sanda da shi ba, to idan ba ki sani ba ki sani akan idona komai naki ya haɓɓaka Yarinya". Sai kuma yaja tsaki yana cewa, "mtswwww wani ne can dai zaiyi sha'awarki amma bani Aliyu Haidar ba, wata ƴar ƙanƙanuwa dake ma ni mai zanyi sha'awa to". Amma Yaya Haidar ɗan iska ne, wai a gaban idonsa komai nawa ya gama haɓɓaka, wayyo Allah nah anya kuwa bazan kurma ihu ba ko na sami sassauci, Wani sabon baƙin ciki ya kuma tsaya min a wuya, kai tasowar yarinta a gaban namijin da gida guda kuka tashi bai yi ba, ƙunƙuni na shiga yi wanda hakan yasa shi matse min fatar ciki a salo na mugunta. Ƙara na saki ina cire hannunsa daga wurin, ya bige hannun nawa yana faɗin. "maimata me kike cewa?". "ni fa ba abinda nace". "ƙarya kike yi, ki faɗa a fili mana idan kin cika mara kunya". "to ai kaine kana cewa babu abinda zaka yi da ni, kuma dai ni nasan ba haka bane sai dai idan baka da lafiya ne. Kana ganina ba ƙwaila ba, yanda nake ƴar duma-duma da ni ai duk wani mai cikakkiyar lafiya sai yayi sha'awata. Kaima dan na taso a gabanka ne shiyasa kake raina girmana". Na faɗa ina zumɓuro baki gaba, sai faman ƙifta idanu nake, kuma duk a tsora ce nake da shi, kallon yanda yake jan gemunsa nasan wani shirin salon muguntar yake haɗawa a ransa, domin wannan munafikin murmushin nasa ba na Allah bane. "ni dai ka matsa min na wuce tunda Allah ya kiyaye ni baka yi min komai ba. Amma fa kasani sai na kwashe komai na faɗawa Gwaggo". Na faɗa ina mai ƙoƙarin ɗauke hannunsa daya tokare ni a jikin bango. Ƙwafa naji yayi wadda tasa na ɗago ido ina kallonsa, ban ankare ba kawai naji saukar bakinsa cikin nawa yana kissing ena da salo na mugunta, ture shi nake ina dukansa a kafaɗa amma yaƙi sakina saima cizo daya bani a leɓe, kuka na fashe da shi ina buga masa Allah ya isa acikin zuciyata, Zare bakinsa yayi ya ɗago yana kallona fuska a ɗaure yana aika min harara. ni ko na kai masa duka nace, "Allah ya isa ban yafe ba". Na faɗa ina ture hannunsa zan wuce, Raina a matuƙar ɓace, tunda uwata ta tsuguna ta haifeni Gwaggo ta raineni babu wani namiji daya taɓa riƙen ko da hannu, sai Yayana kawai dana taɓa riƙe nasa, shima kuma wallahi bana sanin lokacin da nake riƙe masa hannu, amma yau wani ƙaton banza ya haɗa bakinsa da nawa, bayan naci burin mallakin zuciyata ne kaɗai yake da wannan damar. Allah ya isa dana ja ita ta bashi haushi, ya fizgoni ya haɗani da jikin bango, sai daya ɗalɗalle min baki kana ya kuma manna bakinsa da nawa, Yanzu kam harshena ya kamo yana dannewa da haƙorinsa yana cizawa, sosai nake jin zafi amma bai ƙyale ni ba sai daya tabbatar jikina yayi laushi kana ya rabu da ni. "kinga yanzu sai kiji daɗin yima Gwaggo bayani, mara kunyar banza kawai". Ya faɗa hakan yana nufar ƙofa yasa key ya buɗe, bai ko kalli inda nake ba yace da ni, "zo ki fice min a ɗaki, ko na ƙara maki wanda yafi wannan". Yo baima kuma wani yunƙurin magana ba nai wufff na fice da guduna har ina waiwayan bayana kar ya biyoni. "mugu azzalumi ɗan iska kawai, kuma na rantse sai na faɗawa Gwaggo". Shine abinda nake faɗa har na iso side ɗinmu, Haka kawai ban iya rashin kunya ba yau yasa na farata, ina zuwa bakin ƙofa na saita kaina sannan na buɗe ƙofa na shiga, a parlo na sami Gwaggo zaune tana sauraren karatun ƙur'ani suratul baƙara, ta taso da sauri tana min magana ni kam nayi mata shiru na wuce ɗakina. Ina shiga na faɗa toilet na ɗauka brush da macline na shiga goge bakina kamar zan ɗaye fatar jiki. Sai dana tabbatar na goge ƙazantar bakinsa kaf sannan nai wanka na fito, ina fitowa naji wani warin turare mara daɗi ya daki hancina nayi saurin toshe hancina da bakina da towel ɗin da nake goge ruwan kaina. _"to wannan hayaƙin fa na mene?"_
Na tambayi kaina, sai naji Gwaggo ta shigo tana faɗin, "Sabina kin fito?". Ni dai ban mata magana ba saboda duk warin turaren nan ya isheni, makunnan AC naje na ware haɗe da fanka, sannan na ɗauko air freshner na feshe ɗakin, sai dana juye kwalbar duka amma fitar warin nan ko gezau, naji ba zan iya ba na buɗe closet na ɗau hijab na fice da gudu a ɗakin ina tari, ina sauke numfashi kamar wadda taci gudu, ga amai dake taso min. "sannu". Gwaggo kawai ke jaramin duk bata cikin natsuwarta, sai firfita take min. "Gwaggo wannan wane irin turare ne aka saka min a ɗaki, nafa aljanu ne ma, kinji kuwa kamar kayan cikina zasu fito". Na faɗa ina jera tari, maƙogarona har yaji yake min. Tausayina ya cika Gwaggo, bata iya amsa min ba sai ji nayi ta kirani, "Sabina". Muryarta a hankali kuma cikin damuwa.
Na ansa mata ina ɗagowa na gyara ɗaurin towel ɗina, ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin, "to masha'Allahu, Allah ya ƙara miki lafiya ya yaye miki lalurar dake damunki". "amin". Na amsa saboda adu'a ce tayi min me kyau ba tare da sanin inda adu'ar tata ta dosa ba. sai dai dubanta nake da rashin fahimta, saboda yanda damuwa ta bayyana ƙururu a fuskarta, cikin wani yanayi na tashin hankali da ban taɓa gani a ƙwayar idonta ba. "Gwaggo menene? ko kina tunanin banda lafiya? A