NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 50 of 98

Captain da suke shigowa ciki tare da Sajent ta ratsa cikin kunnensa. "Yallaɓai duk wani bincike da ya kamata muyi munyi shi. kuma har yanzu abu guda muke samu, irin bayanin da yake fita daga bakinsa...ƙwarai ba shi da alaƙa da kano, haka kuma mun kasa gano daga wacce ƙasa ko kuma garin daya fito har ya shigo nan. abunda yafi ɗaure kai shine rashin sanin sunansa kaman yanda shi kansa yake faɗa". Sajent jin bayanan Captain yake har sanda ya sami kujera ya zauna, kujerar dake fuskantar Alhussain. "me yasa ba zaka yarda ka ansa wannan laifin ba?". Sajent ya jefa tambayar ga Alhussain wanda kansa ke ƙasa. "saboda bani na aikata ba". ya bashi amsar kai tsaye, kuma ba tare daya jira ƙara cewar Sajent ɗin ba yace. "inaji zan iya ansar wani laifin da ƙaddara zata ɗora min shi, amma banda laifin aikata fyaɗe. bani nayi ba, dan haka babu dalilin da zaisa na amsa cewar ni na aikata. dan haka zaifi muku kyau ku kashe ni ko kuma ku bar wahalar da kanku akan tambayata kuyi abunda ya dace". shirunsa ya haɗe da dukan da Captain ya bashi a gadon baya da gwiwar ƙafarsa, hakan yasa shi saƙin wata azababbiyar ƙara tare da ambaton sunan Allah. "ka yarda kai kayiwa Yarinyar nan fyaɗe, ka yarda kai kayi mata fyaɗe kuma baka ƙyaleta ba har saida ta mutu". "ba zan yarda ba tunda bani nayi ba". "idan ba kai kayi ba to waye yi?". "nima ban sani ba, Allah shine masani". "amma me yasa aka sami gawarta acikin kangon da kake zama? bayan jama'a sun bada shaidar kai kaɗai ne kake rayuwa acikin wannan kangon". "wataƙila Ubangiji ya jarabceni ne da wannan jarabawar saboda ta kawo sauyin wannan ƙaddarar dake ɗaure da rayuwata...jikina na bani cewar rayuwata zata sauya silar wannan jarabawar". Sajent yay wni murmushi yace, "ba fa zamu taɓa yarda da kai ba...duk da cewar likitoci sun bamu tabbacin babu semen ɗinka ajikin yarinyar amma hakan bashi zai wanke ka daga wannan laifin na fyaɗe ba". Alhussain ya rufe ido hoton abunda ya faru a wancan lokacin na haskawa a duhun idonsa. bayan ya raka Sabina ya wuce masallaci, bai dawo ba sai gefin magriba, kuma yana zuwa kai tsaye ya shige cikin kangon don ya samu ya kwanta kasancewar kansa da yaji yana masa ciwo sosai. ya tuɓe rigarsa ya saƙaleta a jikin garun wajen kawai sai yaji jiniyar motar ƴan sanda, bai kawo komai a ransa ba ya wuce ya shiga zuwa ɗaya ɓangaren dake cikin kangon, inda yana shiga yay tozali da budurwar yarinya kwance shememe acikin jini, tsoro da firgici suka sa shi ya razana yaja da baya yana zazzare ido. bai taɓa gani ba, a baki kawai ya san kalmar ta Fyaɗe!. sanda yay yunƙurin saurin fitowa lokacin ƴan sanda suka faɗo ciki, aikuwa nan da nan suka saita shi da bindiga suna faɗin hannu sama, ta ke anan yaji duniyar na juyawa da shi sannan ta tsayar da komai nasa ya tsaya cak, haka ƙwayar idonsa ta komai kan yarinyar. wani ɗan sanda yazo ya wuce ta gabansa ya durƙusa ya ɗauki wayar yarinyar dake yashe a gun, wadda ta bin lokacation ɗin wayar ne ya kawosu gurin. kuma duba da yanayinsa wanda yake daga shi sai gajeren wando yasa ƴan sanda taso shi ƙeyarsa aka sa shi a mota aka taho da shi nan. "kanata wahalar da hukuma. ka faɗa mana gaskiya ka hutawa kanka haka muma ka sawwaƙa mana". Maganar Sajent da dukan day kawo masa na kulki suka baro shi daga duniyar tunanin daya tafi. "har yanzu amar guda ɗaya ce a wurina shine bani na nai fyaɗen ba, haka ban san ya akayi komai ya kasance ba". kuma buɗar bakin Sajent zaiyi managana wani ɗan sanda ya faɗo cikin cell ɗin yana faɗin, "Ranka ya daɗe ɗaya daga cikin waɗanda suka aikata laifin Fyaɗen nan ya kawo kansa...yace shi yaron Alhaji Musbahu Wasai ne". jin hakan yasa Sajent saurin miƙewa suka fita daga cikin cell ɗin cikin hanzari. yayinda Alhussain yabi bayansu da kallo, zuciyarsa na wucewa da wani abu mai kama da sanyi. *Bayan Wata Biyu.* To alhamdulillahi karatunmu na ta tafiya yanda ya kamata, kuma na raba ƙawance da Asma'u saboda ita shirme ne ta sanya a gaba, na samu sabuwar ƙawa mai hazaƙa da ƙwazo kamar ni muka ɗinke da ita, sosai nake jin daɗin harka da Intisar, saboda yarinyar akwai hankali da natsuwa, ita ɗin ce dai-dai da ra'ayina. sosai na maida hankali a karatuna babu wasa, Yaya Abba da Yaya Haidar ƙwarai matuƙa suke taimaka min akan abinda ban gane ba, dama ga shi ni tun a secondry school sarkin read ahead ce, yanzun ma haka ta ke, ko ajikina dan Malami ya shigo yace zaiyi unexpected test saboda bani da shakku akan abinda zan rubuta, karatu ne nake wanda babu dare babu rana shi yasa komai ke zuwar min cikin sauƙi. Gwaggo tayi ta bambami tana takaici, "karatun da bana Allah da Annabi ba a dinga bauta masa, yo ina kuwa jiki zai yi kyan gani, gaki nan duk kin bi kin ƙare kamar ragowar yaƙi". Ni dai bana ce ma ta komai sai dai nayi murmushi, mafi akasari ma Yaya Abba ke bata amsa idan yana kusa, yay dariya yace, "to ai Gwaggo karatun ita zaima amfani ke kuma kiji daɗinsa". sai tayi masa kallo mai harara, idan taso ta bashi amsa idan bata ba so ba tayi masa
🏠