NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 43 of 98

wani harhaɗe rai, ni duk haushi ma yake bani, saboda bana son mutum mai faɗin rai, ni yanzu ma bana ganin girmansa tun abin ɗazu daya mani, a hakansa kamar salihin bawa nan kuwa iskanci ne fal a cikinsa. Naji Gwaggo tace da shi, "Haidar ina fa daɗa godiya a gare ka kaji". "ba komai, ki godewa Allah kawai".Ya faɗa a taƙaice, still kansa na kan wayarsa. tace,"uhm ai dama godiyar Allah ta zama dole bare ka gayamin magana. Kaine dai da nake mamaki ya kamata na maka godiya, saboda yau ka shayar dani ruwan mamaki, yanda naji kana rera ƙira'ar nan kamar Sudais". Sannan ta juyo kaina tace, "Sabina ki masa godiya kinji ko". Sai yanzu na ɗago kaina dake kan waya, ina faman murguɗe-murguɗe da harare-hare na ɗaga idona na kalle shi, karaf muka haɗa ido, sai dana tsuke fuska na taƙarƙare na murguɗa masa baki, hakan yasa shi sakin ƙwafa mai ƙarfi yana jijjiga kai. Gwaggo ta sake cewa da ni, "ke wai yanzu ba'a isa ace kiyi abu a lokacin ba kiyi ne?". yace da ita, "ba ki kalla murguɗan baki ta ke yi ba saboda bata da kunya, to wallahi ni tashi zanyi na fasawa yarinya baki babu ruwana". yay magana yana kallon Gwaggo kamin ya maida kallonsa kaina yana min kallon za ki sani. "kaga ni kuma sharri ne bana so. Yarinyar na gabana kace ta maka rashin kunya, ta ina to ni ban gani ba. Kai dai ka dinga jin tsoron Allah, Mutuwa ake yi. da ace kana da zuciya ma fa ba zaka dawo part ɗin nan ba". Murmushi kawai yay baice mata komai ba, ta ƙara cewa nayi masa godiya, godiyar da ni ban san akan mene ba, ina ɓata rai nace masa, "na gode". Yay min shiru kamar bada shi nai magana ba, na tashi ina bige-bigen ƙafa zan wuce yasa ƙafarsa ya taɗe ni na faɗa jikinsa, ina faɗowa ya aje wayarsa gefe yasa hannunsa ɗaya ya matsoni jikinsa, ɗayan kuma da mugunta ya matse min baki har na gagara yin ihu, sannan ya kai bakinsa nawa ya kamo leɓena na ƙasa da haƙorinsa ya gartsamin cizo mai shiga jiki. Ganin wannan abu ya sanya Gwaggo tashi da sauri ta iyo kanmu tana tafa hannu tana zabga salati. "ni Hannatu yau naga abinda yafi zare tsayi, ,yo dole yarinya mana tace ka tsotse mata baki, tana faɗa ina basarwa ashe maganar gaskiya ta ke faɗa min, nake cewa tofin magani ne kake mata. ba zaka sakar mata baki ba sai ka cinye mata leɓe". Shi kansa maganar ta Gwaggo ta bashi dariya, ni kuma yana mamakin rashin hankalina da kuma rashin wayona, ashe da nace zan faɗa mata sai dana faɗa. "Allah Haidar ka bari na ƙaraso nan baka rabu da ita ba kai zan shaƙe na yiwa ruƙiya ba ita ba, idan aljanun iskancin ne kaima akanka sai naji, mara ɗa'ar yaro kawai". Dariyarsa ya gimtse yana tankaɗani daga jikinsa na miƙe ina hawaye, Gwaggo na ƙarasowa na faɗa jikinta na fashe da kuka. Ɗagoni tayi tana dubana, ta kalla Yaya Haidar ta zabga masa harara, ta ɓata rai sosai tana ce masa. "nan gidan dai baka ga an rubuta gidan kashe awu daga waje ba, saboda haka ka ajiye barbaɗin iskancin ka acan inda ka baro, tunda nake da Sabina wani ƙaton gardi bai taɓa riƙe mata hannu ba amma kai saboda tantirancinka ya kai intaha a gabana ka ke cafke mata baki saboda rashin kunya irin naka, kaga baki ɗan ƙarami da shi gwanin sha'awa, to billahillazi karka ƙara tunda dai ita ba muharramarka bace. a hakan ma kaje kai da Allah, zunubin daka kwasa ma ya isheka, kuma na dawo kan bakata kar ka sake zuwar min ɓangarena tunda bana ka bane, ruƙiyarka bana so tunda na lura irin ta ƴan iskan Malaman nan ce, Malaman gaibu, to zan nemo sabon Malami da kaina wanda zuciyarsa ta cika fal da tsoron Allah. Yanzu ka tashi ka fice min kamin na sassaɓa maka kamanni dan iya ƙololuwar ɓacin rai ka gama ɓatan rai, Ban san haka halinka yake ba, a gabana ka kama bakin yarinya da tsotso kamar ka biya sadaki, kai ai da sunan ƙanwarka, to da take ƙanwarka ai akwai aure a tsakaninku ko". yace, "idan ni kince na daina iskanci itama sai ki faɗa mata ta daina rashin kunya. Don gaba yarinya ta ƙara murguɗa min baki abinda yafi haka zanyi mata". Dogon tsaki Gwaggo taja, Haidar yana dariya yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yace, "Easy Hajiya Gwaggo". Wani dogon tsakin ta kuma ja tana zabga mishi harara a karo na ba adadi, cikin faɗa take ce masa, "kai da Easy ɗin na haɗaku na zazzabga muku mari, Wallahi ka fita a idona Haidar, akan Sabina zan saɓa maka yanda baka zato, sarai kasan halina idan raina ya kai ƙololuwar ɓaci, zan ɗauki komai amma bazan ɗau lalacewa ba, don haka kayi gaggawar miƙewa ka bar min parlo, kuma ko sahun inuwarka kar na sake gani a ɓangarena, abinci kaje can matan gidan nan su baka idan sunga dama, idan ba su so ba su barka da halin iskancinka ya ƙosar da kai, nk dai har ka bar gidan nan na gama saka kwano da kai". Yaya Abba na dariya ƙasa-ƙasa yace, "idan kuma ya dawo gidan gaba ɗaya fa?". Kansa ta juyo da faɗan da ta ke Yaya Haidar, tasa ƙafa tayi fatali da plate ɗin abincinsa, ta haɗa sunansu dana ubansu gaba ɗaya ta zage, da alama dai ran Gwaggo ya ɓaci matuƙa, dan faɗa takewa Haidar sosai, tana nuna masa kuskuren abinda yay
🏠