ggo". kuka ta ke yi sosai a sa'ilin, kuma har ga Allah maganartata na ƙara ƙarfin iskar guguwar dake wucewa ta kacikin ƙoƙon kaina ne. sai dai cikin lokacin da ba zai haura sakanni takwas ba na manta da halin da nake ciki da duk wani abu da naji yana damuna, hatta hanzarin miƙewar da nayi ban san nayi ba dalilin jin Farhana tana cewa da shi. "ina zaka je? ina zaka tafi? kasan Allah ka ƙara ɗaga ƙafarka daga nan saina yi maka ihu, kazo ka sakar min ƴar'uwa dan nasan koma menene kaine sila". duk da cewar ba sosai nake gani ba, amma a taku biyu na cimma inda yake tsaye, kuma ban manta da wannan kama hannun nasa da nayi ba gudun kar ya tafi ya kai kansa wajen da zaici gaba da cutuwa, hakan zuciyata ke ce min, "barinsa nan wurin zai kai kansa ne inda yafi nan muni". shi yasa komai zai ƙara faruwa dani ba zan sakesa ba, ko da ace zan dawwama anan babu tafiya. amma ga wani maɗaukakin mamakin da al'ajabi, damƙar hannunsa da nai sai kawai naji komai na washewa, ciwon yana tafiya, komai na janyewa, kuma a hankali komai ya tsaya cak, kamin ya tafi gaba ɗaya. sai naji ni nayi sanyi ƙalau, haka kuma wani abu da ban san menene ba na tsargawa a jikina. na buɗe ido ina dubansa, yana nan dai tsaye a wurin, kenan tun a ɗazun bai motsa ba, sai dai wannan karan hannayensa duka biyun na zuɓe ne cikin aljihun wandonsa. sai kawai na ƙara kamo hannun nasa a haka naci gaba da jansa,kuma a yanzu bai min gardama ba, bai yi yunƙurin ƙwacewa ba, kawai bina yake kaman yaron dake bin uwarsa. ni kuwa ƙara saurin tafiyarmu nake dan mu bar cikin bolar da wuri, saboda zuciyata faɗa min kawai ta ke karki tafi ki barshi nan, sai dai komai zai faru ya faru dake. gaba ɗaya na manta ma da wata Farhana sai dana jiyota tana faɗin, "Allah kayi min maganin abunda ke neman yafi ƙarfina...yanzu da kike janshi ina za ki da shi?". ba tare dana tsaya daga tafiyar ba ko kuma na juyo nace da ita. "tare zamu tafi. bana son zamansa anan". "Allah uwar da ta haife shi". sai kuma ta ƙara da cewa,"amma dai kinyi hauka ko Sabina? ba ki san mutum ba, ba ki san shi ɗin ko aljani ne ba, ko kuma macuci kawai dan ɗebarwa kai masifa da nemarwa kai jaraba shine kika wani kama zuwa inda yake harda ƙarfin halin riƙo hannunsa za ki tafi da shi, to ki kai shi gidan uban wa uwar masu son taimako ta duniya...yanzu wannan ɗan wiwin har ina dalilin da za'a taimake shi". "kenan Farhana kawai idan mutum ya tsinci kansa a irin wannan halin sai aƙi danganta hakan da jarabawar rayuwa? saboda hakan kuma sai aƙi taimakon mutum?". na faɗa ina tsareta da ido a sanda na tsaya da tafiyar. "oho ni bance haka ba amma wannan dai ai baiyi kama da wanda za'ace ƙaddara ce tasa shi shiga wannan yanayin ba...dan haka kawai ki sake shi mu tafi, karki so ki tona zuciyata kiga takaicin da ke ciki". "ohhh Farhana ki fahimce ni mana, duk abinda zaka yi kayi shi don Allah kuma zuciya a tsarkake, wataran baka san ta inda za'a taimake ka ba kaima. Nifa kawai na tausaya masa ne, naga kuma bai dace muna ganin halin da yake ciki ba mu tafi mu barshi a haka. Yanzu tafiya zamu yi da shi sai mu sauke shi a gidansu". ta galla min harara tana faɗin,"mtswww ƴan wiwi nawa ki kai arba da su ba ki taɓa yunƙurin taimaka musu ba sai akan wannan mahaukacin". kuma furucinta na ƙarshe ya tsaida ƙafafuna, na rufe ido kaɗan sannan na buɗe, magana nake so na yaɓa ma ta, amma ba zan iya ba, bata cancanci hakan daga gareni ba, kuma hakan ba halina ba ne sam. sai kawai na kaɗa kai da cewar,"su sauran basu yi kama da waɗanda suke biɗar a taimaki rayuwarsu ba ne shiyasa kika kalla banyi hakan ba. shi kuwa sai dai idan idon mara imani ne ya sauka akansa, amma a hoton fuskarsa na farko daka kalla zaka shaida ɗan adam ne da yake cikin wata jarabawar rayuwa, ki kalla ƙwayar idonsa da kyau ki gani, ita kaɗai me shaida miki halin ƙuncin da yake ciki ne, balle shi yanda ba ki ɗaya abunda ke zuciyarsa ya bayyana a saman fuskarsa...Farhana ko kaffara ba zanyi miki ba mutumin nan yana da ciwo a tare da shi, wannan ciwon na damuwa da yake roƙon Allah dare da rana ya magance mishi, kuma wataƙila Allah ya sakoni cikin rayuwarsa dan na zama sila...shi yasa ko dana ganshi naji ba zan iya yin yanda kike so ba...so please lets go, i beg you". ganinta nai kawai ta wuce ta gabanmu bakinta na faɗin,"tabɗijam, ko duniya za'a tasa tafiya da wannan ɗan wiwin ba'a motata ba, don babu abinda zai sanya ni yayibar mahaukaci na kama tafiya da shi, ai yasan da gidan nasu yazo ya zauna anan....mtswww ke da kin kalla ma fa kinga alamun rashin lafiya a tare da shi, saboda haka kinga tafiyata". "kece ki ke masa kallon mara lafiya amma ƙalau ya ke kamar yanda muke". "a'a ba dai kamar ni ba kam, me lafiya dai ba zai zo kusa da bola ya zauna ba har yana shan sigari. Ai da gani kin san waye, cikin biyun dole ɗaya, mahaukaci ko kuma riƙaƙƙen ɗan daba, ki sake kallonsa da nazari tukunna ki dube yanayinsa da idon fahimta". ta ƙarasa faɗa tana nuna shi da baki a yatsine. Kallon Farhana kawai yake yana gani