hakan yasa yace, "an dafa a kitchen ɗin nata kuma baza'a bayar ba, bar min nan wuri ko kuma nayi ball da ke". Na miƙe na bar masa wurin, cikin raina ina faɗin mutum ba abinda ya iya sai shegen ci, tunda yazo gidan nan kamin kowa ya tashi zaka kalla ya tashi ya dafa abincinsa, kuma aikinsa kenan shan tea ko da rana ko da dare, sai kace wani balarabe. Kitchen na wuce na ɗora ruwan zafi, yana tafasa na sauke na dama curstad, na fito na wuce dining nayi zamana ina shan kayana, Gwaggo ta fito ta sameni, tana kallona ta fahimci akwai abunda akai min. dan haka ta dakata daga gyaran ɗaurin zane tace min, "ke kuma me aka maki kike faman ɓata rai da sanyin safiyar nan? duk daƙe dama uwar miskilanci ce, ko ba'a taɓa ki ba iskokanki zuwa ɗaukar fansa suke". Na aje cup ɗin na ture shi daga gabana, daga tashinta zata hauni da faɗan da baya ma ta wahala. Taja ƙaramin tsaki tai juyawarta zata bar wurin tana cewa, "ke dai kika sa ni da halin nurƙufancinki da baida kyau, tashi na kenan ban bawa cikina ba, ba za ki sa ni magana ba". Na fara shashsheƙar kukan ƙarya nace, "to ba Yaya Haidar ba ne". Cak ta tsaya ta juyo tana kallona, "aina kuka haɗu da Haidar ɗin har kika masa rashin kunya, ban hana ki shiga sabgarsa ba, ina ce na miki faɗan babu ruwanki da shi ko". "ni fa ba sabgarsa na shiga ba, shine don nace ya sammani tea yaƙi, kuma nace masa na makara a school amma duk da haka ya hanani yace zai zabga min mari, yace naje na taso Kakartawa tazo ta dafa min". a wani sukwane ta dawo da dubanta kaina gaba ɗaya. "to shi aina ya sami tea ɗin bayan su ba kitchen garesu ba, kuma dai matan gidan nan basu isa tashi ba bare ace sun dafa sun bashi". "anan fa yazo ya dafa, na fito zan wuce na gansa ya fito daga kitchen". ta jijjiga kai kamin tace,"shi Haidar ɗin wai? Kai wannan yaro akwai baƙin hali, ruwan shayin da zai sammaki ba wata tsiya ba, ɗan ƙwal uba ina ce ma arziƙin ubanki yazo yake ci. tukunna ma ban ce masa kar ya kuma zuwar min sashena bane". "to dai ai gashi can yana kallo". Ta juya ta nufa inda yake, tana zuwa ta ƙarasa gaban socket ta kashe tv ɗin da yake kallon news ɗin da bai gajiya, ni nama rasa uwar me yake ji da news ko da yaushe, yana ganinta baice mata komai ba haka itama bata kula shi ba. Sannan ta kirani, ina zuwa tace, "kashe min wannan na'urar sanyin". Na jawo ƙaramin table na ƙara tsayi na kashe. Ita kuma ta ƙarasa taje ta janye table ɗin da ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ƙafafunsa suka zube a ƙasa, ina kallon yanda ya cika yay fam ƙiris yake jira ya fashe, nasa hannu na toshe dariyar dake ƙoƙarin fitowa, tasa hannu a aljihun gaban rigarsa ta ciro handkerchf nasa sai tashin ƙamshi yake, ta shiga goge table ɗin daya ɗora ƙafafun nasa tana ta magana kamar bada shi take ba. "Haka kawai a dinga shigo maka wuri da sanyin safiya ko tashi baka yi ba ana takura maka. kuma ba taya aikin fari bare na baƙi, sai dai a hakimce a ware maka na'urar sanyi a kunna maka tv ana sauraren yaren da kai ba jinsa kake ba. Kuma Duk abi a zuba maka dattin ƙafa akan glass, ka yiwa mutum magana ya daina zuwar maka wuri amma saboda ba shida zuciya zuwa yaƙi ya daina, dole dai sai an saka magana, to na kashe kayayyakina kar na soma naji an ƙara kunna min kayan kallo". Maganar ta ke kamar bada shi ta ke ba, tana gamawa ta wurga masa hanky nasa. Ina dariya ƙasa-ƙasa naje kusa da shi na ɗauka mayafina da jaka ina cewa. "Gwaggo zan tafi, ai mana adu'a Allah yasa mu shiga a sa'a". "to kin ƙoshi ne? ko za ki sha shayi ga saura naji a cikin butar nan, ƙila wannan yaron ne ya dafa". Na kalla Yaya Haidar naga ya ɗago yay mata wani kallo, ran nan nasa a haɗe, kawai dan na makara ne amma ko dan na ƙara ƙular da shi da sai na sha, na cije Leɓena ina dariya nace. "a'a Gwaggo bana sha, na ƙoshi ai". "to shikenan yana da kyau na tambayeki ne. Saboda ni ba sha zanyi ba ƙarshe zubar da shi zanyi. ban san ma wane shishshigi ne yasa aka zo aka wani yimin girki a kitchen ba tun gari bai washe ba, kamar ka saka mutum, a dai dinga jin tsoron Allah almubazzaranci babu kyau. kuma wani abin dariya da takaicin kai ɗin dai da aka raina duk tsiya wurinka ake zuwa". ni dai kamar kar na tafi haka nake ji, idan kuga yanda Gwaggo ke magana zaku rantse da kanta ita ɗaya takeyi, saboda yanda ta nuna tamkar babu inuwar Yaya Haidar a wurin, shi kam ina da tabbacin a zuciyarsa ji yake inda ace yana da iko baiga me hana shi saka mata hannu ajiki ba. maganarta ta dawo dani daga tunanin sakanni biyun dana lula. "ki shige ki tafi Allah ya bada sa'a". na ansa da,"amin". Zan fita kenan Yaya Abba na shigowa, na gaida shi ya ansa min, ni kuma fice. Part ɗin Baba na wuce, Anty na samu a parlo tana jera masa kayan breakfast, ina zama kan kujera nake gaisheta, amma ƴar matar nan ko iskar da ta kwaso ni bata kalla ba bare nasa ran zata amsa min. nima na bawa banza ajiyarta, sai can dai dana ga zaman ba zai kai min ba nace da ita,"Anty ina Baba?". tace, "ba dai kinzo ɗakinsa ba, sai ki jira ki gani idan zai fito ko ba zai