ep ya ƙarasa da ni. Yau na kuma yarda da cewan karatun university bana wasan yara bane, sai na tuna Farhana tah da idan ta dawo tana min complain nayita ce mata raguwa, ita dai bata son karatun ne kawai. Ashe abin ba haka yake ba, lectures uku muka yi ayau kuma duk masu zafi, Har sai dana ji dama ba Accounting na zaɓa ba. Ƙawar da nayi Asma'u tai dariya tana cemin, "to ce miki akayi sauran courses ɗin sauƙi gare su, kowanne da irin nasa wahalar, ke dai Allah ya bamu sa'a kawai". "kuma fa haka ne". Na faɗa ina zura sauran littafaina a jaka. Nace ma ta, "muje ko". Har titi muka zo ni da Asma'u, Anan ne muka rabu, ta hau mota ta wuce ni kuma na tsaya jiran wani, saboda hanyanmu ba ɗaya ba. Sai dana jima tsaye rana duk ta gama zane ni sannan na sami taxi na hau. A matuƙar gajiye na dawo gida, ina shiga parlo nai wurgi da jakata na haye kan kujera dan ko ɗaki bazan iya ƙarasawa ba, takalman ƙafata ma ban cire ba. "Lazy lazy".
Yaya Abba yace da ni cikin sigar tsokana. "Yaya Abba wallah ba wani zancen Lazyness, kaga wuyan da muka sha kuwa, Allah ya haɗamu da wani lecturer mara mutunci mugu harda mana test". "to yace ko kinyi abin arziƙi?". "ahh na rubuta masa abinda na iya, na bar masa wanda ban iya ba. Allah tun ƙwaƙwalwata na ɗaukar komai har nazo na daina kwashewa". "dagewa za kiyi yarinya. Karatun bana yara masu lalaci bane". Nai murmushi kawai na juya na gyara kwanciyata, kamar an tsikare ni na zabura na miƙe, na duba Yaya Haidar wanda ke kwance shima kan kujera, na sauko na buɗe jakata na ɗauko littafina na nufi wurinsa. "Yauwa Yaya Haidar kaine kayi Statistic, Please help me to solve this". Kamar bada shi nai maganar ba, "Yaya Haidar please mana". Ya kuma share ni. Na miƙe da sagaggiyar gwiwana zan tafi sai kuma yace, "lem me see". na dawo da ƴar murnata na miƙa masa yace, "i dey hear you; readout". ya faɗa ba tare daya dubi ko inda littafin yake ba balle ni. ina waro ido waje nace, "tabɗi ai bazan iya karantowa ba, wasu numbers ne fa a watsaltsale". sai ya saki wani Silent smiling, ya miƙe zauna ya amsa littafin yana dubawa. tamkar wanda na matsewa baki na masa dole haka yake magana, to ni me ma nake ji, shi ɗaya yake maganarsa a cikinsa, kuma nan wai bayani yake min yana aikin buga calculator, na kallesa na zabga masa harara kamar yana ganina, na haɗe girar sama da ƙasa na warce littafina na tashi na bar wurin nayi ɗakina, Gwaggo dake fitowa daga kitchen ta bini da kallon yanda nake ɓata rai ina jiran fashewa da kuka. Ta juya ta kalla Yaya Haidar daya koma yay kwanciyarsa, sannan ta kalla Yaya Abba wanda ke ɓaɓɓaka dariya ko akan mene oho, shi dai da wayarsa ne, tayi ƙwafa ta koma kitchen da plate ɗin abincinsu da zata kawo musu. Ta hau sababin. "yanzu fisabilillahi yarinyar daga dawowarta makaranta dan zalunci aka ɓata ma ta rai, ko hutawa fa ba'a barta tayi ba ta numfasa, kawai saboda ana Ma ta baƙin ciki, to mutum yaje shi da Allah dan ni dai ba yarda zanyi ba, kuma abincina ne ba zan bayar ba, aje wani wurin aci". Ta sawa kitchen ɗin ƙaton padlock ɗin da tace Baba ya sayo mata ɗazu, saboda Yaya Haidar daya ke zuwa yay mata ɓarna a ciki. Yaya Abba daya jita tana wannan sababi ya taso yana bata haƙuri, saboda shi baya wasa da cikinsa, akan abinci zai maka ladab iya ladab, Gwaggo ta masa wani kallo ta ɗauke kai. "kauce ni zan wuce".
"haba Gwaggo, bafa a wasa da yunwa, kina kallo har ƙarfe biyar bamu ci abincin rana ba, ni dai don Allah kiyi haƙuri ki bamu abincin nan. Waccan yarinyar babu abinda aka mata halinta ne kawai". "mtswww babu abinda aka mata zata zo ta wuce ni haka fuuu kamar tashin iska babu magana, ko fa sannu da gida bata yi min ba. Kuma sarai nasan kune kuka ɓata mata rai, dan wannan ba halinta bane na rashin kyautawa, saboda haka idan kana so na baku abinci kaje ka taso wancan mara kunyar yaron kuje ku sameta ku bata haƙuri, idan ta haƙura shikenan idan bata haƙura ba kuje wani wurin kuci". "please mana Gwaggo". Ya faɗa yana haɗa hannayensa. "please ɗin gidanku, dilla ni gafara min ina da abinyi, ai ni Abba kana bani mamaki, irin girmamawa da biyayyar da yarinyar nan ke maka wallahi sam bata cancanci wani abu ɓacin rai daga wurinka ba, a rayuwa bata da wani zance sai Yaya Abba, wanne kalar bauta ne bata maka ba, bini-bini tana cikin maka wanki da guga, har gajeran wandonka wankewa take, amma ka rasa da me zaka dinƙa saka mata sai dai ka taƙarƙare ka ɓata mata rai, babu batun sanyata farinciki. To kaje kowa dai yay na gari kansa". Ta ture shi ta wuce, taje ta ɗauke mayafina da jakata ta barsu anan da yunwarsu dan ta rantse ba zasu ci abincin ba.
*Please Vote, Comment and Share.*
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(15)*
*Kano, Bompai Police Station.*
*9:00pm, Officer Office.*
"wallahi ba zan yarda ba, kuma ba zan yafe ba, dan haka Officer kayi moving case ɗin nan zuwa court a gobe". Dattijon dake zaune kan kujerar dake fuskantar Officer Yahya Murtala ya faɗa, cikin hargowa yake maga