llah lafiyana ƙalau ki daina tada hankalinki kinji, kinga zuciyata zata shiga damuwa da wannan sabon yanayin naki...ko kuma wani abu ya faru ne?". na faɗa a sanda na taso daga mazaunina na dawo kusa da ita, na dafa hannayenta dake kan cinyarta, ina tsareta da idanuwa. sai tace da ni,"a'a ba abinda ya faru, kuma ai ko ƙalau kike abune mai kyau nayi miki adu'ar samun lafiya Sabina". Ta ansa min tana miƙewa daga kusa da ni ta isa friedge ta ɗauko wani jarka da ruwa a ciki, a cup ta tsiyaya min ruwan ta miƙo min tace,"ungo nan shanye". ni dai kallonta nake da sauyin da nake gani a tare da ita, na amsa na kafa kai zan kurɓe, ɗacin maganin yasa nai saurin ɗauke kofin zan miƙe naje na zubar dana bakina saboda ruwan ba daɗi wanda sai yanzu na fahimci na magani ne. murya a ɗage tace, "dawo ko na saɓa miki, ruwan magani ne maza haɗiye shi, idan ba so kike ranki ya ɓaci ba to karki dawo min da shi". Fuskar Gwaggo babu wasa ta ke min wannan maganar, gaddama na saka mata sai da naga da gaske ta ke kana na haɗiye don dole, kuka ne kawai ban sanya ba. Ina faman yatsine fuska ne nace, "to ni wai don Allah Gwaggo taya ma za ki haɗani da magani bayan lafiya lau nake, ai ba haka ake rayuwa ba, ni dai gaskiya karki kuma min haka domin wannan cuta da cutarwa ne". "ai ban san kina min faɗa ba sai kin rufe ni da duka Sabina". "ni fa ba faɗa nake miki ba Gwaggo, ina gaya miki gaskiyar abinda bana so ne". Na faɗa ina yin narai-narai da idanu. "hmm nayi miki uzuri ƙila har yanzu ba ke bace, da kika taho Haidar yana ɗakin nasa ne?". Baki na turo gaba bance mata komai ba, ta doka min tsawa, "ba tambayar ki nake bane ki ka wani turo min baki gaba kamar zumɓutu, za ki maida shi ko saina bige miki laɓɓa". "to ni ina zan sa ni ne?". "ke kr ki maida ni sha uku, ba daga ɗakinsa kike ba?". "ni mene zai kaini ɗakinsa to, ni tun ɗazu da muka dawo ban kuma ganinsa ba, ƙila yaji faɗanki yaji haushi ya tafi gidansu". Ƙaramar dariya kawai naga Gwaggo tayi ta miƙe tana magana ita ɗaya,
"wato da mai aljanu da mahaukaci dai basu da maraba, ni dama tunda naga kin shigo kin wuce fuuu kamar tashin iska nayi tunanin bake ɗaya bace, ile kuwa haka yake, to Allah ya sauƙa amma ni wannan abu naki da mamaki da kuma tsoro. Bari dai Haidar ɗin ya shigo naji sauran bayani daga bakinsa". "au wai Gwaggo kinma san ya sace ni ya kaini ɗakinsa kenan, bayan sarai kin san shi ɗin mugu ne. Kuma fa kene kike min faɗan ko ɗakin Yaya Abba baki yarda na dinga zuwa ba". "hmmm ba za ki gane bane, ni dai yau na gode masa saboda ya taimakemu. Ɗan ƙwal uba ashe yaron nan kwanyarsa cike ta ke da baiwar ilimi. Ai naga ranar Haidar yau, kuma na gode masa, dan da ace Abba ne kawai a gidan nan abin ba zai yi kyau ba tunda shi wannan bayan karatun sallah babu abinda ya iya sai buga ƙwallo". Ni dai taɓe baki nayi na gyara zamana ban ce mata komai ba. "aike Yau ki manta da duk wani rashin kyautawa da Haidar yay miki a rayuwa, ki gode masa saboda ya taimakeki". "a tsotse min bakin nawa da yay shine ya taimake ni?". A zabure naga ta yar da tsumman dake hannunta wanda ta ke goge ruwan daya zube. ta tsare ni da tambayan, "ban gama gane ya tsotse miki baki ba, bakinki dana sa ya haɗa yana tsotsa ko me?". "ehh mana, kawai ya kamani ya haɗani da bango yay ta totse min baki kamar ya sami alawa, ina ta ihu ina kiran sunanki ba ki kawo min ɗauki ba, har da cizar min leɓe yayi saboda mugunta gashi nan wurin har jini sai da yayi". Na faɗa ina kaurarra maganar yanda Gwaggo zata fusata. tsumman ta ɗauka taci gaba da goge ruwa tana cewa, "to ya zaiyi dole ce ta saka, sai yayi hakan za ki sami kanki". sai nace, "Gwaggo idan na fahimceki haɗa baki ku ka yi dai da shi kenan, shi yasa da nace zan faɗa miki ya ƙara totse min baki yace sai na faɗa miki da hujja...". sai tai saurin Katse min maganata da cewan, "keee ni fa ki daina ambatar min tsotsar bakin nan haka. Ki dinƙa cewa yayi miki tofi shine kawai, amma kya dinƙa cewa ya tsotse miki baki kamar wani ɗan iska". Ban ƙara ce mata komai ba na miƙe na bar wurin cikin fushi ina faɗin, "kuma sai dai idan Baba bai dawo ba, sai na zayyane masa komai. Ai Allah ya hana ko da riƙe hannun mace ne wanda ba muharraminta ba yayi, amma shi kaɗan ne ya rage bai min ciki ba". Ashe ta jiyo ni, tace, "kamin ki zayyane masa ni zayyane masa, ai dama dole muyi zama da shi akan wannan baƙon lamarin naki. Gaɓuwa kawai". Da daddare bayan mun kammala cin abinci, muka zauna kallo a parlo, Yaya Abba ne da Yaya Haidar suka shigo, kowanne kujera ya nema ya zauna, nayi mamakin ganinsa, amma sai na bar mamaki duk yanda akayi sun shirya da Gwaggo ne. Yaya Abba na zama yace da Gwaggo, "ina abincina?" tace, "acici mala'ikun tauna, kai daka shigo gida ina abincin ka an dafa ko ba'a dafa ba, to jeka kitchen ka ɗauka, Matarka dai ta shiga uku da ɗora sanwa dan ba zaka sassauta mata ba". Ya miƙe yana dariya ya wuce. Shi kuwa goga uban ƴan ji da kai tunda ya shigo ya zauna bai magana ba, sai faman latsa waya da yake yana