nar, yayinda fuskarsa ke ɗauke da tsananin ɓacin rai da kuma tashin hankali. wannan tashin hankalin daya sameshi tun a ranar da aka sami gawar ƴarsa da aka yiwa fyaɗe. Officer ya sauke numfashi sannan ya koma baya ya jingina daga jikin kujerarsa dake juyawa da shi gefe zuwa gefe. biron dake riƙe a hannunsa a saman leɓensa yay shiru yana nazari, tsawon wucewar daƙiƙa uku tukunna ya sake sauke numfashi ya fuskanci Alhaji Musbahu Wasai yace da shi,"Alhaji karfa ka manta har yanzu bamu da wata ƙwaƙwƙwarar hujjar da zamu tura wannan yaron kotu, zarginsa kawai muke, har yanzu bamu tabbatar ba". Alhaji Musbahu Wasai ya taso masa sama acikin muryar faɗa yana cewa,"Officer babu wani batun zargi anan. akwai wata hujja da za'a samu ne bayan wacce muka da ita?...sai dai kuma idan wanda yay wannan aika-aikar ne ya biya...". bai kai ga ƙarasa maganar ba Officer ya ɗaga masa hannu. "Alhaji ba'a ɗakin matarka kake ba, saboda haka ka iya bakinka anan wurin". sai kuma shiru ya sake ratsa ofishin gaba ɗaya na wucewar wasu sakanni. kamin daga bisani Officer ya ɗaga waya ya kira, cikin daƙiƙar da ba zata haura ɗaya ba Corporal Murshid ya shigo, tsaye daga gefen table ɗin Officer ya sara masa, sannan muryar Officer ta fito cikin bada umarni. "Corporal". "yes Sir". "kaje ka faɗawa Sergeant a ƙara komawa kan yaron nan. ayi duk yanda za'ai musami abunda muke so ayau ɗin nan". Corporal ya ƙara sarawa yana cewa,"Oak Sir". daga hakan ya juya ya buɗe ƙofa ya fita. Officer ya kalli Alhaji Musbahu yace,"kai kuma kaje zamu nemeka...sai dai abunda nake so kayi keeping a mind ɗinka shine, hukuma bata gudar da aikinta ta irin tsarinka...mun san abunda muke, mun kuma san abunda ya dace...i hope you get me". Alhaji Musbahu bai ce komai ba ya miƙe tsaye yana bin Officer da wani irin kallo sannan ya taka ya wuce zai fita, sai daya je bakin ƙofa maganar Officer ta dakatar da shi. "ina fatan kasan inda ka kawo case ɗinka, Bompai!". Alhaji Musbahu ya jijjiga kansa kawai sannan ya buɗe ƙofar ya fice.
*9:30pm, cikin Cell.*
kansa duƙe yake a ƙasa, yayinda hannayensa ke riƙe da kumburarriyar ƙafarsa, ciwon dake saman goshinsa na zubar da jini kaɗan-kaɗan. yaja dogon numfashi ya sauke tare da rumtse idonsa sakamakon zafin ciwukan dake ratsa ilahirin jikinsa. _"Ya Rahman ka kawo min agaji, ka kawo min ɗauki, ubangiji ka wanke ni daga wannan laifin da ake zargina da shi. Allah ka bani ikon cinye wannan jarabawar"._ zafin ciwon dake kafaɗarsa yasa shi ƙara rumtse ido sosai, wanda ya tabbata idan ba karaya bace to ya sami targaɗan ƙashi. _"Ya hayyu ya qayyum"_ itace kalmar da yake ta nanatawa a fili har zuwa lokacin daya fara samun sassaucin zafin ciwon. sannan ya ɗago da kansa ya jinginar jikin bango yana sauke numfashi a hankali a hankali.
kuma lokaci ɗaya hoton Sabina ya shiga haska masa acikin ƙwayar idonsa, maganganunta kuma na waccen ranar suma suka haska a kansa, ranar data zama ta ƙarshe daya gargaɗeta akan karta ƙara zuwa inda yake, har yay mata rakiya zuwa titi ta hau mota. a dawowarsa, mazauninsa inda yake rayuwa, wata sabuwar ƙaddarar da zai iya kiranta da mafi muni ta kama ƙafarsa, kuma bata sake shi ba har sai data kawo shi nan, cikin wannan cell ɗin da kwanaki ashirin da biyar kenan yana cikinsa, ba zaman daɗi ba, zama na wahala da uƙuba, zaman da a kullum yake cewa inama mutuwa tazo ta ɗauke shi. sai dai a kullum abu guda zuciyarsa ke faɗa masa, ba zaka mutu yanzu ba, ba zaka mutu ba Alhussain har sai gaskiya tayi halinta, ba zaka mutu ba har sai ka fita daga wannan zargin. lokaci ɗaya yaji wani abu da bai san menene shi ba ya wuce ta maƙogoronsa, yayinda Sabina ta tsaya masa a ƙirji ta tokare wucewar komai ta wurin. ya sani! ya san cewar zuciyarta me kyau ce tun kamin ya kai ga kallon kyawun surar dake saman fuskarta...wataƙila ta sake komawa wurinsa tunda bata jin magana, duk da jikinsa na bashi cewar ta koma ɗin fiye da yanda yake lissafawa...tunda yazo nan hankalinsa da tunaninsa suna kanta, suna kan zuwanta wurin zamansa daya zame masa baƙar ƙaddara, yana tsoro, a tsorace yake sosai, shi yasa tunanin halin da take ciki ya kasa barin ruhinsa da gangar jikinsa gaba ɗaya.
ya sake kulle idonsa gam sannan yaja wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke, cikin ransa yana adu'ar. _"Ya Allah ka kula da ita, ka tsareta daga dukkan wani abun cutarwa"._
kuma buɗe ƙofar cell ɗin daya ji anayi yasa komai dake cikin kansa ya tsaya cak, illa bugun zuciyarsa daya ƙaru sosai. har yanzu ya kasa sabawa da wannan horon da akeyi masa, bai kuma san ranar da zai saba da shi ba. abu guda ɗaya ne kawai yake anan, a duk sanda yake ansar wani tsatstsauran hukunci, ya kanji yana samun sauƙin abun idan yana ambatar sunan Allah, kuma ya kanji kamar zafin komai na yayewa ne ya zama kamar babu idan ya tunata, jikinsa yana bashi cewar zata zo ta goge komai, zata zo ta ɗauke shi, zata zo ta fitar da shi, wataƙila nan kusa ko da jimawa...amma da jimawar shi yake lissafawa kuma yake hangowa.
maganar