dariya da yake ƙasa-ƙasa, sababin Gwaggo na saka shi nishaɗi, idan ta fara magana baka ce zata yi shiru ba, taita jera zance kenan. a ƙufule tace da shi, "nifa kasan Allah na tsani ina magana naga ana min dariya kamar anga sha uku-sha uku, abin yana ƙonan zuciya, wannan yana ɗaya daga cikin abinda ya taɓa haɗani da wani saurayina nace na fasa aurensa, Sahibina shima wataran haka ya taɓa min, na kuwa doka yaji na wuce gidan Kakanni na, sai daya sha fama kamin na dawo". Yanzuma dariyar yay ba tare daya bari ta lura ba, ya miƙe ƙafa ya kwantar da kansa saman cinyarta, tana shafa sumar kansa take faɗin, "Abba ya kamata ka aske wannan sumar taka haka kaji ko, haba tayi yawa ai, gashi sai kace bana ɗan musulmi ba". "tom Hajiya Gwaggo". Yace da ita. saiga hawaye ya shiga sauka saman kuncinsa, hankalinta ya ɗaga ta shiga tambayarsa ko lafiya, yay shiru baice mata komai ba, itama saita fashe da kukan, ganin haka yace, "Gwaggo ina kewan mahaifiyata ne fa". Ya faɗa yana sa hannu ya goge mata hawaye. Ta mayar da shi saman cinyar tata, tana shafa kansa,
"kayi haƙuri Abba, Allah ya jiƙanta da rahma kai kuma ya haɗaka da abokiyar zama ta gari wadda zata dinga ɗebe maka kewa". Ta kuma fashewa da sabon kuka, "yanzu haka dole nima wataran zan tafi na barku, mutuwa rigar kowa ce. Allah ya bamu cikawa da imani ya kuma nufe ni da ganin aurenku, ina son Allah ya ara min rai da lafiya naga hannun waɗanda zan damƙa ku". Ya miƙe zaune ya riƙe hannunta, "insha'Allahu Gwaggo za kiga aurenmu har da ƴaƴanmu, duk da mutuwa bata barin wani don wani yaji daɗi amma ai ta bar mana ke tunda ta ɗauke mana Mama, so ki bar kuka don Allah kar Sabina ta jiyoki". Hakan daya ce tai saurin sa hannu tana sha re hawayenta.
*****
Yaune zamu