fito ba. Ni bana son kinibibi". ta faɗa tana wucewa ɗaki ta barni zaune anan, nafi minti goma zaune banga alaman Baba zai fito ba, hakan ya tabbatar min bata sanar masa da zuwana ba. Raina duk yay ba daɗi, na ɗauka wayana na kira Baba, ringing biyu kam ya ɗaga, yanayin da yaji muryana ya shiga tambayana ko lafiya. na kauda ɗacin dake ƙasan maƙoshina nace,"lafiya lau Baba, nazo wurinka ne kuma ban sameka a parlo ba". sai muryarsa ta far fita da sautin faɗa-faɗa. "a'a to wannan wane irin shirme ne, ba sai ki hauro saman ba. Tun yaushe kike nan a zaune?". Dan dai ban iya haɗa rigima ba da nace masa Anty tasan da zuwana, to amma saboda bana son ɓacin ran Baba kuma ni bana so naga ana fitina acikin gidan sai kawai nace masa,"tun ɗazu ne, kuma zan tafi school ne gashi harma na makara". "sorry my daughter gani nan bara na sakko". Ko minti biyu ba'a ƙara ba sai gashi ya sakko, ya zauna kan kujeran da nake, kaina na ƙasa yasa hannu ya ɗago da fuskana, ganin idona ya ciko ya ɗaga hankalinsa. "whats wrong?". Ya tambaye ni. na girgiza masa kai alaman ba komai. "no no ba kya min ƙarya fa". Ina goge guntun hawayen daya sakko min nace, "ban ganka bane". nai mas aƙaryar hakan, wanda a haƙiƙanin gaskiya a lokacin ina kewar mahaifiyata ne, sai Yay murmushin manyance yace, "rainon Gwaggo sarkin shagwaɓa, to yanzu gani me kike so?". Dai-dai lokacin da Anty ta ƙaraso da tea flask hannunta, ta aje kan dining sannan tazo ta zauna itama, tana murmushi ta ke ce min. "Ƴar gidan Babanta har an fito, yau za'a fara shiga makaranta ko, to Allah ya taimaka a maida hankali sosai kinji, banda wasa don Allah, abinda aka je yi shi kawai za'ayi". Tsabar mamaki kasa ce ma ta komai nayi, nai kamar ban jita ba don kar ma Baba yace wani abun. Nace da Baba, "dama zan wuce makaranta ne nace bari nazo na gaisheka". "oh yaune fa za ku fara taking lectures ko, eyyah sorry dear na ɓata maki lokaci". Ya zaro 2k a aljihu ya bani, na amsa ina sambaɗa masa adu'a da kuma godiya. Nace masa ko zaisa Yaya Abba ya kaini, idan naje yau naga yanda yanayin school ɗin namu sai na fara zuwa da nawa motan. Ya kira Yaya Abba a waya yace masa ai yanzu ya tashi ko wanka bai ba. "ina Haidar fa?". Ban san me Yaya Abba yace masa ba naji yace, "to kace masa ya fito ya kai Sabina makaranta, yay sauri tayi late". Mu kai Sallama da Baba na tashi zan tafi, Anty tace, "Sabina tsaya kisha tea mana nasan ba lallai kinyi break ba". "na ƙoshi". nace da ita ataƙaice. cike da ƙwaracewa na kissa tace, "a'a ni dai nasan ba ki ƙoshi ba, saboda ba ki ci komai ba tunda ban kai muku ba, ki daure kizo ki zauna ga plantain nan kici ko kaɗan ne, ba kya tafi makaranta a haka ba". Shi dai Baba wayarsa yake dannawa, ni kuwa mamakin kisisinarta nake. ta kuma cewa, "to ko na zuba miki a flask ne sai ki wuce da shi?". Ƙaramin tsoki naja, na ɗaga kai na jefa mata harara nai tafiyata. sai ga su Aisha sun shigo, suma jikinsu sanye da uniform, Zainab da Khadija ne kawai suka gaida ni, amma Aisha da Amina da suke ganinmu kai ɗaya kallo ɗaya suka mani suka ɗauke kai suka wuce inda Baba ke zaune. Kuɗin makaranta ya basu, ina ji kuma yana musu faɗan latti da suke kullum. Suka bashi haƙurin kan zasu daina. Aisha tace, "Baba yau Umma bata da lafiya tace ba zata iya kaimu ba, sai dai ko Anty ta taimaka mata ko kuma kasa Yaya Abba". Anty tayi karaf tace, "a'a ga Haidar nan zai kai Yayarku, sai ku tafi tare ya saukeku". Baba yace, "ehh hakan ma yayi, kuje Allah ya bada sa'a". A bakin mota muka tsaya muna jiran fitowarsa, ni dai kamar na haƙura da binsa na hau motana kawai na wuce, tun fa ɗazu Baba ya kirashi ko shirin me yakeyi ai yaci ace mun fito mun same shi ma yana jiranmu, kuma duk dan ni zai kai ne shi yasa yake wannan delay ɗin. "Yaya anya kuwa Yaya Haidar yana nan. Kalla fa morethan 5minutes muna tsaye nan muna jiransa bai zo ba. Ni kam yanzu ma nasan an rufe gate". Khadija ta faɗa kamar zata yi kuka, da yake itane autarmu. Har na taka ƙafana zan bar wurin sai gashi ya fito yana gyara zaman hularsa, fuskar nan a ɗaure babu alaman kawo wargi, sai wani takun ƙasaita yake kamar jinin sarauta, na taɓe baki na harari inda yake, ya ƙaraso ya buɗe motan, na buɗe da sauri na shiga. Ya duba su Aisha dake ƙoƙarin shiga yace, "ku kuma fa?". "Baba yace ka aje mu a hanya".
Amina ta bashi amsa, ya wurga musu harara ya shigo cikin fushi ya figi motar, Allah yasa na rufe ƙofar da ba abinda zai hanani faɗawa waje. su muka fara saukewa tukunna muka wuce tamu makarantar, sai daya raba tafiyar biyu naga yaja yay parking, ya kashe motar yana danna wayarsa, naga bashi da alamar ci gaba da tafiyar na kalle shi nace, "Yaya Haidar ya dai, ko wata matsalar ce ta sami motar?". Shiru yay min kamar bada shi nake ba, sai dana ƙara magana a karo na uku tukunna ya juyo a fusace yace, "Get out". Na tsaya ina kallonsa, zan kuma magana ya doka min tsawa, "ba za ki fita ba". Na buɗe motar na fice, dama jira yake ina fita ya figi motarsa ya buɗe ni da ƙura. Na samu na tari mai nap