NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 44 of 98

i, wanda shi kansa sai da yayi dana sanin abinda ya aikata. A tsawace cikin ɓacin rai tace da su, "ku tashi ku ɓace min daga gani". za su fita Baba ya shigo, Gwaggo tace,"yauwa ƙwara da Allah ya kawoka, tunda ni basa ganina da gashin ido bare suji maganata, kaja musu kunne kar su ƙara zuwar min ɓargarena tunda babu tsiyar da suke yi min, duk su biyun bana son sake ganinsu anan dai inda nake, suje can su ƙarata da halin su na rashin ƙwarai, dama ance abokin ɓarawo ɓarawo ne to abokin ɗan iska ma ɗan iska ne. Ko kwanon abinci sun daina ɗauka a wurina, idan zaka dinga basu kuɗin saya sai ka basu, idan ma da matanka zaka haɗasu ka haɗasu, kai idan ma aure zaka yi musu ku dai kuka jiyo kai da su, ni ba damuwata bace, babu ruwana, buƙatata dai a daina zuwa inda nake, idan ba haka ba kuma duk abinda nayiwa mutum shi yasa ya da kuɗinsa". Baba ya dube su yay musu kallon tsab, kansu yana ƙasa sun sunkuyar yace da su, "mahaifiyata ce fa, rashin kyautawar mai kuka yi mata?". Da sauri Gwaggo ta ɗaga masa hannu tana cewa, "n ifa bana buƙatar sulhu, su fita kawai kuma ka gaya musu karsu ƙara dawowa". "shikenan kun dai ji abinda tace, ku fara bata haƙuri kamin ku tafi". "Gwaggo kiyi haƙuri". Suka faɗa tare. tayi musu kallo mai harara, tana nuna Haidar da yatsa tace da Baba, "kai Auwalu wancan yaron idan aikinsa ba mai ƙarewa bane a kusa to ka nema masa wani gidan ya koma can da zama, bana son ganinsa a gidan saboda bashi da mutunci". Ƙaramin tsakin da Yaya Haidar yaja duk sai da muka jiyo, Baba ya juya zai masa magana yaga har ya fice, Gwaggo na jijjiga kai tace, "kagani ko, sam bashi da mutunci. Banda Allah yasa a gabanka ne da zagayowa zaiyi ya bangaje ni tukunna yasa ƙwalelen kansa ya fice. Ɗan banzan yaro mai kama da alkaki sam baiyi halin ƙwarai ba, shi Sulaimanun zai zo ya same ni, naji idan akan hanyar daya ɗora shi kenan". Baba ya nemi wuri ya zauna, nai masa sannu da zuwa, yana kallon yanayina yasan faɗan Gwaggo da su Yaya Abba akaina ne. Gaisheta yayi yay mata sannu da gida, "yauwa". ta ansa mishi. "ya aikin naka?". "Alhmdl". sai naji yana cewa, "Gwaggo tun ɗazu kika ɗaga hankalina, da kika kira kika ce akwai matsala nayi gaggawar tahowa, lafiya dai ko?". "tun a lokacin da na kiraka mai ya hanaka dawowa?". ta faɗa muryarta na nuna ɓacin rai. "kiyi haƙuri ko a lokacin mun riga mun shiga meeting ne, to naso tahowa sai kuma naji kince na kwantar da hankali na amma dai na dawo gida, jin haka nace ba babbar matsala bace har na kammala komai ma". "to dama akan Sabina ne". Na ɗago da sauri ina kallon Gwaggo, gabana na faɗuwa, to ni kuma ƴar gidan Gwaggo na mai nayi. Baba naji yace mata, "me Sabina ɗin tayi?". tace da shi, "kaji na taɓa kawo maka ƙararta ne da zaka tambaye ni me tayi, to ita bata laifi salahar baiwa ce, ka dai ce me ya faru da ita". Baba ya haɗiyi yawu yace, "to mai ya faru da ƴar lelen taki?". "aljanu ne da ita". "aljanu kuma Gwaggo". Baba ya faɗa yana zare ido, don maganar sosai ta dake shi. "ƙwarai kuwa, amma basu yi nasarar shigarta ba, sun dai shafeta ne, wancan fitsararran baƙon yaron shi yay mata ruƙiyya kasan Malami ne, ƙwaƙwalwarsa taf da haddar qur'ani amma babu tsoron Allah a zuciyarsa, amma haka dai na haɗashi da ita yay mata karatu da adu'oi, sannan ya fita cikin gaggawa yaje islamic chemist ya haɗo magunguna da turare aka haɗa mata, nan da nan cikin ikon Allah komai ya lafa. amma farko fellawa tayi da gudu, da ace babu mai gadi ma ba'asan inda zata nausa ba, nan ta faɗi tana aikin shure-shure da buge-buge da ife-ife. Ashe ajiye shirgegiyar mace ma acikin gida yana da amfani, don wannan ƙatuwar matar taka ita ta ɗaukota duk uban nauyin da suka sa Sabina tayi, don ni dana ɗaga hannunta ma banyi zaton hannun mutum na ɗaga ba...yau ai Ƙatuwar can tayi min rana". jin abunda ta ke cewa yasa na fashe da Kuka, gaba ɗayan su hankalinsu ya tattaro ya dawo gare ni, musamman ita da ta ke bada bayani. "me kuma aka yi miki?". ta jefo min tambaya. ina shashsheƙar kuka nace, "Gwaggo aljanu fa kike cewa ina da su, kinsan kuwa mene aljanu, na rantse ni lafiyata ƙalau". Wata harara ta jefa min kamin tace, "nufinki ƙatuwar mace da ni zan zauna ina gillawa ubanki ƙarya ne, to ribar mai zan samu idan nayi miki fatan wannan lalurar da ba'a so, mtswww shi yasa ɗazu nake gaya miki da ku masu aljanu da mahaukata ɗaya kuke, tunda duk bakwa sanin abinda kuka aikata a lokacin da kuke kan ciwo. To a faɗuwar da kika yi ɗazu sune suka zo, Allah shaidata, Haidar Shaidata, Matan gidan nan shaidata, a tou balle ace nayi ƙarya, ƙwamma na sanar miki gaskiyar komai kamin ki ƙullaceni a zuciya". Shiru nayi ina ci gaba da kukana, ƙasan zuciyata kuma ina tantamar anya Gwaggo bata fara daina ƙaunata ba. "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Shine abunda Baba ke nanatawa cike da al'ajabi da kuma tsoro. "Sabina garin ya haka ta faru, me yasa kikayi sakaki da azkar?". "Allah ni Baba bana da wata iska, kawai dai faɗar gwaggo ce kuma ka kira shi Yaya Haidar
🏠