NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 45 of 98

ɗin ka tambaye shi, anyi haka ko ba'ayi ba, tare ma mukaje koyon mota, kuma har yanzu ma muna zaune da su shida Yaya Abba babu abinda ya sameni. Ina jin dai ko Gwaggo ta fara rikicin tsufa ne, shine ta fara rikicewa ta kaina". Ta kalleni ta jijjiga kai, "to ai kaji, itama ta hau sahun waɗancan fitsararrun yaran, amma ba laifinta bane ita zan mata uzuri, tunda yanzu ta zama ba ita ɗaya ba, adu'a kawai zan bita da ita, idan na fahimci kuma sune sai na hauta da duka". Ta kalle ni tace, "ki sami damar yimin shiru, Allah yasa a gaban ubanki ne bare kija ace zane miki jiki nayi, kin ɓare baki kina kuka mara daɗin saurare, Kefa dama haka halinki yake wani zubin, sam-sam ba ki da daɗin sha'ani". na kuma fashewa da sabon kuka na miƙe zan bar wajen. "dawo". Tace da ni. Na koma na zauna ina jin kamar nayi me saboda baƙin ciki. "to yanzu Gwaggo mene abunyi?". Baba ya tambayeta. tace, "abunyi shine ka tattaro min kawunan Matanka suzo nan. Don ina tantama da wannan Al'amarin, ni dai ba aljanu ba, kai ba su ba, uwarta har ta mutu babu wata alama data nuna tana ɗauke da aljanu, kai kafatanin dangina ban samu labarin wanda ke ɗauke da su ba, kaga kuwa bana gado bane. Bugu da ƙari shekarar mu nawa a wancan gida kamin mu dawo nan, babu wata alama da taɓa nunawa tana da mutanen ɓoye sai da muka zo nan. To da sake a wannan lamarin, su zo idan acikinsu akwai mai su sai ka kwashe su daga gidan nan, kuje can kai musu magani idan sun warke sa dawo. Idan kuma ma wani mugun ƙullin aka ɗaura to azo a warware shi anan, don wallahi aka kuskura na gano ture ne akayiwa Jikata ba za'aji da daɗi ba". Baba yace, "To amma Gwaggo ai a cikinsu kaf babu mai aljanu". a harzuƙe tace, "shine ai nace maka ka kirasu suzo koma wace acikinsu, to ta kunce baƙin ƙullin da tayi tun wuri, dan billahillazi bani da kyau, ni gaskiya ce nake faɗa babu ruwana. Kar na ɗau mataki kai tsaye ace nayi rashin kyautawa...dan kai kanka ba zaka ji da daɗi ba". *Please Vote, Comment, and Share.* [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(14)* *Monday Morning.* kasancewar yau monday tushen aiki, kuma yau ɗin da izinin Allah zan fara ɗaukan lectures, dan haka tunda na kammala azkhar ɗina ban koma bacci ba shiri kawai na fara yi, kwalliya nayi sosai wanda ta ƙarɓe ni matuƙa musamman dana ɗora da medical glass ɗina, dama gani ƴar son kwalliya da ado, tabbas duk wanda ya kalle ni dole ya so kuma gani na. Tunda na fito parlo na kalla yanayinsa nasan Gwaggo bata tashi ba, saboda indai ta farka ta fito zata sa karatun ƙur'ani ta kuma saki turare. jakata da mayafina na aje kan kujera na wuce kitchen don samarwa kaina abinda zanci, dai-dai da zan shiga nayi karo da Yaya Haidar zai fito, da sauri naja baya nayi gefe a tsorace, Allah ya taimake ni ban tankwaɓar masa da tea cup ɗin dake hannunsa ba. Na murguɗa baki gefe don banda niyyar gaida shi, sai naji kamar na koma idan ya fita sai na dawo, sai wata zuciyar tace min kawai na tsaya na ƙara bashi hanyar wucewa, ina kallonsa ya wani haɗe rai yana jifana da harara, bai yi niyyar saurarena ba amma saboda neman magana yaja tsaki yana kallon kayan jikinsa kamar nayi masa ɓari a jiki. Ya ɗago ya kalle ni yana kuma hararata, ya ƙara jan tsaki yace, "ba kya gani ne da ba za ki iya lura da tahowar mutane ba". Na kalle shi kaɗan nace, "ai ban san da tahowan naka bane, kuma ina sauri ne". Tsaye yayi yana kallona ta ƙasan ido, "stupid girl". Ya faɗa yana ƙare min kallo ta ƙasan ido, ni dai zumɓuro baki nake ina alla-alla ya wuce, wayarsa ce tayi ƙara, ya ɗauka yana waya, sai daya gama wayar kana ya bar wajen, nabi bayansa da murguɗa baki. Ni dana shiga kitchen ɗin ma rasa me zan dafa nayi, na duba agogon dake saƙale a wurin, lokaci ƙara tafiya yake kuma yau tara ne zamu shiga lectures, ga time har takwas tayi, na doki ƙafa a ƙasa, ko me fa zan dafa sai yaja min lokaci tunda ni bacin Indomie nake ba, ko da tea ɗin zan dafa it will take time too, tunawa nayi da Yaya Haidar zai fita da tea Kettle a hannunsa, da sauri na suri cup da spoon, na zuba madara da bounvita da nescape na fita, ina zuwa kuwa na sa me shi kan kujera yana kurɓan shayinsa, naje gabansa na tsaya ina sosa gefen kunnena. Ya saci kallona ya ɗauke kai kamar bai ganni ba, na turo baki gaba na duƙa gaban table zan zuba tea a tsawace yace da ni,"kee". Na ɗago ina marairaice fuska nace, "Please Yaya Haidar, Makaranta zan tafi and idan nace i will wait to cook something i will be late. tea ɗin da yawa, barinsa ma za'ayi tunda Gwaggo is not drinking". Na faɗa ina ɗaga kettle ɗin na jijjiga naji yawansa. "wallah idan ba ki aje min kayana ba sai na zabge ki da mari, ke kika dafa min da za ki zo kice na ba ki, mara kunya kawai ana magana kina turowa mutane baki, me zai hana ki jira Kakar taki tazo ta dafa miki, ko kuma ni sa'an kine da zan dafa abu kici". ya faɗa yana ƙara tamke fuska. Na aje ina ƙunƙuni ina cewa, "to amma ai dai a kitchen ɗin Gwaggo tah aka dafa". Ashe ya jiyo ni,
🏠